← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 116

Sashe 88

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama fada ya fice a falon gaba daya, ita kuma ta ja ta tsaya tana kallon kofar da ya fita kirjinta na bugawa da wani haushinsa da take ji wanda ta tabata na abinda ya mata da safe ne ba komai ba

Yana fita Yumnah ta koma sama da sauri ta Kunno nata turaran itama ta sauko da shi, tana shirin ajiyewa ta dauke na Khausar din suka shigo Taufeek a gaba shi a baya bakin Husain da salama

Idannuwan TAUFEEK ne suka sauka a kan kasakan turaran wutar, a ransa ya ayana'To fah'

Su duka suka Amsa, Khausar ta yi kamar bata ga abinda Yumnah ta yi ba ta maida dubanta kan Husaini tan murmushi ta ce" Yau dai ga Besty, yaushe a gari?"

Yumnah kuwa sai ta wuce dan kawo masa ruwa a lokacin da Husain ke fadin" Aa a yi haka? Hajia bestyn besty ai ba zaki gane Ni ba jiya kai a lulube ana kukan ba za'a zo gidanmu ba bayan mu din nan mun riga mun rike kuma sai hakuri"

Da dan mamaki ta dago dan kallonsa jin bayaninsa sai ta ga TAUFEEK na kallonta, shi kuma sam bai wani tsareta da kallo ba magana dai yake yi normal , danma sun saba ne a da ya zamto a yau ya dan tsokaneta, basu taba irin haka da Yumnah ba

Kasa cewa komai ta yi ta sada kai cike da jin nauyi

Yumnah ta ajiye masa jus ta koma saman kujerar dake dan kusa da TAUFEEK ta zauna hankalinta a kan mijinta tana jin Husaini na mata godiya, ama kuma bai bude ba ya dai dauka ya rike a hannunsa , ita kuma a ranta tana ayana' Ni da ke a ga wanda zai fi samun shiga a fadar TAUFEEK!'

(Shi fa wani son, Allah ne ke halitarsa a ran bawa, ba dan an cika kyau ko isa ko matsayi ba, a'a, wani son kai dan adam sai ka ga mema aka gani na so din ne? To halitta ce da Allah ke halitarwa ya kuma hada da wanda ya ga ya dace, Allah ka sa mu so domin ka, mu kuma ki domin ka)
[7/24, 10:04 AM] +234 816 049 3429: 💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 5️⃣4️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

A sanyaye Mama ta ce" Ka san yanzun ko babu abinda ya daga mata hankali abin na tashi, dan dai bai kai na yau ba dan idan ya tashi da na bata maganinta ta samu barci yake wucewa shi yasa baka Sannin ya tashinma"

Hajia Nawarah dake zaune a ranta gani take yi harda rashin godiyar Allah a wajen mijin nata da matarsa da kuma dansa, , ita dai bata jima sosai tare da su ba ama ko ita ta san cewa zuwa yanzu ai shekarun Hajia sun kai wajen ciwace ciwace irin na girma masu zafin nan
da ace bata samun kulawama da tuni ta kwonce ai, dan dai ga kulawa, ko abincinta ba irin na kowa bane, jikanta ya dora doka ko tuwon laushi za'a tuka mata da irin abincin masu diabete ake yi mata, sigan bangarenta na masu diabete ne, kai komai da ka sani yana taka tsantsan da shi yana kuma hankalce da shi baya yarda ko da wasa ta yi wasa da lafiyarta, sannan a dole ta saba da sport rawata kaffafuwanta dan a lokacin da ya ga ya dace ya sakata tafiyar shine ke fitar da ita cikin anguwa da duku duku sunna tafe sunna fada har Mai kwanoni shima yake binsu dan wani lokaci har dariya suka bata ita kam a ranta ta ayana' Rai dai ana sonka sai an rabu da kai, du abinku Hajia ai yanzun tana hararan kabari, du kaunar ku da ita kuwa ba zaku hanna ba'

Hajia dake sauraron zancen itama ta budi baki a matsayinta Na matar gida dadadiyar da ta rigayi kowace ta ce" To Elhaji ciwon zamani sai an tankwaloshi, ana gudunsa yana bin mutun bale masu ciwon hawan jinnin nan an ce ba'a cika so sunna yawan fada ba, Allah dai ya ba Hajia lafiya baiwar Allah du ta yi wani iri"

Elhaji ya amsa da amen, ya maida dubansa kan TAUFEEK wanda bai furta masu koda A bane

Jim kadan nurse da ta je da kayan aune aunen jinnin Hajiar ta dawo da result
Bata tsaya ba ta shige ta kaiwa doctors da Khausar dake zaune daf da gadon Hajiar tana rike da hannunta daya tana tofa mata addu'a dayan kuwa yana ɗauke da karin ruwan da doctors ya jona mata

Sunna gama gannin komai Doctor ya umarce su kan sunna iya tafia
Ya zamto shine karshen fitowa sai Khausar dake bayansa rike da wasu takardun da ya bata da kansa haka kuma kaf likitocin sun yi mamakin gaannin Khausar din da Hajia dan babu wanda ya san matarsa take haka kuma basu san ko members din family din Professeur din bace

Su Baba ya fara tsayawa ya kwontawa da hankalin cewa ta samu barci da sauki kamar yadda likitoci ke sanarwa wa'inda ba likitoci ba
Sannan ya dawo wajen da TAUFEEK ke tsaye daf da Mama ya amshi result din Hajiar ya mika masa sai ya dora da fadin" BP dinta ya yi kasa sosai ne, haka kuma sigan jikinta ya yi kasa fiye da misalin mai cuta irin nata, ga kuma ciwon kan da zazabi, mun saka mata maganinta na da wanda ya shafi siga din, ama na hawan jinnin na saka mata sabon treatement dan wancen din inaga ya fara sakin jikinta ne , zazzabin kuwa na saka karin ruwa da allurar saukar da ciwon kai da kuma na zazzabin wace zamu ringa saka mata du tsakanin awa shida, sai dan tari wanda in sha Allah shima zamu saka nasa maganin idan wannan ya daidaita, yanzu zamu ajiye nurse din da zata zauna kusa da ita dole wace zata ringa kula da hawan jinnin nata kowani lokaci har mu ga yannayin saukarsa, in sha Allah zata samu lafiya Sir "

Taufeek ya hadiyi dan yawun dake tsakanin harshensa da makogwaronsa , a hankali ya ce" Zan zauna da ita Doctor"

Doctor ya dan dube shi, dama ya san yakan iya cewa shi zai zauna da ita ama kuma nurse din da za'a saka ta zauna kusa da Itan anya zata iya aaikinta yada ya dace kuwa? Dan idan yana waje sukan rikice ne wani lokacin idan ana gudun kar a yi laifin nan ake aikata laifin ba'a sani ba, dan haka sai ya ce" I'm sorry prof da ka yi zamanka a office idan ya so sai komai ya ringa samunka a cen ko kuma ka ringa saukowa kana komawa dan likitar ta samu filin yin aikinta a nutse"

Khausar dake tsaye dan nesa da su rike da takardun ta budi baki a sanyaye duda ta san ba itace da ɗaukan wannan decision din ba , ama sai ta kasa hanna kanta fadin" Doctor, Please zan zauna matsayin nurse din tare da prof in sha Allah "

Doctor ya dan kalleta da mamakin yadda ta iya fadin haka a gaban TAUFEEK kanta tsaye

Tashi daya ya nuna ba zata yi ba dan ba ita ta saba kulawa da ita ba

Shi da kansa likitan ya fadi haka ne dan baya so ta jawa kanta fada, dan likitocin ba sunne suke da ikon yin hakan ba, uwa uba Khausar ba likitar jinya bace takardarta ya wuce nan

A hankali Taufeek ya dakata daga nufin nufar wajen Baba ya juyo a dakensa ya ce" zata iya zaman , *SHE IS MY WIFE*" Daga nan ya karasa yana fadawa Baba cewar su je gida kawai shi yana nan , kuma sun san harkar asibitinsa ba'a zama a yi jinya, shi dai zai zauna Khausar kuwa zata yi jinyar, dan ya hada kan matansa su juya baya son rigima da hayaniya a kai
Chapter 88 · 0% Book details