← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 116

Sashe 66

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KHausar a hankali ta ce" HAJIA, Kennan shima bai san da wannan abin ba?"

HAJIA cikin hikima Tata ta amsata da" Eh, bai sani ba, hasalima iyayenku suka tsayar da hakan bisa rokon mahaifinsa "

KHausar cike da mamaki da wani firgicin ta ce" HAJIA aba na cen gidan ne ya nemi auren?"

HAJIA ya ce" Eh, shi da kansa mai kwanoni ba"

KHausar ta shiga gyada kai cike da kalar tausayi ta ce" Na san bai san inada saurayi ba, Ama HAJIA shima TAUFEEK din ai an cuta masa, auren dole ai akai masa shi dinma ko?"

HAJIA ta gyada kai ta ce" Wannan haka yake, Ni Bama abinda zai batan rai a zo ana fadin kuma daga aurenki an sake ki y'ar nan, ke dai yanzu ki share hawayen ki ki tausayawa kanki, komai dan a bi a hankali ne, duniyar nan akoy mai gudun bacin ranki irin Magidanci? Idan kuka zauna sai ku yanke abinda ya dace da ku ko?"

KHausar ta ringa jan hanci tana sauraron yar hayaniya bayan fitar Hajiya

Gaba daya abin yana nema ya girmami tunaninta
Ta rasa a inda zata ajiye wannan sabon abin

Abu daya ta sani shine ita da TAUFEEK *HARAMUN DIN JUNNA NE*!, idan ta tuna menene aure da tsarabe tsarabensa sai ta ji hankalinta na neman sake tashi , da sauri ta ringa kade tunanin tana jin tamkar wace ta tafka sabo tuna abinma a ranta, 'Hum, Allah ya kiyashemu abin kunyar nan ba da mu ba, bawan Allah in ya ji wannan aiki ta yiwu saima ya yi kukan takaici!' ta ayyana a zuciyyarta ta kuma dauri zaman daki ba tare da ta fito ko ta kimtsa gashin kanta ba, ita bata ga lokacin ba wani abu wai shi gashi ba a yanzun kam, ana ta Kai wa yake ta kafa?

Murmushi kawai HAJIA ke yi a ranta tana Ayana ' Tirkashi, ai Inaga Bama sai na wani boye masa ba, tunda har Allah ya yi yarinyarma ba zata amshi abin da dadin rai ba koda ta amsa din, ama ba Ni zan sanar maka ba zan bar mahaifinka ya sanar maka, abinda na sani daya ne tak a yanzu ka yi aure, a yanzu ka auri yar mutuncin da ta san darajar iyayenka, babu ruwana da kyan banza da farin fatar banza da iyayi na gayu, abinda na sani shine wannan yarinya itace daidai da kai, kuma bi izinillah itace haske a cikin hasken gidan Mai kwanoni!'

A baban gida shagali ake yi wanda ya daure kan daidaiku daga cikin ahalin gidan, domin babu abinda ya fi basu mamaki da daure masu kai irin yadda suka ga Mama na shige da fice cikin fara'a da farin cikin da suka gaza hade mahadar abin, to su basu ga hadi ba, inma zaman bikin karar kawar danta ta yi niyar yi ta je gidan su yarinyar su yi zaman mana? Ta yi zamanta a nan harda girki da samun baki? Lalle, wani shagalin sai a gidan mai kwanoni! Gefe guda kuwa ga Hajia tana nata itama shagalin, dan kuwa ita din tuya ake ta yi ta masa ana fitarwa sadaka sosai , dan hakan ta shirya wunin yau din dama, sai da yama ta yi sosai ta kimtsa ta nufi bangaren TAUFEEK, domin ta tambayi yan matasan dake zuwa wajensa inda yake sun tabbatar mata yau din bai fito ba, sai kuma ta karra tabatarta a wajen mai gadi dan haka ta mike ta nufi bangaren nasa hankali kwonce

Kamar yadda ta saba bayan sun gaisa da Yumnah ta sanar mata ta sanar masa itace, ama bayan zamanta a kalla ta dauki minti ya fi Ashirin bai sauko ba, hakan ya sa ta rasa shin hawa zata yi ko dai zaman zata ci gaba da yi ko Allah zai sa ya sauko? Gashi Yumnahma tunda ta hau bata dawo ba shiru kake ji

Har HAJIA zata yi tafiyarta gannin shirun ya yi yawa ta tuna waye jikanta, idanma dodo yake a wani wajen banda a gareta da ahalinsa baki daya, ta tabbata in dai ya san da zuwanta ba zai dauki lokaci kalau haka bai sauko ba, dan haka ta juya jiki ba karfi ta shiga hawa tana salama dan gudun shiga hakin kowa

A kofar dakin ta dakata ta yi bugu ya fi a irga tana Salama, ama yarinyar nan da dakinta ke daf da nasa bata fito ta nuna mata ta san da mutun a wajen ba, ita kuma ta ki ta hakura dan jikinta ke bata ba lafiya ba

A bangaren Yumnah kuwa tana sauraron HAJIA, hasalima a tsaye take jikin kofarta tana murguda baki kasa kasa ta ce" Yau na ga jarabar naci, ba zan kira maki shi din ba, Ni kam Inaga bayan rabuwata da wancen a nacin saura wannan masifafiyar tsohuwar, a wuni sai ta mana shigowa uku in yana nan ta zo ta ishe shi da surutu ta tafi, ko mahaifiyarsa bata masa zuwan nan kamar yadda wannan mata ke yi, ba abinda ke bani haushi irin turare turaren shirmen da take masa, ko me take tunani?, Inma menene bata isa ta nunan son mijina ba ama sai tana abu kamar wace bata san me take yi ba, a barshi ya huta tunda bai fito ba ai damu ne baya so zan gani in har zaki shigo dakin kai tsaye ne, inama ace dakin na shige na same shi koda wani abin yake in dauki hankalinsa !"

HAJIA kam jin shirun ya yi yawa ta shiga tunanin ko sauka take yi ta koma bangarenta ta yi kiran mahaifinsa ya mata kiransa ta ji yana kalau? Idan har ta ji an gama wannan ne kaɗai damuwarta dan bata son abinda take ji a ran nan nata

Sai kuma ta shiga tunanin yaushe ta koma cen?, Kai ina , a dan daburce ta juyo ta kama kofar ta bude tana Salama da karfi hadi da Hanna idannuwanta dagawa koda taka tarda wani abin to fa ya zamto idannuwanta basu gani ba

Shirun ya yi yawa, a hankali ta shiga bin dakin da kallo

A gyare yake tsaf tsaf ga kanshin turare da sanyi mai karfin tsiya a ciki har idannuwanta suka sauka kansa wajen kujerar dakin ta gaf da gado kansa a saman kujerar yana zaune a kasa jikinsa ba riga dan ya samu ya cireta da ya raarafa ya yi sallar azahar daga ita bai samu yin ta la'asar ba domin yana kwatanta mikewa sai ya ji kamar za'a maka shi a kas ga wani ciwon kai mai tsanani da bugawar zuciyar da sam bai san zasu iya riskar shi a irin wannan lokacin ba

Gaban HAJIA sai da ya fadi, ta dakata tana kiran sunansa ama ya kasa amsa mata

Da sauri ta daga kaffarta ta karasa inda yake ta shiga tabashi da ambaton sunnansa

A hankali ya iya buda idannuwansa ya sauke kwayarsu a saman fuskarta a lokacin da ta duko tana taba wuyansa ta ce" Subahanallah, Magidanci baka da lafiya ne dama ban sani ba? Ama dazun fa da na Barka kalau na tafi"

Idannuwansa ya lumshe yana sauke numfashi a hankali yana lumshe sunansa kasa kasa , muryarsa cen ciki ya ce" HAJIA......, Kin dawo?"

HAJIA ta gyada kai ta ce" Bari in kira a kaika asibiti kai fa baka iya ciwo ba, na shiga uku ka ga yadda idnanuwanka suka kade kuwa? Jiki du ya dime da zafi jijiya ta yi rado rado, kai subahanallah wannan yarinya da kake aure Ni tana da hankali kuwa? AI sai ki fada bashi da lafiya ko?"

Da kyar ya iya karasa jin maganar da HAJIA ke yi, a hankali ya dan mirgina ya dora kansa saman kaffafuwanta dan hakan yake da bukata, shi dama mutun ne da bai iya ciwo ba sam, kuma idan yana ciwo ta yannayin shanyuwarsa ake ganewa ba zai zo da kansa yace ciwo yake ba har sai ciwon ya kayar da shi tamkar ba likita ba, HAJIA kam ji ta yi hankalinta ya kara tashi, domin ko yana ciwo bai cika yin laushi da ita haka ba, abinda tana ihun a kaishi asibiti yana fadan ba inda zai je? Ama yanzu jikinsa kamar ana rura wuta?

Hankali tashe take janyo abin gadon dan hango salularsa da ta yi karamar , dan kuwa tana iya kamo lambar mai kwanoni da tasa tsaf a kanta

Tana ta rubuta numbobin muryarsa cen ciki da kyar ya iya budar bakinsa a hankali ya ce" HAJIA, KHausar.....yanzu ta daina kukan ko? An mata auren ta huta ko?"

Da sauri HAJIA ta yi cakkkkk daga abinda take yi tana kallonsa

A raunane ta ce"

Kai dai gaskiya bana so ma nace an ji kunyatu sai an saka nace, fisabililahi kar dai kace ciwon Kauna kake? To wai kai dilla mike🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄

😨😨😨😨 Akoy fa rikici, watau ita Bama ta hango halal a ita da Magidanci ba, magidancinma nawa yake in ji matar jikan HAJIA!😨😨😨😨

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣1️⃣

*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*

1: Duk karyar kada

2: Yar mahaukaciya

3: Neman na kaina

4: Bani da zabi

5: Bak'a ce

6: Kutkale

7: Makauniya ce

8: Mage

9: Duk nisan jifa

10: Idan ka raina inda kake

11: Dutse

12: Alkalamin kadarata

13: Bani da zabi

14: Dakika Biyar

15:Wata kokowar

16: Aure yakin mata

17: Ni zan ladabi

18: Daga tafia daukar soja

*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Chapter 66 · 0% Book details