← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 116

Sashe 89

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Likitan kuwa sosai ya yi mamakin jin Khausar matar Doctor ce, sai dai bai tsaya ya wani nuna mamakin nasa a fili ba ya yi gaba yana fadin " Madame bismillah mu je na baki dukkan abubuwan da ake mata da takardar "

Khausar kam tunda ya fadi cewa ita matarsa ce sai ta ji dama ba a gaban Doctor din ba tace zata zauna, sai ta ji kunya da nauyin su Mama da suka ji maganar, ta bi likita shina cike da jin nauyisa ta je ta amso magungunan

Ko da ta dawo ba kowa ta shige dakin ta kai komai ta ajiye ta juyo inda yake zaune rike da hannun Hajia yana kallonta

A nutse ta dauko kujera ta ajiye daf da shi a hankali ta samu kanta da dora hannunta saman nasu a hankali ta dan matsa nasan kadan sannan ya dan bubuga a hankali ta ce" in sha Allah, zata samu sauki, ka kwontar da hankalinka Please"

TAUFEEK ya juyo yana kallon fuskarta, a hankali ya dago hannunta ya kai gefen fuskar tasa ya shafa gefen fuskar nasa da hannunta na dama yana kallonta kasa kasa ya ce" Allah ya sa "

Daga nan Khausar ta yi shiru suka ci gaba da kula da Hajia da dukkan motsinta

Sosai take barci mai daɗin gaske, sunna nan direba ya kawo suturar TAUFEEK wanda ya yi kira ya saka Yumnah ta dauko masa sannan ya fada mata ba sai ta zo ba dan ba barin jinya ake yi ba domin ta nuna tana son ta zo din itama ( wani lokacin, idan da rabo , mai hali irin na Yumnah na cenzawa idan ya samu abokin kwaikwayar halayar nasa mutun ne mai aikata aikinsa domin Allah ba dan a yabe shi ba ko dan ya saka dan uwan nasa jin haushi da kishinsa ba.)

Office dinsa ya je ya yi wanka ya cenza sannan ya shigo masu da abinci

Sallah kadai ke fidashi, Khausar kuwa tunda ta shige bata fito ba dan idan bayin ne akoy komai a ciki, kawai dai kayan jikinta take jin sun kai cenzawa dan kuwa ita rage acn nan ta yi sosai ta kuma kashe panka dan TAUFEEK har fifitu yake yi wai zafi ita kuma ta nuna tarin da Hajia ta fara in ta farka cikin sanyin nan da mura zata tashi,

A haka har aka fito daga sallar isha i, zuwa lokacin sosai jinnin Hajiya ya daidaita sai dai kasancewar bata farka daga barcin da take sha ba ba za'a iya tantance irin aikin da magungunan suka yi mata ba, ama ko a yannayin saukar numfashinta da sauki sosai

A hankali ya mike daga daf da Hajiar ya zubawa bayi ido

Kasa hanna kansa shiga ya yi a hankali ya bude ya shiga yana wani irin fatan da bai dace ya yishi ba a zuciyarsa a matsayinsa na abokin Khausarar Aba

Allah ya taimaketa tana tsaye tana alwallah ne, sai dai duda haka ta wanke pant dinta kennan ta shanya bayan ta yi wanka sama sama sannan ta yi bruch ta maida rigar da take yin datinta yanzun sosai a ranta guda ba wani dati da ta yi ta shiga yin alwallah hankali kwonce dan tunda take nan ta ga babu wanda ya shigo bale a ga paant dinta

Da sauri ta kai dubanta inda ya zubawa ido, a rikice ta kwalalo ido ta budi baki zata yi magana ya tako da saurin da bata yi zato ba ya janyota jikinsa lokaci daya ya dago kanta ya hade bakinsa da nata ya shiga kising cikin saurin da ya saka ta jan numfashinsa ta hadiye a huhunta sannan ya sake juyawa da ita ya hadeta jikin bangon nan a hankali hannunsa na damkar cinyarta ya ki bata damar kwace bakinta sai da ya gaji dan kansa sannan ya saketa yana fitar da numfashi da sauri da sauri ya janyota jikinsa ya sake rungumeta tsam har sai da ta kwontar da kanta dan dole a kirjin nasa tana sauke numfashi

A hankali ya dan yi kasa da bakinsa daf da kunnenta
Cikin kwarewa a aikinsa ya ringa sinsinar kunnen nata yana dan sauke hucin numfashinsa a nan, kasa kasa sosai ya ce" Ba'a magana a bayi, kin ga kin saka na maki abin nan da bakya so ko?"

Khausar ta dago da sauri ta zubawa fuskarsa ido, a rashin shiri ta ce" Kai TAUFEEK walahi da gangan ne ba gashi ba ka yi maganar ba?"

TAUFEEK ya dan zarro idannuwansa da hannunsa ya mata alamun ta yi shiru mana kafin ya nuna mata pampon wai ta yi abinda ya dameta tana yi

Ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta bude ruwan ta daura alwallar tana kiyayewa kallonsa dan gudun kunyar dake nukurkusarta ta kayar da ita har ta gama cikin dabara ta janye pant dinta ta dauki hijab dinta ta nade shi a ciki da nufin in ta faki idonsa zata maido ta shanya ta yi gaba sai turo baki take yi ta bude bayin ta fito shi kuma yana baya yana kwasar ganima wa idannuwansa yana kashe kwarlwatar idonsa

Idannuwanta ta mutsitsika tana sake dubansa daga zaunen da ta kama ta zaunar da kanta da kanta ta sake rage girman idannuwanta tana dake tabatarwa kanta abinda take gani ta dauke kai ta ce" Uhum ikon Allah, dubun munafukai dai ta cika, dama karya fure take bata ya'ya, to Ni du wanda ya kuma min iskancin kukan baya son auren nan sai dai mu daku da ubansa koma waye, aikin banza a asibitin zaku shige bayi to uban mema kuka yi?"

Sai da cikin Khausar ya motsa, a rikice ta kalli magidanci wanda farin cikin gannin Hajiar zaune ya kasa barin fuskarsa da sauri ya zagayo Khausar ya karasa yana fadin" Yaushe kika tashi tawan?"

Hajia ta sakar masa harara tana leken Khausar ta ce" dole ai ka tambaya tunda kun sumar da Ni kun shige kun aikata aikin da ba shikenan ba, Allah dai ya sa ba a bayi zaka min jika ba kai marar hakurin tsiya, dilla dubaka kamar ba kaine ke min rashin daga a kan auren nan ba, to da mai kwanoni kake, sai ku kuncen abin nan mu je gida ka samu filin baje kolinka a mutunce kar ka haifon dan bayi ya ringa kantara min mari, ke kuwa kya karaso ko sai na taso na tardo ki, ashe haka halinki Khausara? Baki kamar agwaluma kina ihun bakya son auren magidanci shine zaku munafunceni a bayi bayan kun sumar da Ni?"

A rikice Khausar ta rarumi hijabinta gaba daya ta manta da pant din ta zurma hijab din ta karaso tana yadda hannayenta ta ce" Hajia, walahi walahi ba abinda kike zato bane, hasalima babu abinda ya hadani da shi gayanan ki tambayeshi Hajia"

TAUFEEK ya tabe baki yana mikewa ya ce" ai kuma sai ku yi" hankali kwonce ya karasa ya dauki pant din ya shiga ya shanya ya dawo ya zauna yana kada kafa Hajia na mitar su je gida ya dubeta ya ce" Ke kam wai wace irin mutum ce, kin farka zaki dagan hankali kuma ko? Babu inda zamu je sai kin warke sumul , kuma maganar tafia babu ita, dan babu inda zamu je kina rashin lafiya "

Hajia ta yi tsuru tsuru tana kallonsa, sai kuma ta kalli Khausar ta ce" Khausara kin gama sallar ne?"

Khausar ta juyo tana gyada kai
Hajia ta ce" Je aro mana waya ki amshi numbar mai kwanoni a wajen wancen mu buga masa waya kin ji? Ba da Ni ba wannan rashin kunyar tana tafe kana lekenta kuma bayan wannan Madina ai Garin Manzo in Allah ya taimakeni kasata a cen shikenan sai ka ki kaini dan son kai? Ni sai mun je bana "

A hankali suka zuba mata shi da Khausar din

A sanyaye ya tashi ya karasa bakin gadon ya zauna daf da ita ya kamo hannayenta yana dubanta ya ce" Dan kina son tafia gida ne zaki daga min hankali ko?"

Hajia ta sauke ajiyar zuciya, sosai jikan nata ke bata tausayi idan ta masa maganar mutuwarta ko me suke yi sai ya sakar, nan da nan ka ga ya zama wani iri, tamkar yaro karami ko kuma tamkar ba likita ba
Cike da rashin kwarin gwuiwa ta ce" Ni mu koma gida"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ok ina zuwa"
Daga haka ya fice dan daidaita tafiyar tasu dan ba zai iya yana kallonta a haka ba, tunda gidan take so za'a tafin mata da komai da komanta a ringa mata treatement din a gida
Chapter 89 · 0% Book details