Sashe 69
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aba ya gyada kansa ya ce" to Ni a bayanin nan ban ga wanda ya zama rikaken hujar da zan yi duba da ita har in fuskanci kin yiwuwar auren nan ba yar gidan Aba, inace na hore ku da jin tsoron Allah kadai da kuma kiyaye hakokin musulunci, yaushe kika fara damuwa da zagin yan anguwa? Ai da kin jima a kasan kasa Khausar dan kuwa ai an jima ana zagin namu ko?, Ko dan karatun nan naki ai babu abinda bamu gani ba, Ni na fi so in akoy wani dalilinki ki sanar min sai mu duba ko yar gidan Aba? Kuma shi aure ai zuwa ake yi da zuciya daya a zauna , idan har zaman bai yiwu bane ake yin hakuri ko? Sannan maganar aikinki Elhaji ne da kansa ya ce min a jibin nan zaki koma bakin aikin ki, a gobe za'a kawo lefenki da kuma direbanki dan yace a yi hakuri da maganar shiga adaidaitar , tarewa kuma da an ce a yi da gagawa sai yace a bari har su Elhaji karamin su dawo daga haji sai ki tare, kin ga ai muna tare ko yar gidan Aba?"
Khausar ta ringa kallon mahaifinta, tana gannin wani annuri a tare da shi wanda du yadda yake son boyewa ya ki boyuwa, haka kuma bayanansa sun mata wani irin girma da neman shiga kwakwaluwarta, Bama irin maganar aure zaunawa ake yi idan ta yiwu ake yinsa, hakan na nufin idan ta dawo tace masa auren nan fa ba zata yiwu ba zai raba? Kai in kuwa haka ne tana iya yin shiru har su hadu da TAUFEEK su yi shawara, ta tabata shima zai ce ne eh wannan aure son iyayensu ne ba nasu ba,
Aba ya sake fuskantarta ya ce" Haka kuma, a kulun ina horarki ko me ya tunkaroki komin rikicewarsa da rikita zuciyarsa ki fadawa Allah, ki kai kukanki wajen ubangiji, ki bashi zabi kin ji yar gidan Aba, Ni kam sai in ce alkhairin ne fa, ki duba ki ga kulun adu'armu kennan fa, nan har cewa kika yi in kai ki masalaci in ba kowane nema ke dai a maki auren kema ko? Kuma yanzu Allah ya kawo sai ki ringa rigima? So kike yi hankalina ya tashi ne ?"
A hankali Khausar ta girgiza kanta tana jin wani irin tausayin mahaifin nata na ratsa mata zuciya
A sanyaye ta ce" Abana ka yi hakuri ka ji? In sha Allah zanma gani ne tunda kace auren ai in zai yiwu ake yi ko Aba?"
Mahaifinta ya amsata, yana sake gannin tamkar wata yar jaririyarsa ne Khausar din, sam baya gannin girmanta, idan ta yi wani abin kuwa gaba daya yake gannin rashin wayonta ƙarara, cikin hikima ya idasa kashe borin rigimar, bale da ta ji cewar zata je aikinta a jibi jibinnan sai ta ringa jin kamarma auren an riga an rabashi ne,
Da wannan ta fito daga dakin mahaifinta, sai tunane tunane take yi, to ita jama'a yanzun idan ta ga TAUFEEK ta ce masa me yace mata me? Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana
Ido hudu suka yi da Mama, Maman ta sakar mata harara da sauri ta sada kanta ta shige dakinta tana jan hanci ta cire zumbulelen hijab din da ta wuni da shi dan dole, ita daya sai tura baki take yi ta nemi waje ta zauna saman katifarta da yar karamar rigar dake jikinta ta barci ta shiga murza manyan cinyoyinta tana sauke ajiyar zuciya tana kallon wayarta zuciyarta cike da tunani kala kala, ita daya sai ta ja tsaki, ta yi kyaftu ta yi wannan ta yi wannan , tunani ya yi mata yawa
Mama kuwa dake tsakar gida bata koma daki wajen Aba ba, tana zaune ne da autanta suka gama waya da Rukaya wace ke shaida mata cewar gobe da safe mai kitso da kunshi zasu zo a yiwa auntyn tasu dan Allah maman ta tirsasata ta zauna a yi mata tunda an ce jibi zata koma aiki sunna so ta koma a matsayin amaryar , Allah ya taimake su yanzun auntyn tasu ita da kanta tana dan gyara fuskarta in zata fita, dama fannin turare ba'a maganarsa da tsafta domin Khausar akoy tsafta
Washe gari
Kusan karfe bakwai na safe Hajia Fatahiya ta yi salama a bangaren TAUFEEK sannan ta dakata kamar yadda Mama, fa Hajia nawarah da shi kan Mai kwanonin ke tsaye sunna jira a basu damar shiga, sakamakon zuwan Hajia ta wanke su tassss ta dawo bangaren domin a nan ta kwana ita da Yumnah a falon tana yi tana leka shi har asubahi ta yi itace ta koma ta aniya taimaka masa har ya mike bayan yana iyawa tace zata raka shi har bayin sai da ya kiya ne ta samu ta fice ta je bangaren Aban ta masa tasss sannan ta bi daki daki ta masu tasss ta koma harda hawayenta wai magidanci ba lafiya bata ga kafar kowa ba
Yumnah ta ja numfashi, ranta cike da jin haushin Hajiar nan, ta sakata ta soya wainar kwai ta zauna tana bashi a cokali kamar ita ta haifeshi, shi kuwa sai wani lumshe ido yake yi jikinsa har yanzu da zafi ama ya ki zuwa asibitin kuma ya ki korar wannan masifafiyar tsohuwar ta saka mata falo banda kaurin jiji babu abinda yake yi wai ita bata iya zama sai da turaran wuta, du tarin turaran wutarsu ta je ta kwaso jijinta ta ringa maka masu a falo kamar gidanta
Mikewa ta yi ta je ta bude dan yadda aka dannan karaurawa aka kuma yi salama ta tabata masu son shigowar manya ne, dan bata taɓa gannin kaffafuwan yaren gidan a bangarensu ba
Budewa ta yi, sai kuma da sauri ta bada hanya tana amsa salamar
Su Hajia ne suka fara shiga, sannan Mama sai kuma Baban shima ya shigo da suturarsa mai kamala hannunsa da carbi da hularsa a kansa domin shi ma'abocin fita da hula ne ko a cikin gidansa
Mama ce ta fara karasawa daf da Hajia ta duka har kasa tana gaisheta, kishiyoyinta suka mara nata baya , sai uwa Uba Aba ya karaso shima da kuzarinsa ya duka har kasa yana cire hular kansa ya ce" Barka da safia HAJIA, fatan an tashi lafia?"
Hajia ta yamutsa fuska tana kallon TAUFEEK dake kokarin tashi daga kujerar da ta saka shi a gaba ya duka shima kansa a kasa yana gaisar da iyayen nasa , ama babu wanda ya amsa tunda amsar ta Hajia suke jira kafin su iya amsawa, sai ya zamto Yumnah itama a dole ta duka din gannin harda baban a duke gaban wannan mai fuska a haden
Hajia ta sake hade fuska ta ce" Kwana ku kuka ganshi Ni ban ganshi ba, dan kuwa kwana na yi ina fama da jikana, ba lafia numfashinsa da kyar yake fita , hannuna a saman daidai zuciyar magidanci haka kirjinsa ke bugawa , Yaren nan sam bakwa jin tsoron Allah, ban san me yaron nan ya tsare maku ba fa kuka tsane shi, a zo a kama min a kai min shi asibiti kuka kiya kuka je kuka kwonta, wai harda ke da kai, in su Wadinnan basu san zafinsa ba ai bai dace ace harda ku ba, daga yau na san zaman da zan yi da kowa a gidan nan, kuma babu wanda zai yi ciwo mu damu Ni da Magidanci, gaisuwa ku rike abinku bana so, wulakancin banza da wofi!"
Taufeek ya zuba mata ido kasa kasa ya sakar mata harare, ita kuma ta tsuke baki ta ce" Ka harari wannan, kai yanzu du abinda suka maka dan rashin zuciya sai ka ji ciwo in na masu fada ko?"
Aba ya yi murmushi kansa a kasa ya ce" a yi hakuri Hajia mun yi laifi, a yi hakuri ba zamu sake ba in sha Allah, ai jiyan kin ga baki ne basu tafi ba sai dare, masha ALLAH daurin auren kamar da wasa ya tara jama'a kuma aka zauna sosai sai da muka ci abinci aka yi zumunci sannan aka watse"
Hajia ta yi dan shiru sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ni walahi du sai da abin ya min lami, ita KHausarar fa har kamar zata summa wai bata so, bata son magidanci fa, kuma na taho nan dan in ganshi na tardashi ba lafiya abin sai ya rikitani, auren nan du sai ya shige min, to yaya ka barota ita KHausarar ?"
TAUFEEK da kansa ke kasa , a kasan dai yake, sai dai a bayanin kakarsa ya dan so shiga hali na rudu kadan, Magidanci dai du duniyar nan daga bakin Hajia shi ake nufi, to meye hadin maganar bata sonsa Khausar kuma?
Aba cikin murmushin ya ce" Ai haka dai aka bata hakuri, sosai ta nuna bata so din, ama an rarasheta tunda an riga an daura ai hakuri za'a yi, kuma tsakaninta da Elhaji karamin ai sun fi kusa , zasu daidaita kansu ne bi izinillah "
Yanzun kam dago kai ya yi ya zubawa mahaifinsa ido, hakama du wani wanda ke wajen ama banda Mama wace ke murmushi itama ta diramar mijin nata da sarakuwarta
Hajia ta yi murmushi gannin yannayin TAUFEEK, ta mike tana fadin" Ku karaso mu zauna a yi maganar abinda ya faru jiya, ke yaminah je sako hijab mana in Ni kin rainani kina yawo da rigar nan da hula a gabana Wadinnan din ai sirikanki ne harda uban mijinki ai da kunya ko?"
Yumnah ta zubawa Hajia ido, idan har zata iya zuwa dakinta a irin wannan lokacin ai tana iya zuwa ko'ina ma
Bata tunanin ko zata iya zuwa wani daki sako hijab maganar da baba ke yi ke neman sakata juwa, dan haka ba tare da ta je din ba ta karasa kusa da TAUFEEK ta zauna a saman kafet din kamar yadda ya yi sannan ta zubawa Baba ido wanda ke saman kujera , hakama su Hajia Dukansu a saman kujerar suke