← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 116

Sashe 13

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Sosai Baba ya rasa bakin magana, sai dadagawa yake yi ,
Shi dai namiji ne bai san tsadar kayan mata a ido ba, in ba zuwa siya ya yi ba yakan hanki masu irin nauyi a idon nan haka a cen bangaren manyan kaya, bangaren abinda ya haura dari du kwaya daya, a yanzu haka wannan na hannunsa ya tabata kudi ne na mamaki, hakan ya sa ya dubi iyalinsa ya ce" Mamansu, kayan nan basu yi yawa ba kuwa?, Kayan nan da gani zasu yi tsada"

Murmushi ta yi tana dan sake ziga masa kunnun dake hannunta ta ce" Ai kama Abansu kayan nan zasu yi tsada sosaima, kuma ka ga na wajen mutuniyarka? Har cewa ta yi yau ko dan goron baka aika mata ba, dama jira nake yi idan ka zo ka gani abinda kace sai a yi in sha Allah " (not, kar ki ringa nunawa namiji a cikin gidansa a irin girma da daraja da Allah ya masa cewa bai isa da wasu manyan decision na cikin gidansa ba kece kika isa..., Tsakaninmu mu mun sam cewa muna da baban iko da rayuwarsu fiye da tunanin bawa, domin muna da damar tankwasa su a lokacin da su da kansu basu gane ba....., Yarda da hikima irin tamu ta siya mana haka ba nuna isa da takama ba, to wai wace isarma Allah na tuba ke da akace ki zo ki yi biyaya dan neman aljannarki? Ba gazawa bane dan kin bashi damarsa a matsayinsa na mai nemo gero da hatsi yana daukan decision din abinda ya shafe ku a cikin gidansa.......hakan ba yana nufin ki kasa juya abinki cikin hikima ba, cikin hikimar kina iya samun abinda kike so shima yake so ba tare da daya ya ga an tauye daya ba......, Allah ya karra hada kawunnanmu da Mai hause🥹😍)

Murmushi Aba ya yi yana girgiza kai ya ce" Hajia hajiar shagali, ai zan je da kaina na kai mata goronta , ama kuma ba za'a mayar da kayan nan ba, a tsakaninmu da mutanen nan inaga idan muka yi haka bamu kyauta ba, sai dai kin ga kudin shadar da na ba Elhaji? Zan koma na ce zasu je su zabo maku takalma da kudin, idan ya so kudaden takalman da wasu tanadin sai na karra mu fara shirin gudunmuwa, har sai na shiga tunanin nawa zan tanada ta gudunmuwa ?"

Mama ta miko masa kunnun da dan dumi ama kuma ba sosai ba tana murmushi ta ce" Abinda Allah ya hore maka, yadda ba zaka takura ba ba kuma zaka yi kauro ba, kai da kake da bikin a gabanka kaima?"

Ai kam ta saka shi dariyar, domin katon asusu ne ya bude yake jefa tanadi kulun ta Allah, da safe da kuma yama , tanadin da suke sakawa a tare domin itama in cenjin kayan miya aka yi sai ta kai ta zuba, a zaunen da take yan saide saidenta su lalle da salatif da dai dan abinda ba za'a rasa ba ta kayade riba na hawa tana zubawa, danma ya ki sana'ar a fita ne ai da samun ya fi haka.....haka dai suka cika darensu kafin suke kwonci dan murnar yau ta hanna masu kwonci da wuri

Kwana biyu tsakani Khausar ta shiga rabon anko ita da yan uwanta

Kusan abinda ke ba Kausar mamaki har ya bata dariya shine du wace ta kaima sai ta jefo mata tambaya fuska cike da mamakin wai dan Allah dama irin yadda zumuncinta yake da TAUFEEK ba saurayinta bane?, Har sai da ta gaji da bada amsar a tsare sai kawai ta katse amsar ta badata a hade dan maganar ta wuce, takan yi dariyar wannan kwabin da wani tunanin wasu mutanen, kai du wanda yake irin wannan tunanim ta yi waje ta ajiye shi a matsayin mutun mafi rashin fahimtar rayuwa gaskiya
In ba rashin fahimta ba ina mahadi? Ina hadi? , Eh lalle TAUFEEK ba wai ta girmeshi bane, haka kuma a yannayin jikinsa TAUFEEK ya fita tsayi kuma jikinsa kakauran jiki ne ba lange lange ba, ama sam bata gannin wata mahada ko kamanin dale iya sakawa mutane wannan banzan tunanin, ba wai da tana y'ar talakawa ba yana ɗan masu kudi ba, ko daya, ita bata taba raina asalinta da samun mahainfinta ba, kuma ta san masu kudin na auren talakawan su kilace cikin hukuncin mai sama, abinda ta gama sani ne ko giya take sha TAUFEEK ba abokin soyayarta bane, ba kuma abokin kalamai ire iren wadinnan bane, kai mtssss haka kawai ana nema a hade mata tunani? Tana zamanta ana hade mata lisafi? A gaskiya abin sai ya fara bata haushi da tarin dumbin uban mamaki..... karshe ta kawo na mujiya ta zubawa du mai mata kallon, in har a ganta da ankonsa ba zai cire tambayar nan ba a ran mutun to dan Allah ya rike tambayarsa a ransa abinsa

Yawan zuwa shagon Elhaji amsar atampopin masu hada mata kudadensu wata halaka ta kulu a tsakaninta da baban yaron Elhajin watau Mujaheed

Alaka ce irin ta shanshakai ta siyaya da farko farko, a hankali ta ringa karantar wasu sababin hulda a tare da shi da suka so bata tsoro, domin sai take tunanin cewa ta zo ne zata yi lokaci kalilan a shagonsu zai kula alakar dan ya tozartata ko dan ya mayar da ita costoma a wajensu ta yadda ko zuwa gaba bata da wajen cire anko sai shagonsu

A hankali kiran dake shiga tsakaninsu ya dan fara yawa, ya zamto ya fara sakata boyewa idan har zata amsa kira a cikin gidansu domin kamar jira ake yi yar rakani masai dinta ta kwashi tsuwa du sai a ratabo mata ido ba ga Maman ba , ba ga ya'yan maman ba, uwa uba ana daf da shan ruwan kwana na goma sha takwas da azumi a ranar Aba ya dawo da wuri wayar nan ta dauki tsuwar da ta saka yayan hanjinta yamutsewa dama ga abin yinwa na sakata juwa domin a irin lokacin nan du wani kayan buda baki a gabanta suke jira kawai take yi a yi gyaram murya a masalaci ko na tsokana ne ta daga ta maka sai kawai kiran nan ya shigo ya zamana Aba dake zaune saman darduma yana jan carbi sunna dan taba hira da Mama dake zaune daga kusan dakinta Auta a saman kan cinyarta ya yi matashi yau azumi yake kamar an summar da shi , su Aisha kuwa sunna gama wanke wanke dan su kam da sauki sosai sunna da juriyar azumi sosai da sosai kowa ya juyo inda wayar ke ajiye tana kuka irin na kashe kunnan nan tamkar mai son saka kurma ya ji tana ringin daf da yasashen hannun Kausar dake yashe ya sake du ya fice a hayacinsa

Da sauri ta dauke kanta, har zuciyarta bugawa take yi, wani takaici na neman kunnota gannin sunnan dake kai watau ATAMPA sai ta ji kamar tana dagawa ta kirta masa Alllah ya isa da masa tsakani da ita, to in ba yana neman sakata a halin ha'u'i ba a gaban Aba? Sai dai kashhh, a dole hawaye suka tsinke mata a lokacin da Aba cike da wani yannayi na son ta daga wayar ya ce" KAUSAR ba kiranki ake yi ba?"

Kai ta girgiza da sauri tana share hawayen dake sake zubo mata murya a kurya ta ce" Ba kira bane Aba"

Aba ya kafeta da duba kadan yana fadin" Aa, kamarya ba kira bane, daga mana wannan na uku ne fa, kukan meyema kike ni ba an kusa shan ruwan ba? Ko yau juwar da karfi ne?"

Kai ta sake gyadawa , ta dauki wayar ta mike da kyar ta shige ciki ta je cen bayan katifar Mama ta duka ta labe sosai murya a shake ta amsa wayar tana cicijewa da son sannin wani bakon munafurci ne wai wannan kiran nata ba lokaci?

Murmushi Mujaheed ya yi , da yannayinsa na sanyi sosai ya ce" Wai kina jin kishirwar nan ta yau kuwa Kausar?"
Chapter 13 · 0% Book details