← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 116

Sashe 47

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine a gaba, yana sanye da bakin wando dogo na sweet, sai farar riga kal a ciki sai cravate mai ruwan maroon da dan fari fari jikinta, sai rigar likitoci fara kal wace ta dan sauka har kusan gwuiwarsa kadan, sai abin awon bugun zuciya dake rataye a wuyansa, hannunsa na hagu daure da agogo kirar kampanin ROLEX na daman kuwa ya dan tatare rigar har zuwa kaurin hannun nasa wanda ya bayanar da jijiyoyin hannun rado rado da tarin kwarjini da fuzga irin ta cikaken gamsheken namiji ta tafi da tafia har ya karasa kusa da baban teburin kwalbar da chef ke biye da shi da sauran likitoci biyar mata biyu maza uku manya manyan likitocin da ake ji da su a kasan nasara biyu sai hausawa uku kowane cikin shiga tasa shima irin ta likitoci ya karasa nan suka dan zanta kasa kasa inda baka jin komai sai dan abin AC dake watsa sanyi domin ko numfashinsu ba fita yake yi da karfi ba

A hankali ya ajiye farar takardar da aka bashi mai dauke da bangare bangare na du wani ma'aikacinsa na asibitin nan harda baki ba tare da ya karanta ba ya mike tsayinsa a gabansu ya dauko dubansa tun daga cen kurua kurya ya ringa binsu da kallo a hankali har ya dawo bangaren da ake nufin nan ne bakin suke su su takwas cif kennan

Lokaci daya Gabanta da nasa suka buga, Bugawa mai tsananin gaske

A hankali ya lumshe idannuwansa ya kai hannunsa na hagu ya dan sosa gefen hancinsa sannan ya sake daure fuskarsa tamau tamkar bai taba sannin wani wai shi daria ba a lokacin da ta kai hannunta na dama ta murza idannuwanta ta sake murzawa ta bude su tarrr a saman fuskarsa da matsanancin mamaki ta budi bakinta tana dan kokarin mikewa duda rawar da jikinta ya karra kwasa tana kallonsa ta ce""''

😌😌😌😁 Mun shiga uku😤😤😤😤

*wollah in fada maku na ci waya, sai dai a yi hakuri har mu samu daidaito da ita ko na cenza wata, thank you*

😔😔😔😔😔😔😔😔
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 💓2️⃣7️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Tana kallonsa a saman lebenta ta iya furta" TAUFEEK?"

sai dai mikewar da ta so yi bata samu yi ba wanda ke gefenta ya kama mayafinta ya maidata zaune saman kujerar kamar wani wanda ya santa ko suka yi sabo da shi, shi kuwa tunda ya zauna addu'a ce yake yi a kasan zuciyarsa kan Allah ya sa a dauke su summa su samu wannan dace na kasance ma'aikatan wannan asibiti mai daraja

A hankali ya dauke dubansa ya sake tsayawa cirr a gabansu baki daya kafin ya bude bakinsa
Cikin gogagen turanci, turanci irin na gogagun wa'inda suka koye shi har suka so su fi mai kora shafawa, watau su fi turawan iyawa domin nasu turancin na haihuwa ne sukan iya yinsa yadda suka yi niya koda basu ba komai hakinsa ba

Da salama ya fara yi, wata salama irin ta nagartatun yan gayun nan, sannan ya fuskance su ya shiga bayanin abinda ya tara su a wajen

Ba alamun wasa ko zolaya a tsakaninsa da su ya ce" Kamar yadfa kuka sani a wajen aiki bana wasa bana son a min wasa dan abu kalilin na iya aika mutun kiyama idan har ka yi wasan, hakan ya sa nake aiki ba sani ba sabo, in ka iya mu yi, idan baka iya ba ka koma ka koya!, Ina fatan du kun san haduwar nan na daya daga cikin abinda yake wajibi a garemu du karshen wata? "

Kusan a tare suka amsa da yes sir
Hakan ya saka shi dan yin murmushi sannan ya juya ya koma wajen abokan aikinsa ba tare da ya sake furta A ba

A lokacin ne Chef ya karaso gabansu ya dora daga inda ya tsaya ta hanyar gabatar masu da wanene shi, watau shi wanda ya tsaya ya yi magana a gabansu a yanzu da kuma sauran ma'aikatan da suka shigo tare

A hankali suka shiga gabatar da rabe rabe dan kowani Likita da wa'inda zai yi evaluer , shi kuwa yana tsaye gaban teburin nan tsayuwa irin ta watsa kafa kadan, hannunsa na hagu cikin aljihun rigarsa ta likita wace ya kai sau uku Chef na sake kallon yannayin nan da alamun mamaki a fuskarsa, domin haka din nan da sir ya yi shine da kansa ya hanna cewar ina likita ina tsaye tsayen saka hannu a aljihu idan Kanada abin yi gwara ka yi da ka zo kana tunani a kan aiki, sai kuma ya ga ya dan dantse lebe sannan ya saki, hakan ya tabatar masa ko menene yau sir akoy abinda ya tabo shi ko yake shirin tabo shin

Mintina ƙalilan macen ta sanar masa sun daidaita komai, dan haka ya karasa shima wajen zamansa ya zauna sannan ya sake zuba ido sosai da sosai a kan harkar aikin

A hankali ta juyo dubanta daga kansa ta kalli Wannan bakon da suke tare a lokacin da ya rage muryarsa ainun ya ce " sister ko dai baki da lafiya ne? Na ga tun dazun kin yi wani iri kuma sir kike kallo, ki dan maido hankalinki nan idan an gama da su za'ai mana kuma mu fa shine zai yi mana ance baya bari wani ya daukar masa ma'aikata sai ya gamsu da iyawarka yake daukan ka"

A hankali , kamar wace take koyon juyar da kai ko motsi da kai ta juya daga fuskar bawan Allahn nan ta sake kai dubanta wajen da kwakwaluwarta ta toshe harma take son Sannin wanene wannan bawan Allahn

Ido hudu suka yi, idannuwanta a cikin nasa
A hankali ya sake zuba idannuwan nata tana kallon nasa, da wani duba kamar wace ke son sai ta ga wani abu da ta sani a cikin idannuwansa, sai dai wani yannayi na bacin rai da take karantawa a idannuwan nasa ya sakata dauke dubanta ta juyo wajen bawan Allahn nan wanda ga dukkan alamu zai yi dan surutu dan sunna kuskus da na kusa da shi ne

A hankali ta mika hannunta ta tabo farar rigar dake jikinsa dan ba zata iya masa magana ba, gashi maganar tasu kamar ta kurame ne dan ba mai daga sautinsa kowa na dan abinda ya fi tsaye masa a rai ne cen ciki ciki kamar munafukai

Muryarta a shake ta ce" To ama, wannan din wanene shi?"

Ido ya dan zarro da dan mamaki a kwonce saman fuskarsa ya ce" Baki san professeur Mai kwano ba?......."

Gabanta ya yanke ya bada wani irin karan da kunnayenta da zuciyarta ne kawai suka iya ji

A hankali ya ce" Ama bakya kai ziyara manyan asibiti ko?, Wannan yanzu baki sanshi ba a matsayinki na likita? Ai ko patient sun san shi, dan da kika ganshi nan a kasar nan shine yaron da ya fara zama professeur a fannin aikin zuciya da kannanun shekaru, dan yadda mahaifiyata ta fada min a shekara talatin da takwas tuni ya fito a rikake jajirtacen likita, ke dai Allah ya sa munada rabo , in muka samu an gama...."

Da sauri ta kifta idannuwanta, shekara talatin da takwas....., No ba TAUFEEK dinta bane, ba nata bane, TAUFEEK dinta ai shekarunsa dududu basu wuce talatin ba, kuma TAUFEEK dinta dalibi ne, bayan wannanma yau ta san TAUFEEK da har zai bace mata????....., Dan haka da har kwarin gwuiwa ta ce" Wai meye sunnansa complet"

*"Mai kwanoni ELHAJ Zakari Muhammad TAUFEEK"* ya fada cike da begen sunnan kansa yana kai dubansa bangaren da TAUFEEK din ke zaune

Da sauri ya dan zarro ido ya juya ya gyara zamansa yana kimtsa kansa ɗan sai ya ga kamar su Sir ke kallo
Chapter 47 · 0% Book details