Sashe 106
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse ta dubi TAUFEEK, dan son ganewa in har yana amana da furucin matarsa, sai ta ga nasa fuskar a hade take bai wani bada damar a soke maganar ba kennan, dan haka ta mike tana fadin " A'a madame ki yi hakuri ai asibitinmu ba gidan tauye kowa bane gaskiya , dole a bi maki hakinki"
Da sauri ta juya ta fice a office din,
Khausar ta zuba masa ido a raunane ta ce" Me yasa zaka min haka? Ka san hakan na iya jaza min rashin zaman lafiya da ita bayan karkashin ta nake?, dan Allah ka ce masu ba komai karma a mata maganar, aikin kasheni zai yi ne? Ko menene zan iya yi mana, haba TAUFEEK sai ka sa a tsaneni cikin abokan aikina"
Banza ya yi mata ya fitar da abincinta yana faman ta ci, domin ba zai iya ce mata komai ba sai tension dinsa ta sauka, sai dai ta yi hakuri dan babu wanda zai wulakanta masa ita ya kyale shi, ko waye kuwa sai dai inda ba zai iya ba ya fadawa Allah wato iyayensu, bayan su baya tunanin zai yarda wani ko wata ya wulakanta masa mata, in tana da laifi ok zai san yadda zai bima abin, ama fa a yadda ya san matarsa bata da wani laifi karya ne kuma a wukakantata a wajen da ta isa !
Yana faman ta cin ita kuma ta dage sai ya yi kiran docter Maimuna yace a bar maganar aka sake neman izinin shigowa
Dan jim ya yi dan ya tabbata sun masa zuwan taron dangin nan kamar yadda suka saba in ransa ya bace a kan daya sukan zo ne baki dayansu a bashi hakurin abin, gashi shi rigimar yake so a yi gaskiya dan an fa tabo shi
Da kyar ya bada damar su shigo
Ai kuwa kamar da wasa doctors suke shigowa karshe docter Mufeeda ta shigo kanta a kasa idannuwanta har sun haye dan kuka domin ita ta gama YANKEWA cewar korarta zai yi, saima da ta ga docter Maimuna hankalinta ya idasa tashi, docter ta mata tassss ta mata fadan hakan dan bata da wani dalili sannan ta sakota gaba da manyan likitocin dake iya tankwasa shi a bashi hakuri, a nan ta sanar masu kaf cewar matarsa ce, Docter Mufeeda ta wulakanta
A yadda yake zaune da cokali a hannunsa yana rike da hannunta daya bai cenza yannayi ba, bayan sun shigo dinma kallo daya ya masu ya sake duban KHausar ya ce" Ha mana bada na son gardama ba zaki ci abincin ba?"
KHausar ta tsare shi da kallo tamkar zata saka ihun kuka
A raunane cike da rikicewa ta ce" Ni zaka ma haka ko? Ni ko?" Sai ga hawaye sun bale mata ta sada kanta tana jan ajiyar zuciya
Docter Maimuna ce ta saki murmushi gannin ya maido hankalinsa kansu ya harde yatsunsa yana kallonsu
Docter Aliyu ya yi murmushin shima ya ce" A gafarcemu professor, in sha Allah laifin da muka aikata ba zamu kuma aikata makamancin sa ba, a yi hakuri
Nan kowane idan ya budi baki hakurin ne yake badawa har aka zo kan Docter Mufeeda
Tana fara magana itama sai hawayen ta sada kanta ta ce" I'm sorry sir, in sha Allah ba zan kuma ba, Madame ki yi hakuri ba zan kuma ba"
KHausar ta girgiza kai da sauri , a hankali ta ce" Docter Walahi ba nice na hadaki da shi ba, Ni saima da nace ba komai , babu abinda kika min, dan Allah ku yi hakuri "
"KHausar ya isa haka tashi ki shiga ciki" taufeek ya fada a tausashe yana kallonta
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike ta nufi cikin ta rufe
Yana kallonta ne har ta rufe din sannan ya sauke ajiyar zuciya Sai kuma ya maida dubansa kansu ya basu damar zama sannan ya ce" Ya wuce, ba a kan Matata kadai nake iya yin haka ba, a kan kowa ne idan har na ga rashin adalci zan tsayawa ma'aikacina, kamar yadda kuka sani babu wanda ke raina ku, hakanan babu wanda zai wulakanta na kasa da shi dan Allah ya bashi dama, dan kina babba a wajenta nima baba nake a wajenki, ba wai maganar kina aiki karkashina ba a yau in sakamaki na yi du inda na hadu da ke ina iya cin zalinki, kin fahimta? Ina iya mayar maki da rayuwa cikin kunci in na so takuraki!"
Su Dukansu dai hakuri suke ta bayarwa har ya gama fadansa ya salame su, sannan ya sake tarda KHausar wace ta cika ta cika sosai, yana shiga suka haura sama sai masifa take tana fadin yana son hadata da abokan aikinta , shi kuwa ya ringa bata baki cikin tausasawa har sai da ta shawo kanta ta sauko ta ci abincin sannan ya dauketa suka yi gida domin ya kula ba lafiya gareta ba sai tare kai take yi kuma ta ki yarda ya dubata tace juwa ce kawai dama tana yi in bata ci abinci a kan lokaci ba
Koda suka je gidan wajen Mama ta je ta amshi jibda ta koma bangarenta ta shaka sosai, tana sakuwa ta sauko ta shiga kicin ta shiga girkinta hankali kwonce har ta gama ta koma dakinta ta kimtsa ta haye salayarta
Kwonci tashi cikin Yumnah karra girma yake yi , inda ta karra ɗorawa kanta abubuwan da take gannin zasu fisheta, domin halaya raguwa dai suka yi ama ba barin su ta yi ba, dan kuwa koda ya nuna mata maganar kaura ita dake fatan a fidata daga gidan saboda takurar HAJIA a da, a yanzu ta ce ai ba inda zata je tana nan a dole aka shiga tada gini a dayan bangaren dake da fili dan KHausar ta koma, domin ya fada mata tunda ta ki komawa wancen gidan a nan din zata yi ta zama har yadda Allah ya yi
Sanadiyar ginin nan da ake kyankyarawa matan mahaifinsa suka tada rigima ta mamaki, dan kuwa karara HAJIA Nawarah ta nuna uba fa ba na shi kadai bane, su da suke da mata ai su ne ya dace a ringa yiwa gurno mai kyau ba mutun baba kamar TAUFEEK ba wanda yake da shi kudin ama dan bakin ciki yana gindin na uba dan kar yan uwansa su samu
Allah ya taima tsakaninsu matan da uban ne suka yi rigimar HAJIA bata sani ba shima TAUFEEK bai sani ba har aka gama ginnin aka kwaso kayan KHausar aka gyara mata bangaren ya zuba dukan abinda ya dace wanda zata rayu cikin walwala kamar yadda wancen bangaren ya malaka, kuma nan dinma dakunna ne har biyar kamar cen da kicin da komai Masha Allah
Washe garin ta tare sai da Yumnah ta wuni gidansu, sai dai bata samu yadda take so ba domin ta tarda mahaifinta a gari yama na yi ya tarkatata ta koma gidanta da nasiha da tsaraba irin ta iyaye ga cikinta ya fito sosai dan a yanzu ya yi girman da ta kusa shiga watanta na haihuwa
Bangaren KHausar tana rayuwa a cikin wannan familly ne tamkar tana rayuwa a familynta domin a watanni bakwai da ta yi a cikinsu zata iya cewa Alhamdulilah,dan kuwa tana ba duk wani wanda ya girmeta girmansa kuma tana kiyaye duk wata fitinar da za'a ce itace sila, tun daga kan HAJIA baba kuwa har auta ba zata ce ga wanda ya mata ido da ido ba, domin su auta idan mamansu ta fita fit suke su je bangarenta in tana nan su yi kallo su dan taba fira, dan irin yadda take jansu a jiki sun fi sakewa da ita fiye da Yumnah, domin Yumnah Akoy tsare gida, kuma tunda ƴaƴansu ya kara auren nan har iyayen nasu take baya baya da su , tana zuwa ama ba kamar da din nan ba da take zaunawa su yi ta sake sake tsakaninsu, domin yanzu har Mama tana zuwa ta gaisar sai dai babu wani abu tsakaninta da Maman bayan gaisuwar wace ta maidata kamar dole ne ba abinda ya dace ta yi bane dan isar abin a duniyarta, haka kuma tsakaninta da KHausar ido ne in sun hadu KHausar din na mata Salama takan amsa a takaice Shikenan dan kuwa bata tunanin zata iya yin wani dogon zumunci da matar mijinta!
Tsakaninta da mijinta ne kawai tafia ke tafe ta fahimta da kokarinta na itama ta samu fuska yadda ya dace, Allah ya taimaketa shi din mai son kare hakokinta ne sai take samun kwonciyar hankali harda rigingimunta yakan Saurara ya kuma bata lokacinsa, sai abin ke kayatar da ita , ama a lokacin da ta so nuna ita zata je sabon ginin ne ya nuna mata bata da wayo sannan ya ja mata dogon kashedi a kan hakayar nan nata da fada mata nan fa da ta zaba ta yi kokari ya zama farin cikinta dan in dai ba ran Mai kwanoni ya bar gangar jikinsa ba kafin shi ya mutu ya bar duniya ya zama wajibi a rabawa ya'yansa gado ba, ba zai taba fidata daga nan ba, tundaga shi ta yi shiru da maganar take binsa
Tsakanin TAUFEEK da KHausar fahimtar junna, soyayya, shawara daya , sunne suka fi komai tasiri a zaman har ya zamo koda ba a dakinta yake kwana ba tana makale a zuciyarsa ne, bale shakuwar da suka idasa sakawa a tsakaninsu bata da abin fadi sai godiya wa zabil izati, Taufeek duniyarta ne, shi din farin cikinta ne, kuma aikinta tana zuwa ba fashi
Kwana biyu da kaurarta ta je gidansu weekend da kuma guzurinta na lalle dan a yi mata
Tunda ta je maimakun a yi lallen sai ta yi kwonciyarta ta ce da Mama in an jima ta tasheta dan Allah juwa take ji sosai
Sai dai bata iya tashin ba, sakamakon juwar maimakun ta saketa har sai da Aba ya dawo ya koma ya kawo wani magani da Mama ta saka ya kawo din ta shaka mata sannan ta ji ta saku har ta mike da mamaki ta nufi bayi dan yi alwallah domin lokacin sallah har ya wuce kuma TAUFEEK zuwansa biyu duka bata sani ba