Sashe 111
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mama, yace idan aka fita da Ni a bakin aurena....." Yumnah ta fada muryarta a sanyaye tamkar wace take daf da summa, domin kana ganninta zaka fahimci bayan tashin hankalin rikici da firgicin haihuwa harda na furucin mijinta ke neman tabbata, du irin zumudi irin na uwa da son ganin abinda ta haifa ita kunnayenta na jiyo mata kukan yar da bata kashewa kowa ba bata birnewa kowa ba ta kasa amsarta ko ta dubeta, ji take yi kamar tana daf da barin duniyar baki daya
Bata taba tunani cewa wannan lamari zai juye mata haka ba, yau gata zaune kishiyar da take tunanin ko fatar Mamanta ba zata taba gani ba koda ta haihu ce ta amshi haihuwarta, karshe mijinta da take hangen wannan rana da tunanin irin farin cikin da zai yi na murnar gannin abinda ke cikinta ya juya ya fita bayan ya ji kukan shigowar abinda ta haifa duniya bai ko kali jaririyar ba ya yi tafiyarsa ? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une
"Yumnah, ki yi hakuri idan bamu je aka dinke ki ba wajen nan tsami zai yi sai kin wahala sosai koda awa daya ya dauka, an fi so da zafi zafin abin haihuwar nan a dinke , mu tafi" mahaifiyarta da ta kamata sosai ta rungumeta take takawa da ita a hankali
Murya na rawa Yumnah ta ce" Mama, TAUFEEK, TAUFEEK bai kalli babynsa ba, bai kalleta ba, Mama ban taba tunanin zai iya yin fushi irin wannan ba, Mama babu inda zan je koda kuwa rubewa zan yi, tunda ya fadi haka ba zan taka kofa ba, idan na mutu ai Shikenan, ko me na masa ai sai ya sasauta min haihuwa fa Mama wayo Allahna " ta karashe tana sake fashewa da wani kukan mai tsananin gaske
Akilah dake gaba da babyn nan ta dan dakata har suka tardota suka karasa bangaren na Yumnah sai aukin sannu suke yi mata, hankali tashe mahaifiyarta ta zauna tana cusa hannayenta bibiyu a cikin hijab dinta tana murza goshinta da gashinta tana ji kanta kamar zai buga da ciwo dan tashin hankali kaffafuwanta kuwa ji take yi du mujirya ke jansu kamar ba nasa ba
Ya Allah, wannan wace irin masifa ce, shin du tsanar ce ta haifar da haka tsakanin yarta da mijinta ko menene? Me aka yi da zafi da zai yi haka?
Akilah na shiga ruwa ta tara mai zafi sosai yadda zata iya saka babyn ta zauna ta wanketa sal , yarinyar sai tsala ihu take ta fito ta kimtsata sannan ta jona wani ruwan mai yawan gaske ta tara shi sosai yana ta tururi ta fito ta samu Yumnah kwonce saman shinfidar da Mamanta ta mata har yanzu ta ki ta cire zanin da ya yi kaca kaca da jinni , fuska daure ta ce" Tashi mu je na maki wanka"
Yumnah ta dago tana kallonta , da kyar ta budi baki a raunane ta ce" Aunty, ba zan iya wankan nan ba, dan Allah ki ba TAUFEEK hakuri"
Akilah ta daure fuska tana kallonta sosai ta ce" Idan kin kula da jikinki zaki bashi hakurin da kanki, in har ya ga zai iya yafe maki ki ci gaba da raina masa uwa tashi daya zai yafe, kin san ke kika san ciwon taki mahaifiyar shi bai sani ba!"
Da mamaki Mamansu dake jijiga babyn take duban Akilah, dan kuwa da wahala ka ga Akilah da magana da dacima bale har haka
Ita dinma murya a sanyayen ta ce" yaya zaki ce haka? Wani ya raina masa uwa ne?, haba Akilah hankali zaki daga min bayan kina gannin abinda yake faruwa?"
Akilah ta sauke ajiyar zuciya ta kama Yumnah suka nufi bayin
Ba sasautawa ta yi mata wankan nan sannan ta tara ruwan masu dumi sosai ta danata ciki, ita kuma ta ringa ihu dan kamar zanta zai fita take ji, sosai wajen ya fara yin tsami sosai da sosai
Sai da ta riketa suka fito daga dakin suka samu Mamansu na waya da babansu tana sanar masa ai a gidama ta haihu abinda ya sa bai gansu sun dawo ba bata jin dadi ne zasu shigo komai dare in sha Allah
Bude wajen da ta tanadi su audugar mata da pant ta yi ta ciro mata komai sannan ta miko mata ta koma ta zauna nesa da su kadan tana kallon mahaifiyarta ta ce" Yaya za'a ce ba'a wulakanta mahaifiyarsa ba bayan abin a bayyane yake ba a boye ba?, na sha fada mata cewar idan ta yarda TAUFEEK ya kula da wani lamari na rashin da'a da take wanzarwa tsakaninta da mahaifiyarsa baki daya darajar da take tunanin tana da ita a duniyarsa tana iya nema ta rasa, uwa wasa ce?, ta san ciwon nata mahaifiyar ama ta kasa girmama ta mijinta? Ban taba gannin banzan tunani irin naki ba Yumnah, ban taba haduwa da mai taurin kai irinki ba, shigowata kasar nan uku bayan aurenki saboda ke, ama a banza, to zan fada maki magana daya tak, duk wani wanda zai so ki kashe aurenki ki fito ba masoyinki bane, mahaifiyarmu ba zata taba fita daga bayanmu ba, haka Allah ya haliceta idan me muka zo mata da shi tana bayanmu ne, da yawa zasu yi anfani da wannan damar su wulakantaki idan har baki san ciwon kanki ba, wace soyayya ce abokiyar ZAMANTA zata maki wace ta zarce Tata? Kina kallo basa son mijinki wace ke da zasu so ki? Na so ace kin yi wayo kin koma gefe kin kalli fadan da bai shafe ki ba wanda kika tarar ana yi a ahalin mijinki, tsakaninsu, na yi iya yina dan ki gane, ama kika kiya kika rintse ido kike daukan hudubar banza kina yabawa kanki dan a rabaki da kishiya!, su su raba kansu da ita mana? Kin kasa ganewa kansu suke nemawa mafita ta kowace fuska, ga dai haihuwar da ta dace ace zuwa yanzu kina nan tamkar sarauniya an zagayeki yan uwa da aminan arziki ana nan nan da ke, ama cikin ikon Allah halayanki sun saka sai kunshe y'a muke daga mu sai mu kamar y'ar gaba da fatiha!, a yanzu bani da abin ce maki, idan kin yi niya ki nemi mafita tun kafin jikinki ya lalace, dan nama kike kayan banza yanzu zaki rube ki fara wari a Gaza haɗawa a dinke a yi biyu babu, babu kyan wannan waje ai kin san TAUFEEK ba zai zauna da ke ba koda kece autar matan duniya!" Tana gama fada da wani bacin ran ta je ta karbi babyn ta wuce ta dauki zamzam da dabino ta wuce ta sauka falon kasa da ita tana jijigata tana tauna mata dabinon da niyar ciyar da ita da shi da kuma ruwan zamzam ranta a mugun bacen da ta jima bata shiga irin halin damuwa saboda bacin rai irin haka ba
Kwarai mahaifiyarta ta fi jin Yaren Akilah fiyema da ita, a tsaye take tana rarabawa kanta tunani da neman mafita a zuciyyarta, ga kuma mijinta ya ce da ita duk mutanen gidan nan basu isa duba mata y'a ba sai itace zata zauna? Ta koyi kara mana ta juyo gida ta barta koda da Akilah ne
Neman rasa madafa ya sakata fitowa bayan ta saka hijab dinta ta shiga neman Mai kwanoni a cikin gidansa
Da kyar ta ganshi bayan an mata iso ta duka tana sake sanar masa halin da ake ciki
Sosai ya ji zuciyarsa na neman shiga wani hali, subahanallah ta sauka? Ama babu wanda ya zo ya sanar masa? Bai jima da shigowa daga wajen datawan Anguwar ba sun je neman auren jikar malam, jin shiru ya zaci ana cen ana gumurzu, bale da bai ga TAUFEEK ba ya zaci yana ciki ana taimaka mata dan ta sauka,
Wayarsa ya dauka ya shiga kiran numbar TAUFEEK din
Kira na farko ya daga yana yin salama
Murya a hade Baba ya ce" kana ina?"
TAUFEEK ya kalli HAJIA dake jan carbi tana gyangyadi, tunda KHausar ta ishe shi da kukan sai ya je ya duba Yumnah ya baro bangaren nata ya dawo wajen HAJIA wace ta masa damu da ƙanƙara tace ya sha ya KWONTA ya kuma cire damuwar kowace Shegiya babu wace zata dagawa jikanta hankali shi kuma ya yi kwoncen burinsa ya je ya dauketa ya kaita a masa hoton cikinta, ama ya san ba zata yarda ba, hasalima ya ga ta nufi wajen Mama ya tabbata tana cen sunna kwasa
A tausashe ya ce" Aba ina wajen HAJIA"
HAJIA ta yi firgigit ta farka daga barcin ta miko hannu tana fadin" Bani shi nan, Allah na tuba masifa muna sume ma yi muke, mai kwanoni kana ji na? Wace tsiyar kake so da jikana ne Ni? Ka fa kiyayeni an jima da shiga duniyar yancin kai tsaf nake kai karar ka a mana tsakani, yau ga neman magana , yaro sai motsewa yake saboda kun tsane shi? To Ni ina so kuma ba zan amince a lalata min kwonciyar hankalin jika na, ka fadi maganarka wa Ni in ji daidai nake da kai"
Tunda ta fara fadan Baba ya sada kansa tamkar yana gabanta, a tausashe sosai ya ce" Ki yi hakuri HAJIA, ki yi hakuri dan Allah, Allah ya huci zuciyarki, babu wanda zai masa komai, dama so nake yi mu hadu da shi a cen bangaren iyalin nasa da KHausar da kuma mamansa dan a sasanta wannan rigimar domin ban ga anfaninta ba sam"