Sashe 46
Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wadinnan watanin uku da ta yi tun daga kan mai gadin kofar asibitin har zuwa manyan ma'aikatan babu wanda zai ce ga abinda ta masa marar dadi ko na raini ko aka kamata da wasa da aikinta ko kula samari ko dai wasu halayan mararsa dadi, ko gadi Khausar take yi ba zaka ga saurayi ya zo wajenta ba, haka kuma manyan doctors dake aiki maza wa'inda suke da dabi'un kula mata babu wanda ya matsewa Khausar waje dan sun san da sunnan wanda ta shigo wajen, watau ubansu ne idan suka yi wasa komai na iya faruwa, mutumen da yake abin wasa a wajenta su dodonsu ne
A ranar da ta gama harda dan hawayenta , a lokacin ne aka tabatar mata kwana daya tak take da shi na lahadi ba zata je aiki ba, likiti ta tabatar ta tafi tunda sasafe babar asibiti mai sunna *LAFIYA* wace aka ce nan ne zata je ta yi aiki a matsayin ma'aikaciya
A ranar farin ciki a gidansu ba'a magana, ta nemi layin TAUFEEK har ta gaji da nema bata same shi ba, ta so tafiya gidan a washe gari sai dai kitso da wankin kafar da ta je da kuma wajen Fusam dan amsar wasu yan kayayakin gyara a dole ta yi dare bata biya gidan ba, ama ta ci gaba da neman layinsa cike da mamakin rashin samunsa , sai da dare ya yi ta hakura dan yanzun in dai ba shi ya yi kiranta da dare ba to fa bata kiransa dan har yanzu bata gane manufar matarsa a kanta ba
Shi kuwa a irin lokacin da take nemansa wayarsa sam baima san inda take ba, aikin da ya gagabo masu shi da manyan ma'aikata suke kai, watau tantancewa da fitar da kwararu masu son aikinsu da kyma ware maus shiririta ciki harda asibitinsa clinik dinsa privet mai sunna *LAFIYA!* wace a gobe litinin yake da niyar shigarta da karfinsa dan ba zai taba lamunce abubuwan nan ba, manya manyan abubuwan dake hargitsa shi a aikinsa shine likitan da bai iya aiki ba, yana iya yin komai a kan haka, shi yasa yake da taka tsantsan da tsauri, dan a ganninsa du ma'aikacin jinya ko na dabobi ne ya dace ace kwarare ne a fannin aikinsa ba haure ba, dogon aikin da ya saka shi bada kamar shekara da shekaru kennan kuma bai ga alamun zai daina yanzu yanzu ba
Tun karfe bakwai Khausar ta gama shiri mai sunna shiri, shirin da Mama ke binta da kallo cike da mamakinta da kuma addu'a a kasam zuciyarta, domin bata taba gannin yarinyar ta yi shiri haka ba,
Ba wai makup ta makawa fuska ba, ama ta saka kwali daidai misali ta kuma saka dan jan baki mai ruwan kasa dan daidai da lebenta na kasa
Girarta cajeta ta yi sosai, kitson da kai mata kuwa sai ta daura ribom mai kyau ta daura dan kwalin atampar da ta saka doguwar riga wace Mama ta dinka mata sannan ta dora hijab mai ruwan sararin samaniya mai yar walwali a jikinsa sai jaka ruwan hijab din da takalmi plate ruwan hijab din sai dan mayafi da ta yafa wanda yake shara shara ne du girmansa dan ba abinda ya rufe a tsarin halitar jikinta wace zuwa yanzu tumbin nan gana dayansa ya sasabe ya mugin zube sakamakon wahalhalun da ya shiga da kuma dan hadin da take masa na bawan albasa da lemun tsami da cita tana sha wanda sosai ya sake sabe tumbin ama bayan tumbin babu abinda ya ragu kama daga duwawunta da cinyoyinta, sai gayu da ta fara koya na mamaki a wajen uwar gidanta docter Rauda da kuma hajiyarta Fusam, ga wani tsararen kanshi da take fitarwa mai sanyi ba mai hayaniya ba
Tsuru ta yiwa Mama cike da jin kamar a takure take ta juya tana fadin" Mama bari dai in dauko hijab, ga jakata da rigar aikina a ciki Mama"
Mama da dan sauri ta ce" Ke Khausar zo, me wannan din ya yi?"
Sai kuma ta yi shiru tana dauke kanta a ranta tana mamakin yau itace da cema khausar kar ta fita ba hijab????
Tana shirin ce mata ta dauko hijab din Aba ya shigo yana fadin" Ina Khausar din maza zo ga dan sahunki nan, shi zai ringa kaiki yana dauko ki, ki tabata wayarki da caji ga wannan katin ki loda dan kiransa in kina so ya dauko ki, ga kuma kudin abinci, a kula sosai yar albarka a kula bana son biye biye, bana son ka je aiki ka ringa abinda ba shi ya kaika ba kin ji? Ki kama mutuncin kanki kin ji ko?" Ya idasa fada yana riko jakarta dake gefen mamanta ya Sakkata gaba suka fita
Mama ta yi murmushi bayan ta rakata da addu'a ta mike ta shiga fitar da kayan abincin da aka kawo tana dubawa, harda su kwai da doya da su waken suya da madara, tunda ta kawo albashinta harda su kuka da mahaifinta ya raba biyu ya bata rabi wai ita bata son ko sisi, da kyar shima uban ya amshi duka, ama gaba daya kudin a hidinar gidan ya zuba su, ya siyo matta wata waya yar madaidaiciya da hijabai sababi har biyar, ya masu siyaya suma sannan ya daukar nata dan adaidaita sahu ya kuma ware kudin abincinta.....lalle a wata ukun nan sun mori albashinta sosai, ama na watan nan sun fi morarsa domin na watanin da suka shige a hidinar kannenta ta saka kudin kafff
Tunda aka ajiyeta a bakin makeken get din asibitin ya ringa taslima a zuciyarta, lalle a yadda ake kwatanta masu asibitin nan ba'a fadin ainahin yadda yake
Tafe take tana tambayar baban wajen reception har ta karasa tana karra bin komai da kallo tamkar wace ta fita daga kasar ta je kasar turai
Madubai ne, shukoki ne, ma'aikata ne sunna ta aiki sai sake gogewa ake yi bayan ba wani dati da wajen ya yi , haka kuma komai a tsare ga kanshi dake tashi ta ko'ina
Ajiyar zuciya ta sauke cike da samun kanta a rudu, yanzu a nan ne zata yi aiki? Ma'aikatar da akace gagaruman likitoci ke cikinta, du wani likita mai ji da kansa kana samunsa a nan cikin sauki, to ita a matsayin yar goge goge ta zo nan ko
Da ido take bin masu aikin, sai ta samu kanta da jin sanyi sanyi da ta saka sabuwar atampar nan, yau da ta rasa wajen buya da bata dan kimtsa kanta ba
Wata mata mai riga ruwan goro ce ta kula da yadda Khausar ke bin mutane da kallo ta dasu a waje daya tunda ta shigo baban filin dake rarabe da mutane daban daban kowane a bangaren da yake nasa aiki ta tunkarota tana tambayarta ko ta bata ne?
Da dan barin baki Khausar ta mika mata ambulop din da aka bata tana binta da kallo, ita kanta mai wanke dakin masu haihuwar nan sai ta dauketa aiki jama'a, kwas kwas da ita harda farin gilas na yan gayu
Dubawa ta yi sai ta kalleta da sauri ta ce" Kai, to zo maza na raka ki sunna sama yau oga na tantancewa bakinma du sunna sama maza ciro rigarki saka mu je wajen chef sai ya saka ki bangaren da kike, Allah dai ya sa ki samu karbuwa dan baki taki Sa'a ba gaskiya a hasale oga yake kuma yau yake fara tantancewa , Allah ya da kin iya aiki yar nan, dan kuwa daya bayan daya sai kun saka ruwa ne da sauransu aikinku dai na likitoci....."
Cikin Khausar sai da ya amsa, nan take ta ji wani shaka da tsoro na neman aurar zuciyarta
Tantancewa, dama a makaranta ana cewa itafa asibitin nan ba'a wata ba'a yi tantancewar nan ba, tsaf ake iya cireka a maye gurbinka da wani ba wasa, shi yasa likitocin kowa ke aikinsa ba ji ba gani domin ko dan albashin wajen ba zaka yi sake a yi maka sakiyar da ba ruwa ba
Biye take da ita har suka karasa wani tankamemen hl wanda sunna shiga kanshin wajen da sanyin wajen ya sake sakata a hali na tsoro da tunanin lalle yau zata samu baban abu da ake kira ta leko ta koma, dan bata idasa fita a hayacinta ta ringa kallon mutane tamkar ba yan adam ba da irin tarin kayan aikin wajen sai da suka karasa aka amshi ambulop dinta aka duba aka yi mata tambayar ina kit dinta na kayan aiki irin su abin auna zuciya abin daukan zafin jiki dai da sauransu ta nuna shi hannunta na dan rawa aka umarceta kan ta fitar da su ta je ta layu wani bangare gefen hagu inda wasu bayin Allah ke laye kamar an masu mutuwa kowane na nazari da addu'a a zuciyarsa domin su kusan bakwai ne kuma dukansu baki ne yau suka fara zuwa asibitin
A kala sun dauki minti sama da arba'in ana ta karra gyare gyaren wajen
Ba wasa a lamarin
Kowa kai kawo yake cikin manyan har ta ga an dana wata katuwar tv ta nuna shigowar wasu motoci uku balbalin asibitin sannan aka kashe tv din aka sake tsatsaresu da duba kamar wa'inda suka aikata katon laifi duba irin na to fa ga maza bisa kanku, ya zamto harta manyan likitocin sun shiga taitayinsu sunna sake bin dukkan abinda suka san na iya zame masu matsala sunna tabatar da sun daidaita komai da komai
Minti kusan sha biyar kofar mai dauke da madubi ta wangale,