← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 116

Sashe 109

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da kunya KHausar ta sada kanta tana janye hannunta , gaba daya ta shiga a halin rudu

Taufeek ya sake janyota jikinsa sosai yana dage rigarta a tausashe ya ce" Kar ki sako kunyar nan yanzu, na fi so na gane eh ne ko a'a? Ina son ganewa"

Ajiyar zuciya ta sauke, ta rasa ita amsar da zata bashi, abinda ta sani shine kwarai lokuta da dama idan mahaifiyarta ta tsananta juwa kwanaki ƙalilan tsakani zata tashi da nakuda ne, ama shin itama irinta ne ko yayane?, Ita dai bata sani ba, kuma shima ta tabbata ya shiga rudani ne na tunanin maganar nan, ko dan shi din likitan kwakwaluwa ne ba na mata ba? Ama koda likitan kwakwaluwa ne yanada wasu sani a fanin matan, shine zai fada mata ai ba ita ba,

A sanyaye bayan ta kama hannun nasa itama ta ce" TAUFEEK ban sani ba, ban sani ba, Ni dai na san ina juwa, ina cin abinci fiye da da, wani lokacin kuma nakan ji gajiya sosai ama da zarar na yi barci Shikenan sai ka ga komai ya wuce"

Zai kuma yin magana wayarsa ta ringa ringing sosai a dole ya dauko ya daga bayan ya ga mamansa ne

Da wata Muryar da maman bata cika amfani da ita ba ta ce" TAUFEEK dama Yumnah nakuda take yi tunda yama ban sani ba?"

A hankali ya samu kansa da lumshe ido, a Nutse ya ce" Nakuda?, Ban je part dinta ba , tana wajenku ne?"

Mama ta furzar da hucin bacin rai , ta cire hijab dinta ta ce" Ni na isa na san abinda take ciki ko na kai matsayin sani? TAUFEEK ace ina cikin gidan nan da raina da lafiyata ka auro macen da zata raina Ni? Tun ban yarda na furta ba har ta kaini makura? Ni makiyiyarta ce ko bata san girman mahaifiyarta ba da zata raina Ni?, Ace ina cikin gidan nan jikinta ya motsa na abin dake cikinta wanda nake cikin zumudin zuwansa duniya nake siye siye dominsa nake addu'a ba dare ba rana kan Allah ya nuna min, sai yanzu HAJIA nawarah ta shigo ta fada min cewa wai tunda yama sunna tare da mahaifiyar Yumnah a bangarenta tana kan gwuiwa YANZUN dai jikin ya motsa sosai ta yiwu haihuwar ce in sanar maka zasu tafi asibiti? Na nuna a kan me ba'a sanar min ba tace wai Yumnar ce bata so KHausar ta san tana nakuda sai dai ta ganta da abinda ta haifa? Wannan wace irin masifafiyar nataciyar gaba ce yarinyar nan ke fama da ita a ranta tana tare da yan zuga?, To bari ka ji, ina fatan matarka ta sauka lafiya, ama ka sani na kai makura , tunda har Ni Khadija ban isa da ita ba ba laifi Allah ya raya , ama Nima babu ruwana da dukkan abinda ya shafeta , ciki harda abinda zata haifa!"

Daga haka Mama ta katse kiranta ta jefar da wayar ta yi zaune a bakin gadonta tana dafe kanta wasu hawaye Masu zafi suka balo mata

Shin yaushe ne zata samu sasaucin zama da abokanan zamanta? Ko dai har ta koma ga Ubangijinta ba ranar samun sauki? Tun bata saba wahalaliyar raayuwar nan ba har ta gane in fa ba kanta ta rike ba komai na iya faruwa ciki harda sakwantar mata da cilon danta, sai ta basu lafiya take rayuwarta a gefe itama
Ama abu kulun cikin tugu da shari kala kala ake yi mata?
Tun tana da jan sawunta har yanzu da jinni ya dauke mata take kokowa da su da lamarinsu, shin yaushe zasu bata lafiya? Ace matar TAUFEEK, TAUFEEK nata , sai dai ta hangota da su? Me take tunani ne ita Yumnar?, Ba damuwa ko TAUFEEK suka kwace zata yi addu'a ta bishi da addu'a bale wata Yumnar banza da wofi, Allah ya taimaketa ga KHausar, wace ta mayar da ita tamkar uwar da ta haifeta, tunda ya auri KHausar take rayuwa da yanci itama a cikin gidan, take da abokiyar fira, mai yi mata girki ta kawo mata, mai zuwa ta yi mata fira, mai share mata kaso tamanin a damuwarta, kuma ga kyautar Allah ya bata itama, in sha Allah zata kaita asibiti da kanta gobe da safe a duba mata ita, su dawo ta raini cikin nan dan ba zata yarda ta koma aiki ba sai ta haihu da izinin ubangiji

A kalla ta dauki minti ashirin a zaunen nan tana share hawaye ta ringa jiyo hayaniya sama kamar za'a tsaga falon nasu

Sai da ta Saurara sannan ta ji gabanta ya fadi, ba dan komai ba sai dan tunawa da ta yi waye danta da tsinkayo muryarsa da ta yi sama da ta kowa, da Muryar kakarsa na dafe masa baya sai uwa uba Muryar mahaifinsa

A dole ta saka hijab dinta ta fito sanan ta nufi kasan tana kallon taron ba laifi harda maman Yumnah da yayarta da kuma Yumnar dake murkususu ko yaya aka yi aka nufo nan da ita kuma?

Mai kwanoni ne ya sauke ajiyar zuciya dan ya san yanzu rigimar ta lafa tunda wace ake rikicin kanta ta sauko, ya kuma san ita din mai hakuri da sanyaya fitina ce da KOWAMA bale in ta ga abin ya shafe shi, sai ya sauke ajiyar zuciya a karro na ba adadi ya ce" Maman Magidanci, ai gwara da kika sauko, shin ko me ya bata masa rai ai yana iya yin hakuri har wannan taa samu lafiya , haihuwa ai ba wasa ba maman Magidanci , sun fito zasu shiga Mota su nufi asibiti wai ya tarda su yace idan aka fita da ita a bakin aurenta sai kace ba likita ba? Kuma na yi tsawar kin ga HAJIA a gefe kin san dai ba barina zata yi in Hanna ba, dan Allah a yi hakuri a yayafawa matsalar ruwan sanyi, komai ya yi zafi maganinsa Allah, kuma hakuri shine ja gaban komai a rayuwa kin ji maman mai kwanoni?" (Wato ashe da baya kiran sunnanta dan fa ci sunan HAJIA ne?)

Mama ta kai dubanta kan KHausar wace mahaifiyarta ke sake talabarta dan ko tsayawa ta kasa yi, da gaske haihuwa ta zo mata dan kiris ya rage dan du ta fita hayacinta kukanma ya dauke azaba ta yi azaba kuma ga abinda mijinta yace
Mama ta ce" Elhaji a kaita asibiti mana, sannu Allah ya raba lafiya"
Daga haka maman ta juya da nufin komawa

Da mamaki ya ce" A'a, yaya zaki ce haka ki juya , wai yaya zaku tsaya wasa da haihuwa ne? Ke ku kamata a kaita asibiti" ya fada yana duban su KHausar dake tsatsaye, domin a lokacin da TAUFEEK ya maka wayar da suka yi da Mama a kas ya fice bai ce da ita ufan ba ta fito a guje ta bi bayansa tana ihun lafiya? Sai ta ga ya nufi bangaren Yumnah, da farko ta so komawa sai sai sunna tunkara ta ga an talabo Yumnar, a dole ta karasa tana aukin sannu, sai dai abinda ya fada ya saka su Dukansu rikicewa a lokacin da TAUFEEK, professeur TAUFEEK ya dubi tsabar idannuwan MACEN dake kan gwuiwa matarsa yace idan har aka fita da ita a bakin aurenta, sannan ya dubi mahaifiyarta yace da ita babu wanda ya isa ya wulakanta min uwata in ga darajarsa a duniya ko waye, sai kuma ya kalli HAJIA nawarah wace ta fara sarewa yace da ita a yau a gidan nan ko Ni ko ke, sai suka idasa sarewa duniya baki dayansu

HAJIA ce ta yi gagawar fadin" A kama wace? Sunna da damar tafiya da ita ama ka ji ai abinda mijinta yace , duk shegiyar da ta isa ta fita da ita a bakacin aurenta!"

Da mamaki Mai kwanoni ya sake yinkurawa zai yi wata maganar da tsawa da kuma rarashi da fadan a yi maza a kai baiwar Allah asibiti sai Yumnah ta yi wani irin ihu da nishi wanda ke nuni du inda kan d'a yake yana daf da zuwa duniya

A rikice suka rikice, gasu a falo su duka, Mama tuni ta komawarta dakinta ta datse da ky dan ta san mai kwanoni na iya cenza mata ra'ayi YANZUN nan, ita kuma ta yi rantsuwa babu ruwanta, abin ya isa haka, iskancin ya kai wajen da ba zata iya dauka ba kuma!

Kiri kiri TAUFEEK ya yi tsaye kikam a lokacinda KHausar ke sake sakin nishimai tare da bayanin fitowar kan Da daga jikinta

Da sauri mai kwanoni ya fice, kusan suka fita tare shi da KHausar wace ta yi bangarenta da gudu ta warto Safar hannu da kayan aikinta ta juyo da gudu gudu tana saka Safar hannun ta koma dakin hankalinta tashe , kana ganninta ka san taimako ne zata bada dan ceton rai

Wato an yi gudun Gara an fada gidan zago, sai ga KHausar din da aka so sai an haihu ta ji duke gaban Yumnah ƙafafuwan Yumnah Ware a irin mummunar warewa, jikinta bude a budewar da ko mijinta da wahala in ya taba gani a zamantakewarsu, jiki ya aune halitta ta zazago ta bude kai ya bado tana ihun azaba da ni'imar ubangiji har kai ya fito KHausar ta kama cikin kwarewa na cikakkiyar likita mai ruwa da tsaki a fannin amsar haihuwa ta juya jikin baby cikin dabara ta fitar da hannu daya sannan ta sake juyawa ta fitar da dayan kafin ta janyo babyn da ta tsalara kuka kamar a baakinta aka fara gwajin kukan, ta mike ta mikawa Aunty Akilah dake hawaye, hawayen girma irin na hukuncin ubangiji wanda ya fi kowa tsara komai, wannan shine kana naka Allah na nashi,daga wannan idan mahaifiyarsu da kanwarta suka ci gaba da wani abin to lalle zata dage da sanarwa ubangiji kan ya shirye su baki daya, a raunane ta sake kallon mijin kanwar nata wanda ya juya ya fice a lokacin da aka shiga musayar yawun ta karu, sai an yi mata ɗinki, gashi ya Hanna fitar, wannan shine ga koshi ga kwanan yinwa , ga amsar haihuwa daga wajen kishiya ga kuma ɗinki da kishiyar zata mata.........
Chapter 109 · 0% Book details