← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 116

Sashe 18

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Mama ta yi farin cikin haka, kuma kwarai ta san hakan ya yi, domin ko rijiya tana son kari kuma ita kula dadi ne da ita , idan har suka kamanta ta tabata za'a ji dadin hakan domin iyayen na TAUFEEK masu karamci ne, sosai ta yiwa mijinta godiya da fatan alkhairi, ita ta san auren namiji mai zuciya ya fi wani mai kudin, domin mijinta Allah ya masa zuciyar nema da kuma sannin ya kamata, mutun mai matukar jajircewa a kan iyalansa, azumin nan aka yi aka gama bai taba fashin yawon kasuwa ba, kuma a kadan yana shigowa da ribar dubu takwas in kasuwa ta yi mugun dadi har sama da haka, in kuwa kasuwa ta cije wani sa'in har kasa da biyar, a haka yake cire yan bukatunsu na su yan fruits haka ko kifi haka sauran kuwa ya juye a asusun da ta tabata yanzu kam ya yi nauyi sosai, kuma a haka ya cire na hidimtawa yaron da yake hidimtawa y'arsa, lalle zata iya cewa ita kam ta dace duniya da kiyama tana fatan ƴaƴanta su samu mazaje masu fahimta da fita hakin iyali

Bayan ya tafi ta samu su KAUSAR din a daki ta bata kudaden da suka sakata ihun murna da farin ciki, zuciyarta cike da kauna da tausayin mahaifinta, a duniya tana fatan Allah ya bata aikin da zata talafi mahaifinsu da mahaifiyarsu da shi, iyayenta sunne iyaye talakawa masu zuciyar fita hakin ya'yan da bata taba gani ba a duniya, tana sonsu tana tausaya masu tana taya su kula da tarbiyarta kuma ta yi alkawarin in sha Allah ba zata kasance daya daga cikin ya'yan dake jazawa iyayensu azabar ubangiji ta hanyar yada badala a doron kasa ba....nan fa suka shiga tunane tunane da neman abinda ya dace ta ba TAUFEEK matsayin gift, su ce wannan su ce wancen, har dai kansu ya kule suka rasa mafita, sun tsaya a tsakanin biyu, agogo ko Turare....sai dai shima sun fadi ne dan jin dadi dan kuwa ita ta san a turarukan TAUFEEK da wahala in yanada na kasa da dubu talatin , hakama agogon hannayensa bama zata iya kidaya kudinsu ba dan ta tabata masu tsadar gaske ne, maganar suka ajiye kan zasu bincika wajen kawayensu yan gayu su ji sunnayen turaruka sai su zabo na daidai kudin

Wannan kennan
___________________________________

Kwana biyu tsakani KAUSAR da A'isha suka shirya suka je gidan aminiyar Aishan, dan ta nacewa yayarta cewa dan Allah ta zo su je dan matar ta iya mak'up tana so su dauki ranar da zata masu domin aure dai yau saura kwana takwas cif, anko dinsu kansu daya ne kawai basu amsa ba

Da kyar suka samu gidan, domin ta jima rabonta da ita, sunna dai haduwa a school lokaci zuwa lokaci dan ita Usainar yanzu ta fi ba harkar kwaliyarta karfi babar mai harkar mak'up ce a garin

Sun samu tarba ta mutunci, sun kuma taki Sa'a ranar hutunta ce bata kwaliya dan haka suka zauna suka shiga fira

KAUSAR kam da hankali du ya dauku a irin sansanyan kanshin da falon matar ke yi na turaran wuta ta gaza hakuri ta ce" Kai Usaina ama dakin nan naki na kanshi mai dadi walahi, haka nake son kanshi mai sanyi da ratsa zuciya"

Murmushi Usaina ta yi tana fadin" Lah aunty ki ce kanshin akoyshi har yanzu? Kin kuwa san tun jiya da dare da na turarawa dakin ban turara yau ba, sai da yama nake son turarawa, ai matar nan ta iya hada turare na kasa da kasa, haka na fesawar da kuma humurar akoy wace sai ta yi sati a jikin tufafi kanshin na nan radau, ai baban Abdul baya hanna kudi in dai turaran HAJIA FUSAM za'a siya"

Aisha dake murmushin itama tana amsar wanda ta mikowa KAUSAR ta sinsina sai lumshe ido take yi itama ta sinsina ta ce" Kai, ama kawa wannan da tsada ko? Na san wannan in zaka shiga sia ka shirya"

Usaina ta sake mikewa ta dauko mata turarukan ta ce" Ke kuw kawata, abu mai kyau ai shi ke siyar da kansa, tsada kuma ai karkon kennan, balema har ga Allah kayanta ba tsada, ga kyautatawa, kw harda gift take sako maka bayan na kudinka fa, kin ga wannan gift din ne , in takarkare maki kin ga dai baban abdul babban mutun ne ko? To walahi turaranta ne yake aiki da shi yanzu, cewa yake yi ko irin wunin office ya kama shi in ya je sake alwallah haka zai ji kanshin na tashi a ruwan, ke abokiyar zamana tun tana jin haushin hakan har ta hakura , nan fa yake amsar turaran wutar wai in zai kwana wajenta ya je da shi, ke dai har abu ya isheta ta nemi Hajia FUSAM itama ta shige, ni yanzu a gidan nan kin ga harta maina a wajenta nake siya da sabulu nawa da na yaranki, kin san kuwa ai kyau ya sa na nace"

Itama Aisha yanzun dariya ta yi dole dan yadfa Usaina ta yi, sai take ji a zuciyarta kai dolema ta samu mu'amala da matar ko dan ta dan gyagyara masu harka, ah to magana ta kanshi da gyara wa ya ki? Bale ance da sauki ai kawai zata gwada sa'arta, tana shirin tambaytar numbar natar KAUSAR dake ta faman sinsinar na ruwan dake hannunta ta ce" Usaina kuma a ina take? Ina so, ni kam tunda kin ce harda na maza ina son na mazan"

Usaina ta ce" Aunty yar Nijar ce ai, yanzu haka dai tana damagaran kuma ba inda bata aika sako, ga numbartama +227 97 82 44 94 , sunnanta kuwa shine HAJIA FUSAM"

Numbar suka kwafa sunna jin farin cikin hakan, dan kuwa irin yadda turaran ke gyare a daure da wata fulawa mai kyau ta tabata a kanti ba zasu samu irinsa ba, dan kuwa hadawa ne take yi da tsararun nagartatun turarukanta su bata kanshi mai ma'ana da sace zuciya...., Sai daga baya nema suka tsayar da lokacin kwaliyar, ita da kanta ta ce su zo karfe goma ta masu kafin dai a dawo daga daurin aure in sha Allah

Sun dan jima a gidanta kafin suke yi mata salama,
Har sun kusa fita ta biyo su da sako leda baka ta mikawa KAUSAR tana murmushi ta ce" Aunty ga wannan, kin ga yannayin fatarmu kusan daya ce mu ba baki ba mu ba haske bau ba, ki ringa shafawa fuskar kafin ranar kwaliyar, na tabata sai kin siya da kanki a wajen hajia FUSAM"

Godiya sukai mata sosai
Wannan shine mafarin shirye shiryen auren TAUFEEK

Tunda satin auren ya kama kuwa ya zamto babu mai lokacin kansa, duka bangaren biyu cikin shige da ficen shirye shirye suke, harta Kausar ba'a barta a baya ba domin bata zauna ba ta yi nan ta yi nan, ga wani abinda ya faranta mata rai
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 1️⃣1️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃

Ga wani abinda ya faranta mata rai shine sakon kyautar da zata yiwa Taufeek, gefe guda kuwa Elhaji ya zo kuma ta mayar masa da kudin ama abin mamaki sai ya je ya duka da kansa gaban Mama yace da ita kudin nan ba rokarsa ta yi ba, haka kuma yana iya ba wanima a titi bale wace yake neman aure, da kyar Mama ta amshi kudin, shima dan ya bata kunya sosai irin yadda ya duka din, duda ta san ta girme shi sosai domin dan yanada mata da ya'ya ba wani baba bane, kawai kudi ne suka kwonta ya tara mata abinsa, su kuwa suke gasar haihuwa kamar yadda aka saba
Chapter 18 · 0% Book details