← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 116

Sashe 44

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makociyar Mama da suke abin arziki sosai ta tareta tana fadin" Eh mu iyayenta ne, da komaima, babu abinda zai saka ki cire mata hijab a banza a wofi, mema ta maki ne yarinyar da ba komai take cewa ba? Shekarunta nawa a anguwar nan bata taba yi da kowa ba, haka a makaranta da tana yi da koda sau daya ne an sani, to koma menene ba zaki ci mata zarafi a gaban kartin maza ba, ku kuwa su Isuhu kunna tsaitsaye me kuke jira ku gama gani kafin ku tsawatar ku hanna a zo har anguwa a wulakanta yar gidan mamuda? Ai kam ba adalci a lamarinku dan na tabata da shine walahi sai inda karfinsa ya kare!"

Sai da ta yi wannan maganar ne kuma samarin suka shiga hargowar rabiyar fadan da yannayi irin na dabacin nan sunna nuna ko ta bari ko su far mata, tuni aka samu aka sake matsa Khausar hanyar gida, da lalube ta juya tana son bude gidan ta shige ta ga mahaifiyarta ta ja kofar ta fito domin ta kasa hakuri zuciyarta sai harbawa take cike da tsoron menene wannan din kuma

Da wani yannayi na yan daba matar nan ta karewa makociyar mama kallo a lokacin da Mamanma ta fito ta ce" Mama, kina jina? Zamu tafi, ama ba hakan na nufin zan kyale yarki bane innhar bata fita daga harkar wancen mutumen ba, da kika ganshi a cen mijina ne, a yanzu dai a gidansa nice ta uku, a cikinmu duka haka kirarmu take dan yana sin manyan mata, Mama nima mun hadu a yawon ta zubar da shi ne ya aureni , ya bamu gida ya bani mota, wannan fa zan iya ce maki zaku samu , sai dai in zaku iya jure hali irin nasa da kuma nawa, dan na rantse maki har saman gadonta yana iya kawo mace ya warwareta sala sala bale idan ya rainata, wulakanci kala kala da gori zata ringa gani a rayuwa dan baya auren yayan masu kudi sai ya nemi yayan talakawa ya wankesu tsaf ya amshi yar ko me ta je ta fada a gida sai dai a bata hakuri a dawo da ita, ga kuma nawa a gefe, dan da kika ganni a nan mama abin kunya ne a cikin kawaye ace wancen ba wada haushin ya karro min wata, babu abinda na rasa shima ya sani, in bama masifa ba shi fa halitar da zai gamsar da matan irinmuma bashi da ita ama haka yake aurowa ya halaka a gida, ai na fada maka ni da kai shege ka fasa Walahi sau dubu zaka hau mace sai na samu jikeken Kato mai sunna kato na kawar da ƙishirwa haka kuma mun riga mun zamewa junna karfen kafa dan ba kari ko uban wa ya yi maka tsaye nice nan na fada, in kuma kun yi gardama ku aura masa ita , ke ki yarda ki aure shi ki zo ki sameni ina nan ina jiranki dan sai na.........".........................

........

Kalaman da kunnayenta suka iya ji kennan ta samu ta karasa dakin Aba da gudu ta zube nan saman kujera ta rufe kanta da hijabinta tana rizgar kuka tamkar kanta zai rabe biyu

Wasa wasa Mama ta dauki minti talatin kafin take shigowa, ko tace take shigowa tare da Aba, wanda idannuwansa suka gama kadewa suka yi jajajir har hada hanya yake yi wajen karasawa inda Khausar din ke kwonce

Murya a tausashe bayan ya zauna ya ce" Kuka kike yi tun dazu? So kike yi ki hadawa kanki ciwo ne? Tashi mana autana, ya isa hakanan"

Tunda ta ji muryarsa a farko kukan ya tsaya , tana jin me ya fada ta fashe da wani kukan mai karfin gaske ta dago fuskarta da ta yi jajajir gashin idonta ya hade ya yi wani irin luhu luhu da shi ta zubawa Baba idon tana girgiza kai a raunane ta sake mayar da kanta ta dukunkune a cikin hijabinta cike da jin kunyar baban da kuma tarin kunyar kalaman da matar nan ta ringa fada a gaban su Mama wa'inda ita dai a kankin kanta tunda Allah ya haliceta babu inda ta tsaya ta ji kalamai mararsa da'a irin wadinnan, sam bata tare da mutane masu gurguwar yare, haka a anguwa bata shige shigen yaren mata masu sakin harshe sunna maganar mazajensu a bayane ba dan raha ba, shi yasa abin ya wani irin daketa ta kasa kallon kowa a dakin

Auta ne ya karasa ya zauna yana kama hijabin nata ya ce" Aunty, kin ga kuwa yadda aka musu? Aba fa ya je har gidan da ni yace to kar ya kuma gannin kafar kowa a gidanmu, in fada maki harda shi uncle din Aba yace ya rabaku kar ya kuma ji, kuma sai ki ringa yin kuka? Tunda Mama ta yi kiran Aba muka fito daga kasuwa muka zo fa"

A birkice ta dago, ta dubi Aba, har lebenta na rawa rawa ta ce" Aba, kar ya kuma zuwa? To wa zai aureni in bai zo ba Aba?"

Mama dake share hawaye a kofar dakin ta shigo kamar an sanyota ta zubawa Khausar ido
Muryarta a raunane ta ce" Ke? Kina da hankali kuwa?, Ko tunanin kin gaza samun mijin ya fara taba kwakwaluwarki ne? Kina nufin in akace ya zo ya aureki zaki iya yarda bayan duka kaf abinda kika gani kika kuma ji? Yau ba dan Allah ya sa ana mutunci da makota ba ai da sai sun gama wulakantaki tsaf sai dai ki mutu in mutuwa zaki yi dan kuwa da y'ar bariki ta hado ki fa Khausar!, Ke wai shekarunkima nawa ne? Ko hamsin ne da ke sai aka yi me? Ko mun mutu mun barki ke daya a gidan nan sai aka yi me? A kanmu farau ne? Ke ba yar bariki bace, ke ba mai wulakanta mazan bace, kadararki ce fa ta zo a haka kuma shikenan sai ki dauki ciwo mai tsanani ki sakawa zuciyarki? Khausar ina sane da halin da kike ciki na ki baki dama ne kar abin ya zama shirme ki kasa rike kanki a cikin gida, ama tunda haka ne ya isa haka, ya isa hakanan khausar, miji idan ya samu to in bai samu ba babu yadda zamu yi, abinda na sani daya ne tak shine idan kika wulakanta kanki ta hanyar bin maza kin cucemu kuma kin cuci kanki, ki ci gaba da kula da mutuncin kanki da namu har yadda Allah ya yi!"

Daga haka Maman ta yi gaba ta barsu da binta da Kallo, Baba ne ya tausasa muryarsa ya yi mata nasiha sosai , kafin shima ya tashi ya fice masalaci

Da raunin zuciya da komai ta karasa wajen salaya ta samu ta yi sallah sannan ta kwonta a nan har dare ya fara yi

Kiran da wayarta ke yi ya sakata laluba ido har yana rufe mata dan abinda ke ranta ta daga bayan ta ga sunnan mai kiran ta yi masa salama a sanyayen da yannayinta yake

Kasancewarsa mutun daya kwalin kwal dake saurin cenkar yannayinta, hakan ce ta kasance yanzunma, harma kamar ya mike ya fice daga cikin mutane ne ko menene muryarsa a tausashe ya ce" Me yake damunki? Dazu ance baki je aiki ba baki da lafiya, wht hpn?" Ya karashe hapn din yana gagawar dakatar da nurse din da ta shigo da nufin yin magana kan list din wani magani da aka rubuta za'a ba wani patient a asibitin, domin du a rikice suke tunda ya masu dirar ba zata sai guje guje suke dan kar ya kama su da wani laifin domin ya samu abinda ba daidai ba yana cikin fadan ne ya ce da su ohk tunda haka ne da shi suke maganar, kuma sun san me hakan ke nufi shine fa du suka rikice yana office din docter Ibrahim sunna maganar abinda yake faruwa a asibitin ne ya danna mata kira

Rabewa Nurse din ta yi kanta a kasa , shi kuwa ya saurara yana son jin amsa daga Khausar

A hankali ya furta" Khausar? Ko kin yi barci ne?"

Khausar ta lumshe idannuwanta, a hankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin gurbin idannuwanta, muryarta a shake ta ce" Aa, ban yi ba"

"Kuka kike yi ne? " Ya fada a sanyayen da ya saka nurse din nan da mahaukacin mamaki satar kallonsa, domin tunda take bata taba jin dai ya yi doguwar fira da su ba in ba shafar aiki ya yi ba, ama kuma in ya kamaka da laifi a kan marar lafiya yadda ka san zai cinyeka danye haka yake damkarka, a ranta ta ayana' ta yiwu da Hajia yake' watau Mama, dan kuwa du duniya ita kadai ce suka san ko asibitin ta zo idan zai mata magana to fa a sanyaye muryarsa take, dan kuwa hajia kakarsa su caku be tace ba'a yi yace sai an yi, matarsa kuwa basu taba ganninta ba, basu san yaya mu'amalarsu take ba

"Rashin lafiyar ne yau ake yiwa kuka? Yayama aka yi baki da lafiya ama baki sanar min ba? Kin sha magani ne????" Ya sake fada a hankali sosai a kuma sanyaye sai dai kuma abin auna zafin zazabin jikin marar lafiya dake hannunsa ya masa riko mai karfin dake nunin da shiru shirun da yake yi ta yiwu wani abin ya hanna shi fido ainahin abinda ke ransa a irin wannan lokacin

" TAUFEEK, Mujaheed ne....." Sai kawai ta saki kukanta a raunane har tana dan dafe gaban kirjinta dake mata zafi.....dan sai ta ji inma bata fadawa TAUFEEK ba ai an gama cutarta, dole ya san damuwarta dan bata da amini abokin sirri sama da shi

A hankali ya lumshe idannuwansa da suke karra girmama bacin ransa, a saman lebensa ya maimaita sunnan yana hangen Mujaheed din a idannuwansa
Chapter 44 · 0% Book details