← Book details Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 116

Sashe 5

Da Ciwo A Zuciyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallar isha'i da kamar minti talatin da daya ta fito tana rufe gifan dan zuwa ta kamo Auta, domin ya cika dare haka a waje dan kawai ana taron nan ne da ba haka ba da tuni yana gida sallah kawai yake fita , gashi mamansa bata nan , hakama Babansa gwara ta kamo shi ya dawo gida ya ci abinci ya kwonta ko dan islamiyar safe

Dakatawa ta yi ta zubawa galeliyar motar dake parker gaban gidan kadan ido

Gane mai motar ya sakata sake bude gidan ta shige, shi kuwa daga zaunen da yake sake zubawa kofar ido ya yi a hankali ya shiga dan lumshe idannuwansa dan maganar sai ta so zame masa biyu a cikin kwonyarsa dan kuwa budurwarsa na magana ne ta wayar da ta yi kiransa da kuma tunanin me nufin komawar aminiyarsa cikin gida bayan ya tabbata ta san motar nan?

Jim kadan ta fito tana sake kulle gidan ta karaso hankali kwonce ta bude gaban motar gefen da ba kowa ta shiga ta zauna ta mika hannunta ta dan matso kofar dan a bakin hanya ne ga anguwarsa da yan acaba

......ba komai ya saka ta shiga motarsa ba sai dan ta fada masa abinda ta kulo a zuciyarta!
Tarin abinda zata juye masa ne a zuciyarta!
Kuma ta rantse sai ta fadawa Taufik duka kaf abinda ta shaka

Kasa kasa sosai Taufik dake kallon wayarsa da ta ajiye gaban motar ya ce" Zan yi kiranki *YUMNAH*"

YUMNAH dake son sannin wai yaushe zai karaso gidansu ta ce" To shikenan, ama baka fada min karfe nawa zaka karaso ba?"

Agogon ya dan kalla, sai kuma kasa kasa ya ce" Zan dai taboki"
Wannan karron bai tsaya ta bashi amsa ba ya katse kiran sannan ya juyo yana dan sake rage girman idannuwansa dan ya ga ta gyara zama ta cika fuska tamkar zata fashe ya bata hankalinsa

A takaice dai kamar yadda ta saba ne idan ta kwaso masifa sai ta zo juyewa ta rasa ta inda zata fara da kowama hakan ne yanzuma yake neman samunta

Da kyar, da kyar ta iya sake cije lebenta sannan ta saka hannunta zata bude motar ta fice

Da sauri ya ce" KAUSAR "

Dakatawa ta yi ta juyo da wani tuwon takaicin mai hadasa ciwon kai ta sake zuba masa idannuwanta tana sauraronsa

Kai ya dan sinne kasa kasa ya ce" Sorry besty "

Rai bace ta ce" Taufik, ka rike sorry dinka, nace ka rike Sorry dinka Taufik, bari ka ji in dai ni yar halak ce an haifeni a hanyar halaci ba zan kuma........................."

Idon da ya tsura mata da wani irin kallo mai kama da kashedi ya saka ta shiga wani inda inda kamar tana gaban Aba, har sai da ta tuna irin haushin da ya shaka mata sannan ta jure ta yi watsi da wani wasi wasin tunani ta ce" Ba zan kuma yi maka magana a kan harkar karatun nan naka ba, ai da ake fada min nice nale rintse ido dan tunanina na isa ko ina iya gyarawa ne? Ban san cewa nice nake lalube kai karatu ya maka rana ko kar ya yi kansa ne, sai dai na kasa gane a kan me ka zabi zama likita bayan ka san shine aiki mafi hatsari a duniya, domin da allura daya kana iya kashe bawa, na san kana da ilimi, hakan ba yana nufin kai aljani bane, likitanci ba'a cenkarsa sai dai a karanta du ilimin mutun!, Ka ki ka gane ko ka ki ka mayar da hankali zan ce? Duka wannan yanzun kam babu ruwana ka yi yadda kake so Taufik, ka ga tafiata"

Watau da ake cewa babu abinda ya fi ciwo a duniya irin ka shako fadanka ka rikoshi da hannu bibiyu irin na rashin mutuncin nan, ka zo dan ka juye shi a kan mai rabo ama ka yi ka yi a maka shiru hakane, watau a ki biye maka hakane, yau ta karra yarda da maganar

Du wannan babatun da ta yiwa Taufik, duka kaf wannan fadan da ta saukewa TAUFEEK ita TAUFEEK ya karewa kallo ya mata banza tamkar wata shashasha wace bata san ciwon kanta ba? Ita TAUFEEK ya kyale ta ringa hayaniya kamar zata ari baki? Lallema!

Da bacin rai ta maki masa marfin motar , tana juyowa ta ga Auta a tsaye yana bangalar baki shi da abokinsa har yana dage ya ce" Auntynmu, yayanmu ne a motar?"

Wani takaici ya kuleta, wai ƴaƴansu, to yau du wani mai kiran TAUFEEK yaya dan yana dan uwanta ta soke!, Da bacin rai ta janyo shi ta ingiza keyarshi gaba bata bashi amsa ba suka karasa kofar gidan ta saka dan makulin ta bude suka shige ko gaishe da Malan Barau bata yi ba domin ya wani kura mata ido har lekawa yake yi motar da ta fito, ta tabata yau sai an dora dandalinta a anguwar

Ajiyar zuciya ya sauke ya sake duban wayarsa dake haskawa

Bai daga ba kawai ya tayar da motar ya juya ya nufi gidansu, dan ba zai je wajen abokanan nasa ba, haka kawai yake ji idan ya je yana iya sauke fushin da ba nasu ba a kansu

Mikewa malam Barau ya yi yana lekawa kafin ua juyo yana kama haba ya gyada kai ya ce" Ikon Allah, ni ban taba gannin gida irin na bawan Allahn cen ba, ka ga fa malan Saidu sai ya je ya dawo daga kasuwa da ledoji na kayan kwalam da makulashe ya shige ciki ya sake tirke kartin yan matan cen ya ciyar ya yi barci harda minshari safiya na yi ka ganshi kalau abinsa....., To ni Allah na tuba ko daya na girke irin ya'yansa ai ba ni ba rintsa ido kalau kamar wanda bani da damuwa a duniya, ba zan taba iya rintsa idannuwana ba dan ya'ya mata ai fitina ne, ka ga du sun kamo shi a tsayi biyu jikaka biyu mudil mudil ama baya ko yar suman nan ta badi? A gaban idannuwansa a shiga a fita ana rawar nanaye wai yan mata ne? Ka ga yanzun itama wace ake cewa bakin aljani ne ya sa bata da mashinshina ta fara shiga motocin karti!"

Malan Agali ya zubo shayi ya juyo yama miko masa ya ce" Kai wani bakin aljani, malan ai wannan y'a ta Malan Saidu garke ce ciyar da ita sai makiyayi, sau nawa ana kwatanta tunkararta sai ace tsoronta ake ji?, Wannan y'a da ka gani ina fatan gannin namijin da zai dauka, kuma motar cen da kake gani inaga ta wannan elhajin ce da yake shiga gidan nasu, ni na rasa a ina suka samo shi, mutun mai kudi yana shiga gidan motar cen tasa ce ni na santa"

Na Awa ya fyace abin raken dake bakinsa ya fuskanci Barau da Agali ya ce" Ni ka ga da za'a bani y'ar nan, tsaf zan aura, Allah na tuba Malan Saiduma ya iya da mace irinta bale ni? Kai dai abu daya nake tsoro da shi da ka ganshi a nan lange lange sai masifar karfi, bana son na shiga lamrinsa ya kwasheni ya watsar a anguwa da yan jikoki da sirikai fita ta gagareni, dan tsaf tasalah zata ajiye min dandali a bayan layi ta tsigeni , ita har yanzu bata hakura da ni ba ni kuwa na gama aure da kazama, tasalah fa ko jini ta gama bata wankan kirki sai shafe wai yawan zubawa fata ruwa na raurautar da ita, ji fa masifa?......."
Hakane, wannan zamani ya zo mana da abin mamaki, maza sun dauri aniyar yiwa mata shiga hanci da kudundune harta dan tsegumin da ake kira na mata nema suke su mana fin karfi, kiri kiri yanzun idan namiji ya dara biyu basa jajen nema da turbisa sai su aro kalabi su yafa su nemi yin shige cikin shingen nazaru.....zamani kennan babu ruwanka da wani ama kana fama da tunaninsa.... Allah shi kyauta

TAUFEEK direct gidansu ya nufa, Baban gidan fitacen dan kasuwa nagartacen mutun mai kyauta da kari, mutun mai sadaka da tausayin talakawa, wanda aka fi yiwa lakabi da *MAI KWANONI*

Kasancewar get din a bude sakamakon bakin da aka yi daga cikin gari na mahaifinsa ya sa ya bi bayan motocinsu kafin ya yi baya ya ganganra cen gefen da ake ajiye motocin gidan ya dakatar da motar a hankali ya kashe ya sake duban wayarsa da yanzunma ake kiransa kiran kuwa ya tabata idan har ya yarda ya shige bangarensa ba tare da ya daga ba yanzu zai ga wace ta isa da shi ta tardo shi ta kuma wanke shi soso da sabulu, a dole ya juya baya ya dauko ledar kilishinta da kuma embulop ta maganinta da ya siyo sannan ya rufe motar bai ko dauki wayar ta wajen KAUSAR da ta dawo masa da abinsa ba

A nutse ya nufi bangaren Matan gidan, watau matan Elhaji
💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

*DA CIWO A ZUCIYATA*

💔💔💔💔❤‍🩹❤‍🩹💔💔💔💔

_MALLAKIN_

*SAJIDA NIJAR*

*FREE BOOK NE* 4️⃣

LITATAFAN MARUBUCIYAR

Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak'a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar

Now

*Da CIWO A ZUCIYATA*

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
Chapter 5 · 0% Book details