← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 117

Sashe 99

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karra bude bakin ta yi, da niyar sake dandana masa azabar da ta dandana masa yanzun nan, a yanzu kam lokaci daya ya ja tunga da ita a rike a hannunsa ya sake kama hannayenta ya cirata ya nufi dakinta da ita

Ihu take yi a yanzu, dan tun dazu bakinta a jimke yake, tana harba kaffafuwa tana ihun ya sauketa, ama ya kiya sai da ya kaita dakin ya karasa wajen gadonta ya dagata ya timata a saman gadon

A zabure ta mike ya kuma daukanta ya timata a saman gadon yana sake kallon y'ar nan da wani balagagen fitina dake sake tsimkota niyarta kuma mikewa, dan wani tsohon neman isgili idonta idonsa ta ce" Ka barni, ka barni sai na zaneta walahi!'

Ido ya sake zarrowa yana kallonta ya ce" Ke to y'arki ce da zaki zane ta?"

Ido ta zuba masa tana mamakin yadda daukanta baya ce masa komai, ta dafa ta zauna tana furta" Wash Allahna bayana, yanzu tarayya zaku min kai da matarka ku karya Ni?"

Shima idon ya zuba mata, irin yadda ta marairaice muryarta tana nuna masa zasu mata tarayar sai ya rasa irin kallon da zai yi mata,......gaba daya ta yi kamani da kyakkyawar fulawa mai kyan kallo, a hankali ya ce" Ki ji tsoron Allah RAUDA, me ta maki ne?"

Kai ta cire daga dubansa tana mikewa tsaye gaba daya, hakan ya sa ya yi saurin tsayawa a kan hanyar

kirjinsa ta bi da kallo yadda ya yi mata kikam, kuma ta san ko a kashe sai ya kasheta ya birne babu wanda zai sani, hakan ya sa ta ja baya ta bude murya rai bace ta ce" Allah ya isana Ni da ita, kai kuma ba'a yi dacen mace ba, na zata zan ga wata zukekiyar mace a gabana ne, sai na ga wancen abar, kuma walahi haduwa koma fitar da raini goma tunda ta raina min iyaye, ita ta isa ta zagar min uwa? ita din banza? duk wanda ya yarda ya zagar min ita sai inda karfina ya kare, aikin banza,, na rantse idan na kuma ganninta sai na kumbura mata fuska!"

"Ke zo nan, zo nan!" YUSUF ya fada yana sake zarro ido da kallon bakon balaki yau shi Yusufa jikan Muntari, duk inda yayi tunaninta ta wuce nan ashe? kuma idonsa idonta tana cewa wai za'a yi mata taraya

Baki ta turo ta shige bayin da sauri ta rufo tana sake tunzuro bakinta a ranta ta ayana' Ba zan zo ba, kuma yau Ni da ita shege ka fasa, aikin banza mai kama da munafukai!'

Ya jima a tsaye, ya rasa abinda zai yi, kofar bayin yake kallo , a ransa yana tunanin ya bani yanzun yaya zai yi da wannan fitinar?, da kyar ya juya daga dakin yana tuna maganar Hajia ta dazu da take fadin yarinya saliha da ita bata cewa komai sai ido idan aka yiwa jikarta wani abin ba zata kyale kowa ba......

A bayane ya furta" Hum!" Bayan ya fito ya yi tsaye ya ga ba Amnah ba labarinta

A nutse ya nufi dakinta, dan ba zai je ya kwonta haka ba kar aje wancen rigimamiyar ta yi mata ilar da ake iya yi mata shari, dan haka ya je ya kama kofar ya murda ya shiga

a hankali ya dakata yana kallonta ta baya yadda take tsaye tim da ita bata da komai a jikinta tana waya da mahaifiyarta tana sheka kuka da zayane abinda ya faru

Idannuwansa ya dauke daga kanta ya juya ya fice a dakin ya ja ya rufe a hankali ya nufi kujerar nan baba ya zauna ya shiga yamutsa gashin kansa kirjinsa na neman cenza masa yannayi

Dan murmushi ya yi a hankali yana girgiza kansa...., a ransa yana tunanin ai ba laifi an jima ba'a sadu ba, idan yanzu an ji dan alamun bukatar hakan normal ne, sai dai koda shi maye ne wannan naman ba abincin cinsa bane, bai taba tsana da kyankyamin nama ba sai a kan wannan, tabas a kan wannan naman ya gane ashe shima yana da haram a duniyar nama

Murmushi ya sake yi ya mike ya nufi dakinsa,, dan wanka yake so ya fara yi kafin komai, ga yinwa yana ji, ga gajiya kuma ta kokowar nan da ya karra

yakan yi murmushi ne kawai ya fitar da sautin Hummmmmmmmmmmmmm, shi da kansa ya gama yarda cewar kamar kumbo kamar kayansa ne

Da sassafe kusan karfe bakwai daga daga masalaci ya wuce bangaren Hajia, ya sameta a falo zaune tana ta fama da turaran wuta a cikin hijabinta ko tsoron ya kama mata hijab bata ji

Zaunawa yayi yana shan kanshinsa da yake yi mata kwana biyun nan, ita kuwa sai faman masa sannu take da gaishe shi kamar shine baban ba ita ba

Ciki ciki ya ce" Abinci nake so"

Hajia ya zuba masa ido tana kallonsa, abinci kuma? ita batama san me zai fito da bawan Allahn nan ba da safiyar nan ya zo wajenta bayan ga y'ar mutane cen an kai masa

Baki ta dan tabe ta mike da kyar tana fadin" To bari in ha ko sun gama girkin, ama kuma na zata ko ka yi hakuri a kai maku cen din kar ka ci ka bar baiwar Allah marainiyar Allah, gashi ka barota ita kadai kar aje wannan fitinaniyar matar taka ta tarda min ita ta yi mata wani abin, dan Ni walahi Amnar nan tsoro take bani"

Har ga Allah sai da ya kalli Hajia bai shirya ba, kafin ya saki murmushin da bai shirya ba yana gyada kai hadi da dan cije lebensa ya mata shiru

Hajia ta kauda kai a ranta tana ayana' Oh, d'an nan sai ya ringa wani abu kamar wanda ke dauke da wasu halittun bayan bil'adama, bari a hada a kai maku cen din dan ba zan so ka jima a nan yau yau ba ake ta tarda baiwar Allah ta yi mata wata ilar ba!'

Yana nan zaune dogari baba ya karaso ya yi salama sannan ya tsaya yana jira a bashi damar shigowa

Jakadiya ya sanarwa Hajia wanda ke salamar hakan ya sa Hajia zuwa falon ya bada damar a shigo da shi

Shigowa ya yi ya zube kasa kansa kasa ya shiga kirari gannin YUSUF din a falon, har sai da ya dakatar da shi sannan ya yi shiru kansa a kasa ya ce" Allah ya taimaki kakar saraki, dangane da dokar da kika dora ne jiya cewar gabanan kar a ringa shigowa yadda aka so dan ana takamar an shafi gidan nan dan ana aure a gidan, to tun jiya kusan karfe daya na dare baki suka zo muka hanna shiga, da kyar suka koma sun ce ne wai iyayen Mai baban daki ce wato gimbiya ta farko, to yau ma sun dawo tunda duku duku sunna kofa mutane hudu ne da mata uku da wani akace mahaifinta ne, wai ance bata da lafiya ne sunna son shigowa shine nace bari dai na sanar maki kar mu hanna su shigowar aje abin mai mahinmanci ne"

Hajia ta kalle shi da kula ta ce" Wai kanana nufin iyayen Amnah?"

Ya karra sada kansa yana mai tabatar mata su din ne

Hajia ta rafka salati tana tafa hannu ta ce" Yau na ga balaki, uban me kuma ya dawo da mutanen nan gidan nan yau? Yau na ga dangin mahaukata haka zata yi zaman auren? a'a fa, ba sai yiwu ba, a kira min Jakadiya a je da baba baba a hadata a kai masu ita, idan sun shirya barinta yin zaman aure sa dawo da ita ta yi zaman aure!, ba zai yiwu ba, a kirawo min duk wani mai isan isa a gidan nan, bata isa ba walahi, kuma duk isar iyayenta basu isa ba , ba dai a fadar TSATSUNBURUM ba!"

Ta karashe ranta bace hadi da daga muryarta, da sauri ya mike bayan ya bayar da hakuri ya fice a falon ita kuma ta zauna ranta na tafasa tana kada kafa

Da ido yake kallonta, yana mamakin rikici irin nata, tsofai tsofafi sai iya daga murya bata ko jin wahalar ihu idan ranta ya bace

Dan murmushi ya yi ya sake gyara zamansa a nutse ya ce" Ta yiwu fa da gaskiyar zuwansu fa"

Hajia ta lalle shi da sauri ta ce" wace gaskiyar zuwansu kake fadi ranka shi dade?, wace gaskiyar zuwa? basu da dalilin da zasu nemi zuba min raini a nan, jiya fa ubanya ya zo nan da maganar dan mi za'a yi mata kishiya ko shekarewa bata yi a gidanta ba, walahi yana maganar idan ka kalle shi kamar mahaukaci, Ni kuma na tuna masa shima ai auren ya karra ba iya uwarta yake aure ba, kai dai abokinsa da suka zo tare ya koma yake bada hakuri da fadin dan Allah a yi hakuri shi bai san abinda ya kawo su kennan ba da ya hanna, Ni dai ban raha masu ba na masu sumul, me suke tunani , yau da ace wata y'ar a yi kwatance ce suka bamu sai ace masha ALLAH, ama y'ar da ita da banza shashasha duk daya, mtssssss Ni dai an bani abu a rufe ana ta cutata a banza a wofi!"

Murmushi ya sake yi a nutsensa ya ce" Kar ki ga laifinsa, y'arsa ce ai, kuma kin ga kar ki sa a kore su baki yi bincike ba, tam, dan kin ga salihar jikar nan taki? jiya zane min mata ta yi kamar ita ta haifeta!"

Hajia ta sake dubansa da kula da yannayin tashin hankali ta ce" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, Kana nufin jiya Amnah din ta dakar min RAUDA?"

Sai da ya karra yin murmushin nan da ya ki barin zuciyarsa ya gyara zama ya girgiza kai ya ce" A'a, ita dai baby din ce ya zanne Amnah"
Chapter 99 · 0% Book details