← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 117

Sashe 32

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa ta yi, a matsayinta Na mace, wace take uwa daya uba daya da uban wanda ake maganar , wace duk kunnuwa suka so jin bayanin ta dan an san idan akace YUSUF an ce ita, ta yi salama da mutuntawa sannan ta fara bayani kamar haka" Kwarai dukkan abinda aka fada a kan YUSUF hakane, sannan shi din da kansa baya son mulkin dan ya san bai tashi barin aiyukan da yake aikatawa ba, duk wani wanda ya san ahalina ya san muna dauke da jarabawar da daidaiku ke cikin tsarewar ubangiji, YUSUF duk wata masifar lalacewa ta taru a kansa!"

A wajen wanda bai dubeta a zabure ba daidaiku ne da suka san kwanan zancen, Hajia kuwa zuciyarta nan take ta ringa sukanta da karfi da ya sa ta rike kujerar da take sama ta rintse idannuwanta tana rokon Allah ya sa a gama taron nan kar ta lalata masu dan har jikinta rawa ya dauka

Cikin wata murya da ta dauka Tata ta ce" Bayan shaye shaye har aure ya ki ya yi, kuma yana son sha'anin mata tamkar wanda zai bi daba!"

Rai bace SHAHEED ya zuba mata ido, haka RISLAN

Bata ki dakatawa ba ta ɗora da fadin" Da wannan nake rokon kar a bashi mulkin kasata, dan idan aka bashi bamu san yaya zata kaya ba, ga dan uwansa RISLAN, a wajen nan babu wanda bai san waye shi ba, yaro mai mutunci mai mutunta manyansa, ga addini, gashi yana da iyali, RISLAN shine ya cencenci zama sarkin kasata "

Da wani shakiyin murmushi Jabiru ya mike yana kallonta ido cikin ido ya ce" To ko ke kika aika sakon nan ne?, kina nufin kanki ya yi cushewar da zaki sako mana zancen banza a nan?, kina tunanin Muna raye zaki dauki sarauta?"
Irin yadda ya kare maganar yana zarro mata idannuwansa da daga mata murya sai da ta ji tamkar zata kifa a wajen, sai a yanzu wani abu ya ringa zuwa da dawowa a kanta, tana tunanin ta yi nasara ashe da sauran rina a kaba? Idan har sarauta ta fita daga hannunsu ita ta san sai ta fi kowa wulakanta a ahalin nan dan kuwa ta fi kowa tunkaho da gobara saboda sarautar nan

Mai maradi kam abin ya girmami tunaninsa, takaici ya gama rike masa zuciya, hankalinsa ya yi mummunan tashi kuma ya sani ne idan har aka yi abin son rai tabas za'a samu bacin rai a wajen nan

Asalin shugaban masu kare yancin talakawan ne ya mike yana son daidaita hargitsewar da wajen ke son yi, dan idan ka dauki magana ba'a katse ka sai ka isar da sakon ka, kuma idan ka kai kara ba'a bayana wa ya kai

Yana kokarin dakatar da maganar Sultan SHAHEED ya mike tsaye yana bin kowa da kallo

Daga yanda ya jimke sandar da ta zame masa ta sarauta zaka gane irin yadda ransa ya ɓaci

A nutse ya shiga nufo filin har ya karaso tsakiya, hakan ya sa daga jibirin har Nana yin baya sosai ciki banda shugaban masu kare yancin talakawan dan dukar da kansa ɗan sarakai basu fara magana ba, kuma yana da damar rarashi idan har rai ya ɓaci, dan haka a tausashe ya ce" Allah ya taimake ka, ka yi hakuri da shige cikin maganar da aka yi, in sha Allah ba za'a kuma ba"

A tausashe, sai dai kana jin furucin ka san rai a bace yake ya budi baki yana dubansa ta saman ido ya ce" yaushe muka yi zubewar da zaka tara mu, a gabanmu, ka zagi jinnin mu? Koda kuwa kana sanar da yadda aka kawo maka karra ne bamu cencenci darajantawa ba ko dan magabatanmu?"

A tausashe ya yi maganar, ya yita be har karshe, yana ajiyewa Sarkin bulala da karfi ya budi baki ya maimaita yana iza maganar ya ce" A gaban sarakan kasarka zaka zagi ɗan sarki, jikan sarki? Kai din baka da kara da girmama masu riko da ayar Allah ko zaka mana tutse cikin ganganci ne?"

Sarki SHAHEED ya dora da fadin" Yaya zaka ajiye mu, ka daidaita abinda bai isa rabar hanyar mu ba, dan kawai ana so a kawo darajarmu daidai da kowani dan Adam bayan Allah ne ya dora mana rawani ba wani ba?"

"Kai ja baya dan talakawa ka kai uban damagarawa kurya uwar daka, ja baya dan a yi kare jini biri jini da mu ba komai bane, rayukanmu muka miko dan yaki da gaskiya babu ruwan mu da takarda, kai ja baya dai auna tsayinka da wanda ya isa kuma wanda Allah ya nada !" Sarkin bulala ya sake wage muryarsa yana fada har kamar zai fasa wajen dan kaurin murya ne da shi sosai

Rai bace sarki SHAHEED ya juya wajen sarakan nan ya dukar da kansa sosai ya furta" Ku min afuwa, idan na yi laifi a hukuntani, ama idan har kuka yi shiru ina tsoron a kai ga taba darajarmu da mutuncinmu, dan idan mai turawar wawa ne mai zartarwar ba wawa bane, ana so a shigo Mu ne a boye dan a cin mana bamu gane ba? Ko rawaninmu ya yi hawan banzar da za'a sakani saukewa a bainar nasi? Innalilahi Wa ina ilaihi raj'une kalmar da take tabataciya, mudin raina har na koma gaban Ubangiji a yau ina da ja da raini da sabon salon wulakantarwa da ake son sako min dan a shigeni ta hanyar da bana so, idan kuwa sarauta karya ce na ajiye rawanina!"

Yana fada ya sake sada kansa ya shiga kunce rawaninsa, kuncewar da ta girgiza duk wani wanda yake wajen ta nemi daga masu hankali bilhaki

Da sauri YUSUF ya dago kansa yana gannin da gaske rawanin zai sauke? Idan har haka ta tabata an yanki yakin da har shi ba zai bari ba, a birkice ya bi ayarin wa'inda suka mike suka nufi sarki SHAHEED ciki harda shugaban masu kare yancin talakawa da sauran da suka zube kasa kawunansu a kas

Yana karasawa ya damki rawanin dan sai hakuri ake badawa ama fir zai rainawa mutane hankali

Da karfi ya matsi hannunsa a hankali ya ce" Kar ka soma!"

Bayanan da ake yi na bada hakuri wa YUSUF Sultan SHAHEED ya dauka shima a tausashe yana kallonsa ya shiga bashi hakurin, wanda hakan ya saka Mah sakin kukanta muryarta a boye

Rawaninsa ya maida masa yana dubansa, a lokacin ne Sarkin maradi ya budi baki bayan an dan sassauta rikicin ya ce" Tabas ana nufo mu da rikicin da gaba kadan mu ne zamu kai hari ba tare da an hau ko an sauko ba, ta yaya da ransa da lafiyarsa wani zai yi tunanin kai rawani wani gidan? Shin sarauta wasan yara ne? Ko an fada maku sarautarmu ta yanzu ba sai mai kokari ba? Idan nace kokari ina nufin wanda zai iya ciyar da talakawansa, dan mun jima da ɗaukan nauyin kasarmu ba tare da jiran sai an bamu ba!, waye zai rike a yanzu? Idan kunna da ja din ne har yanzu ku sai takobi ta yi aiki!"

Idannuwa YUSUF ya sake rintsewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une ta tabata fa, ya Salam zata tabata a kansa? Ya san za'a hau a fado ama bai yi tunanin zasu shigo da korafin ta sigar rainin da sarakai zasu ki dauka ba,

Yana ji yana gani aka ringa ba junna hakuri, aka ba zaben damar da za'a yi shi da mutuntawa ba tare da an kawo harka ta rashin da'a ba, zaben da YUSUF ya koma gefe yana bin duk wanda ya dangwala masa hannu matsayin shi ya zaba da kallon baka kyauta min ba, abin mamaki harta manyan malaman garin shi suka zaba wanda hakan ya bashi mamaki ainun, har dai magana ta tabata a kansa aka kuma maidoshi tsakiyar filin nan kansa na sarawa sarakan nan suka zagaye shi da Sarkin nadi kowa ya mike nadi ya tabata a kansa, nadin da ana nadawa masu dauka na dauka a vidios, masu dauka na gidan rediyo na yin nasu aikin summa, abu dai ya zo a lokacin da bawa bai jira ko tsamata ba, duniyar YUSUF ta yi girgizar da bawa ba zai gane komai ba, har aka gama aka fice aka bar shi da mutun uku kawai, Mahaifiyarsa wace ita dinma kaffafuwanta ke neman gaza daukanta, hawayenta kuwa har sun kafe, kakarsa wace ita dinma ta sha hawayen kuma ta gaza dauke dubanta a kansa, sai SHAHEED wanda ya tsaya ne saboda abinda yake son fara sanar masa a kan ISHAK, sai dai gannin halin da iyayensa ke ciki ya gaza masa wannan furuci karshema ya yi doguwar addu'a ya rike hannunsa sosai sannan ya masa alamun zasu yi waya shima ya fice tare da taron jama'arsa suka tafi

Sunna fita Hajia ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa, a sanyaye cike da girmama ta furta" Malik, a tsakanin sati guda zaka shirya komai na fadarka, ya dace ka yi dogon......"

"Hajia......" ya fada da wata irin murya mai cike da galabaita da kuma tarin gajia da rauni

Kai ta sada a hankali ta furta" Allah ya huci zuciyarka, bari na je cikin gida"

Daga haka ta matsa kujerar Tata ta juya da ita ta fice da ita daga falon bayinta suka rufa mata baya da tarin jama'ar dake waje, a nan ta sake zubawa RAUDA ido, wace ke zaune tun zuwansu da Mah aka hannata shiga bisa umarnin Hajiar, sai kuma ta dauke kai suka shige ciki

Kansa a kasa Mah ta saka hannunta mai dauke da dumi ta dago fuskarsa, a hankali ta sakar masa murmushi sai hawaye ya bale mata, tana kallon rigar da aka rufa masa ta alkyaba, da rawanin da aka naɗa masa da kanshin da aka fesa masa, a yau tana ganninsa da wani irin girma da daraja ne wanda bakinta ya kasa misaltawa, a raunane sosai ta ce"

...............AZAL😍😍😍😍😍

Azl 19

A raunane sosai Mah ta furta" MALIK!"
Chapter 32 · 0% Book details