← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 117

Sashe 54

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwansa da suka yi laushi ya daga a hankali yana tuna irin firar da suka yi da lauyansa a kan abinda ya shafi dukiyarsa, shi kam bayan na taimakon marayu, gine ginen gidajen marayu, su rijiya da masallatai a wajen da suka dace waye zai barawa dukiyarsa bayan ita?, to ai koda da ransa ita din ce bale idan ya tuna ta yiwu ya rigayeta barin duniyar? Allah shi ke dasa so a cikin zuciyar wanda ya so kuma abin al'ajabin kowa yana so baba da yaro

Wayarsa ya laluba da hannunsa na dama da kyar ya dauko ya shiga buga numbar Salima da adu'ar Allah ya sa ta dauka, dan dare ya yi ta yiwu ta yi barci

A irin lokacin ne RAUDA take kallo a wayar ta Salima dan rashin abin yi, gashi ta sha barci ya ki daukanta ga tunanin da ta dasawa gayar sodi dan bata ga abinda ya kai kare layin ragunnan laya ba!

Sunnan take kallo, haka kawai taji kamar hankalinta zai tashi duba da lokacin karfe biyu ya gota na dare

Da dan gagawa ta daga kiran, muryarta cen kasa ta yi salama lokaci daya tana fadin" Abdallah, lafiya baka yi barci ba har irin wannan lokacin?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da yannayin jinya ya ce " yaya zan iya yin barci Bayan zuciyata na neman fashewa dan ban kaita ta ganki ba?, Please ki bar dattijon saurayinki ya ganki noory"

"Mah ne tace sai na warke" Rauda ta fada a hankali

Ya buda idannuwansa shi dinma a hankali ya furta" idan na mutu fa kafin lokacin?"

Da sauri ta bude idannuwanta ta ce" Wai kana ina ne?, baka da lafiya ne?"

Da yannayin muryarsa mai rauni da abin ciwo ya furta" Alhamdulilah"

Idannuwanta ta lumshe, dan sarai ta san me amsar ke nufi, idan bashi da lafiya bai cika yi mata dala dala ba, yakan bi ta da alhamdulilah, tun bata gane ba har ta gane

A tausashe sosai ta ce" Ka kwonta da hankalinka,Abdallah tunda aka baka damar zuwa, na tabata aurenmu ba zai dauki lokaci mai tsayi ba, kuma kar ka damu in sha Allah gobe idan Mah ta dawo daga wajen Bah zan sanar mata, na san zata ce ka zo ne, zamu hadu gobe in sha Allah ka ji?"

Murmushi ya saki, harda sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da hirantarta , ita kuma ta bashi dukkan hankalinta har shi da kansa ya yi mata sai da safe sannan ya kashe kiran ta kwonta................

🤔🤔🤔🤔 Su waye yan team BALARABE SAK????????? KU ZO MU KAFTA
Azl 30
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Washe gari da safe Mah ta dawo, kana gannin fara'ar dake fuskarta ka san nutsuwarta ta dawo jikinta, sai da YUSUF ya isa asibitin aka dawo da ita
Tana zuwa jikin y'arta ta fara dubawa sannan ta wuce dakinta ta shige wanka
Sai da ta kimtsa jikinta sosai tana shirin fita dan neman abin kari RAUDA ta buga dakin ta shigo bayan ta bata dama ta ajiye kular dake hannunta da plate da cokali tana kallon Mah da murmushi itama a fuskarta ta furta" Barka da warhaka Mah, yaya jikin Bah?"

Mah ta saki murmushi ta karaso inda take tsaye ta kama hannunta suka zauna tana mata alamun ta zuba mata abincin ta ce" Bah din ku, yana lafiya alhamdulilah, ya yi hakuri sosai ya karbi kadararsa, ko yanzu sunna fira da YUSUF na baro su"

A lokacin da Mah ta furta sunnan YUSUF sai da RAUDA ta ji gabanta ya fadi, ama ta ture ta sakawa Mah cokalin tana murmushi ta ce" Allah ya karra masa lafiya da dangana, ya jikan sarki"

Amsawa Mah take yi, da kula, da wani yannayi na gaske wanda take ji Yawancin lokuta idan tana fira da YUSUF, dan haka ta dubi RAUDA bata son firar tasu ta katse ta ce" Ina Abdul? Ban ganshi ba tun dazu"

RAUDA ta yi murmushi ta ce" Salima ta yi bako shine ta ja shi dan ya rakata"

Mah ta yi murmushin itama tana kallon RAUDA ta ce" ki dan bani labarin soyayarku da Balarabe mana? Daughter kina son shi?"

RAUDA ta yi wani kiskirim dan har ga Allah tana ji a ranta da wahala ta iya wannan firar da Mah, kai, yaya zata iya yin irin maganar nan da Mah kuma?, maimakun ta bada amsa sai ta sunne kanta cike da jin kunya

Mah ta yi murmushi a tausashe ta ce" kar ki ringa sako kunya a zamantakewana da ke, Ni uwa nake a wajenki, kar ki yi tunanin zan dauke ki na ba wani aurenki ba tare da na tabatar da kina son sa ko akasin haka ba, dan Ni na san cewa auren soyayya duk rintsi ya fi auren da ba na soyaya ba dadi, domin kin ga shi zaman aure fa ba wai irin na kunna soyaya bane, zaman aure ibada ne RAUDA, duk macen dake zaune a gidanta komai kudin mijinta ko takaicinsa, komai addininsa da nata akoy ranakun da ake iya wayar gari da tashin hankali, rigingimu kala kala akoy su a cikin gidan aure, kuma da ba kiyaya ta sa ake haduwa da ire irin hakan ba, zama waje daya ne da yau da gobe wace ta fi karfin wasa, baby sai ki ga idan irin an hada auren nan ne motsi kadan ana kai kara ana yaji, rashin hakuri da junna zai yi mugun tasiri wajen gaza jin dadin zaman, shi namijin da halaya ta yau da gobe da kuma gannin hada shi aka yi, itama macen sai ta ga ai ba zata iya wani hakuri ba gaskiya, shine zaki ga wani gidan ko an hakura ana zaunen kulun cikin rigima ake, wanin kuwa rabuwa ake yi, wanin kuwa an hada din ama kuma idan soyaya ta shiga da yarda da junna zaki ga sun zauna kalau, duka aure dai ba kamar na soyaya, dan in yana son ki, zai ringa daga maki kafa wajen wasu abubuwan, ba fa ana nufin zaku zauna kulun ku cikin dariya ba, No, zai zamo ne koda halin a yi rigimar ta kama zai yi mai sauki, kuma idan ya yi fushi da ke zai sassauta maki da wuri ya yafe maki, haka kema zaki kasance mai yi masa uzuri, idan ya baki zaki yi da abinda ya baki ne, in babu zaki kasance mai talafawa ne da dukkan dabarar da Allah ya hore maki, in fushi ya haɗa ku da junna zaki kasance mai neman hanyar da zaku shirya kanku cikin ruwan sanyi, tsakaninku dai ba wai babu sama da kasa bane na rigima, akoy sosai, sai dai babu wanda zai ji tsakaninku, shi yasa nace Ni da ina da dama da na ringa kawo shawarar a ringa aurawa kowa wanda yake so"
Mah ta ajiye maganar a nutse da kula tana kallon yadda RAUDA ke dan murmushi

RAUDA kuwa, sauraron Mah take yi tun daga farko har inda ta dasa aya
A zuciyarta kuwa tana ayana' Mah kennan, idan haka za'a bi lalle za'a samu saukin wasu abubuwan, ama kuma da yawa ba zasu yi auren ba, bayan wannan Mah duka kaf Yaren soyaya da sauransu na yar gata ne ba wai Ni RAUDA ba, yaushe zan tsaya batawa kaina lokaci da maganar soyaya? Zan iya yin aure idan ba hali na kara gaba, to rayuwar tawa dukantama ai ta in da hali ko ba hali ce, Allah dai ya sa mu dace"

A fili kuwa a tausashe sosai RAUDA ta sada kanta tana fadin" Hakane Mah, yanzun ma ABDALLAH ne yace na roka masa alfarma yau ya zo ya gaishe ki, sannan ya ga jikin nawa wai"
Ta karashe maganar tana ji kamar wace ta yi wani laifi a harshenta, da shayin furucin bakinta kamar wace ta fadi abin a tuhumeta?, sai hakan ya zame mata sabo, kai, ikon Allah, ita RAUDA? To ko tsakiyar dare ta so yin zance ai yinsa take yi hankali kwonce bale yanzu? Allah kennan
Chapter 54 · 0% Book details