← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 117

Sashe 113

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar suka samu abin ya koma rizgar kuka kawai da cimuimuyar hijab da tarin tashin hankali marar misaltawa a lokacin da ta samu yayarta itama ba yadda take suka ji tamkar ace basa raye a duniya da wannan tashin hankali, gashi sunna ji sunna gani a cikin gidan mahaifin da a da suka fi kowa isa da tunkaho a yanzu sun boye sun rasa inda zasu saka ransu domin uban da suke takama da shi aure ne ya bashi ama ba nasa bane, kuma ya nuna idan sun so zama ba zai hanna ba, sai dai shi kam bai san wani irin zama zai yi da su din ba, abinda ya sani kawai zai kiyaye hakinsu a kansa, shi yasa shi dinma ya fi yarda da maganar fitarsu daga garin, domin ya riga ya san cewar a yanzu zaman garin nan ya fi karfinsu, rayuwar da suka yi a da tamkar su suka haifi kansu a yanzu ba zai taba iya zuba masu ido su maimaita ba , dan haka duk inda za'a kai su zai yi iya yinsa dan gannin ya fita hakinsu, wannan tashin hankali ya karra saka Amnah a mummunan halin da ya nemi jirga tunaninta, ba ruwanta da halin da mahaifiyarta ke ciki, domin ba itace a gabanta ba, abinda ya fi rikitata damuwarta da asarar da ta gane cewar ta tafka ta rayuwa fiye da komai, asara ta duniya da kiyama idan bata tuba ta koma ga Allah ba, ba mutunci, ba usuli, ba MALEEK, kadararta mai zafi ce wace ta hannata sukuni sai kuka da maimaita kalaman mahaifiyarsu ta cuce su da ta bi wani mutumen har suke hayayafa da aurenta, fadi take yi ita ta san ba zata rayu ba ba MALEEK........
(Allah ka hanne mu aikata aikin dana sani, ka rabamu da muguwar Kadara)

Sai bayan isha RAUDA ta koma bangarenta bisa rakiyar Jakadiya, wace ta yarda ta tafi da kyar bayan Mah ta tabatar mata jikinta da sauki suka shigo har baban falon daga nan Jakadiya ta duka cike da girmamawa ta yi mata salama, ita kuwa ta rasa yaya zata yi dan gaba daya yanzun sai take jin bangaren ya yi mata wani irin girma, a dole ta lalubo wayarta ta dannawa salima kira suka shiga dan zantawa tana yi mata nacin ta zo bangarensu, ita kuwa tana fadin wane ita, ba yanzu ba, Bah ya masu kwakwaran kashedi cewar ba yanzu ba, karshema firar ta ki dadi dan Rauda ta rasa yaya zata yi da ita kan dan Allah ta zo ita gidan ya mata girma, a dole suka yi salama ta sake dokawa Atu kira, ama take ringin ba'a daga ba sai a kira na biyu ne Atun ta daga kamar wace ke barci ta ce" Sweetheart "

A hankali, cikin yannayin sanyin jiki da Muryar da ta wuni da shi ta furta" Atu, kin yi barci ne?"

Atu ta sake bude idannuwanta da kyau ta ce" Ina kwoncen dai, yannayin nan na saka kasala sosai, yaya kike, lafiya nake jin muryarki wata iri?"

RAUDA ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Atu , Bana tunanin zan iya, karfina karewa yake kokarin yi....., Atu ke kin san burin irin mijin da nakeda a rayuwa, Atu sarauta ba tawa bace, gaba daya rikicinta da irin yadda na shigota nema suke yi su karar da karfina "

Da kyau Atu ta zauna tana sauraron Rauda, ta bata dukkan kulawarta saboda ta sani idan har Rauda ta budi baki ta fara magana haka tana cikin babar damuwa a zuciyarta
a tausashe ta ce" Subahanallah, wani irin ba zaki iya ba? me yake faruwa? wani abin yayan ya maki?"

RAUDA ta lumshe idannuwanta tana jin irin yadda take son yin maganar kamar ba za'a fahimta ba

A hankali ta ce" Babu abinda ya min, Ni dai nake tsoron kasa zamowa abinda nake son zama, "

"Tl me, me yake damun ki, Please ki min magana dala dala mana " Atu ta fada a tausashe dan zata so ace RAUDAR ta yi kokari sun yi maganar yadda ya kamata saboda ta cire mata damuwarta

Huci Rauda ta fitar mai dan dumi a hankali ta ce" Na riga na yi saken da kadarar zuciyata ta cafki wanda ya zamo gogage a lamarin kwaliyar mace da duk wani abin da take iya birgeshi da shi, uwa uba yake da ya'yan banki , da kuma RAWANI Atu...."
Ta ajiye tana lumshe idannuwanta dan jin nauyin abin sosai a zuciyarta da harshenta

A hankali ta ɗora da fadin" Dan son kai irin nawa, nake jin haushinsa da matarsa bayan na san wanda aka aura min ko bayan mata idan yana da bukata zai iya ajiye kwarkwaraye su amsa kiransa a duk lokacin da ya so...., Atu tana iya kasancewa ganninsa ya min wahala a lokacin da na so, kuma magana da shi ta zamo aiki a lokacin da na buƙata,......Atu ina tsananin kishinsa wanda ke neman yi min ila , bayan na san wa nake aure....uwa uba na fara shakun in har zan iya birge shi ko na ga abinda nake son gani da ji ƙarara ba ta wani yannayin da nake jin ana iya ba wata dina ba!, Atu ban san yaya zan kwatanta maki ba, ina iya cewa ina jin kaina tamkar ba mace ba a gabansa........duba ki gani yau kwana na na h..........."

Dif ta dauke maganar sakamakon bude kofar nan ta baya ta wajen hanyarsa ta sirri da aka yi aka shigo

A hankali numfashinta ya shiga sauka daya bayan daya sakamon gannin bayanuwarsa a cikin idannuwanta a irin wannan lokacin da ya shigo yannayinsa a gajiye, sai dai daga tafiyarsa ba zaka gane ba sai ta idannuwansa da suka yi wani irin lumtu, shigar jikinsa kuwa banda daukan ido da shiga ido babu abinda take yi, domin ta hau jikinsa das ta zauna Bama kamar alkyabar dake jikinsa

A hankali wayar dake hannunta ke neman subucewa, duk bayanan da Atu ke kwararowa ta daina fahimta har sai da Atun ta dawo maimaita hello hello ama tamkar ba kowa a wajen, bayan ga call din bai mutu ba kuma takan ji abin Ac dake dan tite tite lokaci zuwa lokaci wanda ke tabatar mata ba network ya datse kiran ba

Idannuwansa a kan fuskarta suke, tunda ya shigo din
Gaba daya fuskar yake kallo da zagayayen hijab dinta wanda ya matukar bi kyan fuskarta ya kawatata.....shi fa a da yana yiwa hijab kallon abinda in za'a yi sallah ya dace a ringa sakawa dan a ganninsa in rufar ce ai abayama sutura ce, sai dai tunda ya santa ya ringa ji a ransa idan zai samu ta ji komin girman suturar da zata saka ta dora baban hijab da nikab, zata fi kyau a haka.........

Idannuwanta ta sauke saboda dokawar da kirjinta ke yi, cikin yannayin sanyin nan ta dan dago zata kuma kallonsa da sauri ta lumshe idannuwanta sakamakon maganar da ya fada dazu da safe kafin matarsa ta katse su, wata irin kunya ta ji tana neman rufeta a zaunen da take dan haka ta kai hannunta a hankali ta shiga dan murza goshinta sannan ta dago muryarta a boye sosai, sai dai amon na shiga kunnayensa ta furta" Barka da shigowa"

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya karaso inda take zaunen yana Binta da kallo,
wayarta da ta saki jikinta ya saka hannu a hankali ya juyo da ita ya ga kira na tafiya da kuma sunnan ATU
Numfashi ya fitar kadan, kasa kasa ya ce" How Are You?"

Da sauri Atu ta datse kiran tana talabe kuncinta a ranta tana ayana' Dama yana nan take waya da Ni a irin lokacin nan?, wai wani ba zata iya ba, Ni na yarda ki Kunno fitinar da zata sa ki haukace min a nan ke daya ki ringa fada ? ke da MALEEK daidai da junna ne, kuma ke ce mahadinsa'

RAUDA kam kasa sake bude baki ta yi a lokacin da ya kai bayan hannunsa dake fitar da kanshin turaransa mai naci ya dan shafi gefen fuskarta ya bar hannun a jikin gefen fuskar nata bayan ya dan duko da tsayinsa kadan

Dayan hannun nasa ya saka yana dubanta a nutse ya kama hannunta na dama da dayan kuwa ya talabi gefenta ya mikar da ita tsaye yana kallonta kasa kasa ya ce" Menene?"

66

A hankali RAUDA ta saukar da dubanta daga cikin nasa muryarta cen ciki ta furta" Ba komai "

Dan murmushi ya yi a nutse ya furta" zan samu tea dina? za'a bani yau?"

dagowa ta yi a dole ta dube shi tana jin murmushi na son maye gurbin tashin hankalin da take ciki, dukda ta gama kwanakin da ake yiwa amarya bazawara irinta tun jiya, ba zata ki kai masa tea dinsa ba, bata jin zata taba iya kasa amsa bukatarsa a rayuwa ta wani aikin da zai iya sakata, dan haka da dan murmushi ta gyada kanta shi kuwa ya furta" Thank you"
Sannan ya saketa ya nufi Part dinsa yana sauke alkyabar jikinsa tun a hanya yana sake sauke rawanin jikinsa dan abinda zai fara yi a yau shine shiga ruwa masu zafin gaske sannan ya samu hutu mai kyau ko zai dawo daidai

Yana shiga dakin kiran ISHAK na karra shigowa wayarsa
Dagawa ya yi ya masa shiru bai ce komai ba

ISHAK ya sauke ajiyar zuciya muryarsa dake cikin halin karaya kusan sati guda cirrrr a wannan yannayi ya ce" Barka da warhaka Sir"

YUSUF ya yi shiru na yan dakiku sannan ya dan sauke numfashin dake tabatarwa ISHAK yana jinsa

ISHAK ya sake shan jinnin jikinsa, gaba daya so Yusuf yake ya birkita masa lissafi, tsoronsa daya kar aje YUSUF ya dan abinda ya sa ya shiga jikinsa? Sai dai wata zuciyar na fada masa kai ina da ace ya sani ne da tuni ya nemo shi in a ina yake ya wanke masa dukan rashin tarbiyarsa, ya fi kyautata zaton wani abin ya masa a rashin sani ya sa yake share shi
Chapter 113 · 0% Book details