← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 117

Sashe 86

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba da niyar wulakantarwa ba, dan ya riga ya amsa ko mecece, kamar yadda ya gama yarda cewar ya rungumeta shine zai sa ya manta abinda ya fi komai tsaye masa a rai, ya dubeta da kula sosai , da irin izar mulkin da yakan yiwa na waje wa'inda ba Mah da Bah da kuma Hajia ba ya furta" na san kin gaji yau ko?"

Dubansa ta yi da sauri, dan irin yadda ya yi maganar yana dubanta sai da gabanta ya fadi

Dan murmushin da ya sakata shakun anya murmushin ne? ko ba murmushin ba ya yi mata a hankali ya furta" Ki je ki huta, ga part dinki cen........sweet dream....."

Ya karashe yana juyawa ya karasa nasa part din ya bude ya shige sannan ya rufo kofar a hankali ya karasa wajen bed dinsa ya shiga kashe fitilun dakin ya kwonta yana janyo carbinsa a hankali ya rintse idannuwansa hadi da rukunkume fillon dake saman gadon yana jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa......
Bai taba zaton za'a bashi harka a bude ya kasa karba ba, bale harkar nan ta halal, matar aurensa, duk irin yadda ya rike kansa tsayin lokacin nan shi kadai ya san cikin azabar da yake shiga wasu lokutan idan yana cikin happy, na bukatar mai ɗebe kewa, gata ta samu ama wani lamari mai ban haushi ya hanna shi rawar gaban hantsi?.....in sha Allah zai ture, zai ture dan ya fuskanci matarsa su yi irin zaman da ya dace da su, na mutunci ko na abokin gabar mutunci dan duk abinda ta zo da shi da shi zasu kafta.....

AMNAH Kam......., sai ta ji wannan abin da ya yi wata dungumemiyar nasara ce, dukda ta so ace ta kwana a dakin, sai ta bar hakan zuwa ta hutan da yace ta juya tana jin farin ciki ta nufi dakinta ta sake kunna wayar dan tana son sauraron voice din Habu dan daudu, sai dai tsarin dakin nata ya sakata sake shagala kamar yadda ta shagala a falon nan ta ringa yiwa mahaifiyarta vidion falon haka yanzunma ta ringa yiwa dakin vidio tana turawa a wayar mahaifiyarta sannan ta danna mata voice note tana sanar mata tabas kayan nan sun ninninka nata da aka kawo, ita batama ga natan ba, kai kayan nan sun haukata ta fiye da tunani dan ta jima tana sake dauka har bayi sannan ta zauna sai kace ba itace ke takamar daga gidan kudi ta fito ba, zuciyarta ta sake cika da wulakanci da tarin dagin kai, a yanzu ta gama yarda tana iya bin Mah ko dan ta sayi zuciyar d'anta, idan yaso daga baya ta yi mata zagon kasa dan ta gama ganewa idan har ta idasa baban haja komai ya kare, a yanzu ba wai iya kasar nan ba o
ko waje ta fita daidai take da uban kowa!

Da wannan ta zauna bakin gadonta ta shiga sauraron Voice din Habu tana cire uban lulubin da aka yi mata da rigar da aka saka mata a karkashin lulubin

Tana sauraro ne bakinta da idannuwanta na buduwa zuciyarta na tafarfasa

wani irin takaici ya gama lulubeta a lokacin da ta kusa gama sauraron maganar da takaici ta datse , sam bata ji bayanin aurenta da Balarabe da dukiyar da ta samu ba, a bayane ta furta" Da ke karamar fakirar talaka ce har kika budi baki kika zageni dan uwar mijina na rikon ki?"

Idannuwanta ta lumshe cike da ture tunanin dalilin dake raya mata yana iya sakawa RAUDA ta yi mata haka a bayane ta sake furta" na san ko giyar wake kike sha ke ba zaki so mun miji ba, kuma na san ko tube ki aka yi a gaban mijina a halayan da aka fada min nasa na da ba zaki dada shi da kasa ba bale har ya tanka, domin wanda yake amini a jikinsa ya sanar min irin matan da ya yi mu'amala da su ba kannanun kadangarun bariki bane!, walahi Ni na san tunda na ga matar nan matsayin mamansa sai ta ja min matsala, ba damuwa na sayi fadan ki Ni da ke za'a ga karamin dan iska, in dai ina raye walahi sai na ga bayanki kafin na ji ubanda ya tsaya maki har kike zagina, tunda na ganki na ji na tsane ki, ashe dan talaka ce ke? mtssssss!"
Sosai ranta ya ɓaci, hakan ya sa ta ci alwashi sosai a kan RAUDA, kafin ta yi kwonciyarta dan ko fitsari bata ji, kuma ba zata wanke kwaliyarta ba dan tana so gobe da safe ma ta birgeshi da ita, shi yasa ta gama kudurcewa ranta salolin zata hade kawai zuwa gobe ta gani ........
( Uhum!)

Washe gari haka aka yi yar hidimar girki aka kai bangaren, ama Mah ta hanna RAUDA taɓa girkin dan tunda ta tashi da asuba ta ji jikinta da zafi, shi yasa ta sa ta je bangarenta ta kwonta, har dare a bangaren nata take sai da aka yi sallar isha'i ta sa ta je ta kwonta domin da sauki kawai dai rashin kuzari ne, Mah ta alakanta hakan da matsowar cikawar tabakarta jibi jibin nan, shi yasa take ta yi mata nasiha da rarashi har ta samu ta kwonta

a kwana na biyu kuwa su Atu suka dauke mata hankali, dan sun sakata gaba wai sai an yi mata kitso da kunshi na fita takaba ita kuwa tace ba zata yi ba gaskiya, sunna shan fira sunna ɗebe mata kewa har Mah ta shigo ta sanar masu zata je bangaren Hajia ta yi kiranta tace ta je SULTAN SHAHEED na son ganninsu har ya karaso, suka yi mata a dawo lafiya suka ci gaba da firarsu a tsakaninsu, Firar da rabinta kokarin nunawa RAUDA ne cewar hakuri zata yi na rashin mijinta, addu'a itace abinda zata ci gaba da yi masa har ta koma ga ubqngijinta na nuna Soyaya, ama a yanzu kuma da ta fita a takaba shikenan , duk wani abinda ya dace yi za'a yi, walahi ko bata yi kitso da kunshi yau ba sai ta yi gobe.......
Ita dai walahi zazzabin dake mata ya je ya dawo ya fi takurata, dan ta kiyewa Mah maganar asibiti ne, gani take yi daga dan zazabi sai asibiti? ama nukurkusarta yake daidai misali!

Da girmamawa, da kula ya fara gaishe da su, a kujerar da yake zaune wace take facing din su

Hajia baba bata san da zuwansa ba, sai da aka shigo aka sanar da ita, kuma yau YUSUF ya yi yar tafia tunda asubahi ko da ta kire shi, shima jim ya yi yana tunani yace yana zuwa, da ya kira shi sai yace da shi zuwa ya yi kawai gaishe da Hajiar, hakan ya sa ya sanar mata da gagawa aka shiga tarban SULTAN SHAHEED.

Mah na murmushi take sake tambayarsa takwarar Anmi Sarkin rigima, yana murmushin shima ya ce" Tana lafiya Mah, ai kam zata zo maki hutu ko na dan huta da rabiyar fada ita da yan uwanta"

Hajia na daria ta ce" Allah ya nuna mana, da mun yi farin cikin hakan"

Ya amsa da amen, sannan ya yi shiru na dan lokaci, kafin ya dago kansa da girmamawa da kalamai irin wanda zaka yiwa baba magana da su ya ce"

(😨😨😨😨😨😨😨)
Azl 49
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

A nutse, cike da girmamawa bayan ya dago ya dube su , sannan a tausashe ya ce" Ina mai baku hakurin zuwan ba zata da na yi, na tabata idan har ya san zuwan nawa yana gari zai iya biyoni ne, idan kuwa yana zaune firar ba zata yiwu ba, bayan abinda yake tafe da Ni mai mahinmanci ne"

Hajia ta dubi Mah, Mah kuwa ta sake tsura masa ido tana addu'ar Allah ya sa ba wani abin ne ya samu YUSUF din ba, dan sukan yiwa junna haka, a baya idan YUSUF ya bata mata rai ta ki hakura shi yake zuwa ya wani kalamaiceta, shi yasa a yanzunma tana kallonsa tamkar zata ciro maganar daga bakinsa take ji

A tausashe ya dan nisa ya ce" Dangane da maganar RAUDA ne"

Mah ta dan zarro ido, Hajia kuwa ta dan matso gaban kujerar tana dafe kirji tana kallonsa, sai kuma ta shiga salalami tana fadin" Yi bayani mana Sultan, me ya samu baiwar Allah marainiyar Allah?, me ya sameta?"
Chapter 86 · 0% Book details