← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 117

Sashe 102

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gannin ya bi ta baya ya tabatar mata bangarensu ya koma, dan haka da gagawa ta je ta karasa ta shiga ta nufi Part dinsa

Tunda ta shigo ta ringa bin yannayin tsarin wajen da kallo
masha ALLAH wajen ya kawatu fiye da tunanin bawa, haka kuma bedroom biyu ne da shi su kuwa sauran part din daidaya ne da dan madaidaicin falo bayan falon nan baba sai dayan part din da tsarinra ya yi ginnin dakunnan a jere wa'inda ke nuni da na yara ne

Tunda aka bude aka shigo ya dakata da bale botur din wandonsa yana kallon falon

gannin shiru sai kawai ya bale din ya dauki abin wanka ya shige ya rufe, ya san da an shigo, abinda ya barawa ransa shine ko waye ya shigo cikin su biyu ne, shi yasa ya shige wankan nan, saboda zaman fada yau dole zai yi

Ya jima sosai a bayin, ya fito yana tsane ruwan jikinsa , a kugunsa da tawul daure mai fadi, sai karamin da yake goge jikinsa da shi ya nufo falon part dinsa ya bude ya fito yana sauke dubansa a kanta

Itama mikewa ta yi tsaye da sauri ganninsa a haka, gaba daya ta gaza dauke idannuwanta a kansa saboda irin yadda ya yi freshh da abin ruwan wankan dake diga a jikinsa

"Amnah, lafiya?" Ya tambayeta da kula yana karasowa inda take tsaye

gabanta ya yanke ya fadi gannin ya nufo ta kai tsaye ba wani tsaye tsaye

Yana zuwa da kanshin sabulun wankansa da irin hucin da jikinsa ke fitarwa da tarin kwarjinin da Allah ya masa ya dan dago fuskarta yana kallo kasa kasa sosai ya furta" Aush, sorry wifey, zai huce, idan bai huce ba zan sa a kai ki clinik lafiya ki ga docter Papalo na tabata yana da maganin ciwon ki....."

Babar duniyar da Amnah ta shiga ta farin ciki gannin wannan kulawa harda ambatonta da matarsa ce ta katse lokaci daya daga tsayen d atake wata irin mahaukaciyar juwa da tashin hankali suka sakata yin baya ta maku a kasa jikin kafet din wajen idannuwanta a waje ta dago a firgice tana kallonsa tana kokonta abinda ya faɗa

Da yannayin ya damu sosai da yannayinta ya ce" Subahanallah, Kai, meye haka? kar ki ji rauni mana yi a hankali........." Ya yi alamun zai duka ya kamata, ita kuwa ta yi saurin dafa cafet din ta mike kirjinta na dokawar da ta wuce misali idannuwanta na neman rufewa ta juya da sauri tana fadin" Am, eem, ina zuwa, bari in je na dawo" Ta fice da mugun sauri, shi kuwa ya mike ya bi bayanta hankali kwonce har falo sannan ya tsaya yana kallon shigewarta dakinta da rufo kofar da ta yi jikinta sai rawa yake yi , hakan ya sa ya sauke murmushi ya juyo hankali kwonce idannuwansa suka sauka cikin na RAUDA dake tsaye da cokali a hannunta , ko me zata yi da shi oho, jikinta dauke da wata mahaukaciyar doguwar riga ruwan maroon mai laushi, gashin kanta daure, a kanta ko dankwali babu tana gaban table din jera abinci ta ga wannan ikon Allah

Da farko murmushin ya dauke dif, dan umarnin da ya samu daga zuciyarsa kennan cewar kar RAUDA ta yi wani tunani a kan lamarin, sai kuma ya kwato yancin girmansa ta hanyar dawo da murmushin saman lebensa ya wani motsa kugunsa sannan ya nufo inda take tsaye da cokalin nan a hannunta tana kallonsa

Kai ta sada da sauri ta ci gaba da aikinta ta hanyar barin wajen zuciyarta cike da kunyar yannayinsa, ko dazun sakin bakin da ta yi ta ga ya fito da wani zani a kugu yana bale bale Tu sunna da wani bamakatarai ya bi wancen abar ne, bayan wannan ina ita ina sake kallon mutumen nan? sam ba kunya a lamarinsa

"Meye zaki wani saka mana ido Ni da matata?"
ya fada yana yafa karamin tawul din a gefen kafadarsa

turus ta tsaya daga abinda ta yi niya ta juyo tana kallon kasa wajen yatsun kaffafuwansa a hankali ta furta" Ban san kunne ba, da ban bi da kallo ba"

Gira ya hade yana fadin" Ki dago ki kalleni ido cikin ido mana, kina wani abu kamar wace ke tsoron mutane?"

Baki ta turo tana sake juyar da kanta ta ce" To ka saka abinda ya dace mana, Ni a haka ba zan iya ba gaskiya" ta karashe tana idasa ajiye kwanon da ta dauka ta cenzawa waje sannan ta ci gaba da gyaran table din , dan kuwa girki suka sha ita da masu aikin bangaren , shine ta shiga gyara wajen dan ita a rayuwa tana da sha'awar girki ko dan ta ci ta more da bakinta

Dan tsai ya yi na alamun mamakin furucinta, ya sake kallonta ya ga da gaske tana kiyaye kallonsa, hakan sai ya bashi mamaki ainun, ama kuma bai tsaya jan abin ba ya juya hankali kwonce ya nufi Part dinsa

A hankali ta tsayar da dubanta waje daya tana jin wani radadin na ratsa mata kirji na abinda ta gani, sai kuma ta kora ta ci gaba da aikinta , bata son shigewa cen ita kadai, ta tabata gajiya zata yi da zaman, bata saba ba ko farko zama waje daya kuma sai Allah ya hadata da Mah itama mutun mai son aiki da tsafta, shi yasa basa zama sam koda yaushe cikin aikace aikacen su suke kala kala, shi yasa yau dinma ta fitowarta dan bata ga dalilin da zai sa ta nade a gado ba

A lokacin da yake fesa turare ya dakatar da sauri kansa na sarawa sakamakon tinowa da ya yi a cikin mutanen dake masa girki harda kuku biyu maza

Ajiye turaren ya yi ya fito idannuwansa na neman rufewa ya dawo inda ta zauna tana zuba abincinta ya sake bin shigarta da kallo ya ce " Ke da wa kuka yi girkin nan?"

RAUDA ta kalli fuskarsa jin amon muryarsa kamar ranar da yake mata fadan nan, dan haka ta bashi amsa tana fadin" Ni da masu aiki"

Hannunsa ya kai wajen goshinsa ya shiga murzawa da dan karfi sai kuma ya juya da sauri ya nufi hanyar nan ta baya da suka shigo shi da ita jiya ya dadana wasu numbobi ya bude ya fice

Mikewa ta yi tsaye da sauri tana kallon kofar, gannin an rufo ya sa ta yi kasakai tana tunanin mutumen nan kamar wanda yake tare da almatsutsai masu saka shi shiga halin fushi da sauka a lokaci daya? kai ita kam ta fi kowa shiga wani hali a rayuwa gaskiya

YUSUF na fita Taj ya karaso da gudu ya kawo gaisuwar da ya saba kawo masa kansa a kasa

YUSUF ya rintse idannuwansa dan ba zai so jin amsar tambayar da ta zama wajibi ya yi ba, sai dai dole zai yi tambayar nan , dan haka ya ce" Masu dafa abincin nan maza tare suka dafa da RAUDA?"

Kai Taj ya sake sadawa a hankali ya girgiza kansa ya ce" A'a sir, tunda chef din kicin din ta sanar min Hajia ta fito tana kicin na suka bar wajen lambu ina fatan ban yi laifi Allah ya kara maka lafiya"

idannuwansa ya lumshe yana fitar da huci mai sanyi daga zuciyarsa,
ya jima a tsayen nan kafin ya ce" Ka cire su a harkar kicin tunda tana son shiga,nd......"
ya dan dakatar yana bin manyan talo talon dake yawo da kallo ya ce" Nd ko da wasa, kar wani ya shigo inda za'a iya haduwa da ita........Doka ce"

Da sauri Taj ya amsa yana sake dukawa, shi kuwa ya juya ya nufi dakin da suke rufe masu laifi kirjinsa na masa zafi da wani tunani da ya yi a kan maganar da ake cewa idan ka bi ta wani sai an bi takan nan?
' innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, ya Allah ka yafe min abinda na ringa aikatawa, ya Ubangiji ka yafe min kurakuraina kar ka kamani da RAUDA.......' shine abinda yake ayanawa har ya kama karfen da Habu dan daudu ke ciki ya yi tsamo tsamo kamar kazar da aka saka cikin ruwan zafi

A lokacin da AMNAH ta shige dakinta direct bayi ta nufa ta haye saman wc cikinta na kurdawa tamkar zata zubar da hanjin cikinta hankali take hannayenta saman kanta

Tuni ta cire abayar nan dake jikinta ta Yar a nan ta saka hannayenta tana sake sosa kanta dan sai ta ji kamar tafia ake yi mata a cikin kan nata

*Clinik lafiya, docter Papalo* kunnayenta suka jiyo daga bakin MALEEK? wannan wani irin tashin hankali ne? dama ya san Papalo? , Da karfi ta ja ruwa ya kora abinda ta aikata ta janyo pampon nan ta wanke jikinta ko sabulu mantawa ta yi da sakawa tsabar tashin hankali ta kuma fitowa dakinta ta duka ta warto wayarta tana dane dane hankali gaba daya yana daf da barin jikinta, domin ya zamto mijinta ya san rayuwar da ta yi da Papalo shine abinda ba zata taba so ya faru ba a rayuwa, dan kuwa da wahala idan har ya san haka ya iya zama da ita, ita kuwa in har akace zata bar daular nan komai na iya faruwa da ita, ta riga ta shigo rayuwar nan bata tunanin akoy wata bak'ar kadarar da zata fitar da ita, ko mecece, shi yasa ta kudurta aniyar a kwana kusa sai ta san yadda ta yi da yarinyar cen, sai ga wata fitinar na son bilo mata?

Ringin take yi ama ba'a dagawa sai da ta yi ya kai sau biyar sannan aka daga kuma aka yi shiru aka ki yin magana har sai da ta ce allo sau uku sannan aka amsata da murya kasa kasa mutumen ya ce" Lafiya kike kirana?"

Itama da yannayin a tsorace take ta ce" Kai zan tambaya lafiya na ji sunnanka a bakin MALEEK? ya sanka ne dama?"

A zaune yake, sai da ta sa ya mike tsaye yana fadin" Ni? ya san Ni? a ina? a'a fa, wani irin sanina?"
Chapter 102 · 0% Book details