← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 117

Sashe 49

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ransa ya ayana' toh fa'
A bayane kuwa sai ya ki dakatawar ya saka hannunsa gashin nan nata dake baje da ya fi bashi haushi , a ganninsa in ta san fadanta zata je yi ta saka hula mana? Yarinya kamar wata kura du in ta fita sai ta daku? Yau dai an sha duka su uwar fada ta yiwu a daina.
Gannin police din nan ya bude dayan bangaren ya saka shi zura masa ido, ta wajen inda kaffafuwan uwar Abdul yake ko wa police din ya je, shi kam ta yiwu an hadda shi da tababe kuma, yake ta ayanawa a ransa, kasa kasa ya furta" Bari mana, kar ka dauketa"

Dakatawa police din ya yi, har ga Allah bai gane shine zai dauketa ba, shi yasa ya shirya iya shirya wa dan kar ya daukota aje tana da mugun nauyi ta kada kato a shiga uku, sai gani ya yi Sir da alkhyabarsa ya cicibo RAUDA ya mata daukan jaririya domin a hannayensa ya daukota ya juya ya nufi ciki, shi kuwa daga nan ya tattara kakayayakinsu ya ba Salima da ya dakatar sannan ya ja motar ya fice da ita dan sai ya mata sumul zai dawo da ita ya ajiye a muhallin ta sannan ya ba direban dake janta ky dinsa

A nutse yake nufar dakin Mah, tunda ya shigo din, likitar kuwa na take masa baya bayan ta risina ta masa Barka da karasowa hannunta rike da jakarsu na likitoci sannan ta bi bayansa kamar yadda ya mata alamu, yan matan dake zaune a falo na biyu kuwa suka yi mutuwar zaune suka bi abinda suke ganni da ido, dan babu wani abinda ya shafe su da reton da hannunta yake yi, abinda idannuwansu suka gane masu shine MALIK dauke da wannan budurwar da Mah ke kira baby, wace Mah ke yawon nuna mata kulawa a gaban kowa, Wada Mah tace y'arta ce bayan iyayensu sun sake tabbatar masu basu san lokacin da ta haife ta ba, ya nufi dakin Mah da ita , likita na biye da su, Salima na dafe mata baya....kusan sai suka rasa abin yi a zaunen nan, domin a dan zaman nan da suka yi sun riga sun fahimci in dai so suke yi su sayi wata zuciyar da zata iya kusanta su da YUSUF sai dai su sayi ta mahaifiyarsa, dan duk irin yadda aka nuna masu mutumen mutumen mata ne, abin na neman gagararsu, dan ko da wasa su dai abin nan bai tabata a kansu ba, sai gani sai hange tsakaninsu da shi, kusanci ko na kwabo sun kasa ciyowa daga fadarsa, ko a yanzun gaba dayansu tsoron karasawar inda yake ya saka su tsayawa da zubawa sarautar Allah ido!

Tunda ya bude dakin Mah Musulima ta dago daga vidio call din da take a saman kujera ta ji tamkar zata summa ta zuba masa ido, lokaci daya kuma ta mike tana daukan hijab dinta dake ajiye ta ware shi za saka ta fice a dakin dan tunda ya kalleta sau daya ya ja tunga ta san me hakan yake nufi, a dole ta saka hijab din da aka saka su saka shi dan dole a cikin gidan ta fice tana jin zuciyarta tamkar zata fito daga kirjinta, dan Allah yana ganni ita a zaman nan da farko an nuna mata wannan miji ne da ya dace da duniyarta dan sarautarsa da kudinsa, a hankali ta idasa gane ko bayan su, miji ne da ya dace da ita dan ya isa a so shi, ya haɗa qualities na mamaki, ya kasance jaruminta burinta, mafarkinta, ita fa ta jima da kamuwa da so din da koda bashi da komai tana iya rantsewa cewar zata iya zama da shi, bale ga ya'yan banki ga sarewa jama'a, kwarai a matsayinta Na yar Sarkin kasuwa ya dace ta zama matar MALIK, a nan sarautar zata gama haduwa gaba da baya

Direct bakin gadon ya kaita ya shinfidata sannan ya juya ya koma wajen kujerun nan ya zauna yana duban agogonsa da auna lokacin da Mah ke iya shigowa a zuciyarsa

Likitar kusan du Salima ta yiwa tambayoyi ita kuwa ta bata amsar gaba daya abinda ta sani dan haka da gagawa ta juyar da RAUDA ta shi bata taimakon da zai taimaketa ta hanyar fara duba ciwon da ya hadasa mata zubar da jinnin nan dan ba sumar ta fi damunta ba , ba kamar ciwon dan in har ya taba wajen da ba'a so dole a kaita asibiti a shiga bincike, domin ita summa ai ko da hannu ana iya summar da mutun in dai aka daki keyarsa bale da wani makami.
Ajiyar zuciya ta sauke gannin ciwon , cikin kwarewa bayan ta hade gashinta ta daure mata shi ta yi maganin ciwon sosai ta saka mata dukan abin bukata sannan ta daure mata shi da farin abin pansama sannan ta juyata ta dora kanta kan matashin kai mai laushin gaske ta shiga duduba jikinta sai dan balshe a cinyarta nanma ta saka mata magani sannan ta nemi jijiyarta ta saka mata karin ruwa dan kadan na dauke zafin ciwon , yana karewa ta cire mata ta yi mata allurar dake iya dawo da ita sannan ta zauna daf da ita tana rike da hannunta mai dauke da allurar nan dan sai ta farka ta ga zata ci gaba da yi mata ne har ta ji sauƙin ciwon ko daga wannan ya wadatar?

Bai fi mintina biyar ba Rauda ta ja wani Gwauron numfashi hadi da shedar da ya saka shi dago kansa a hankali ya zuba mata ido
Da farko tamkar a lokacin take shirin barin duniyar mutane ta farka, a hankali a hankali ta samu tana jin maganar likitar nan sama sama a kanta tana jimke da hannayenta bibiyu har ta gane a duniya take kuma magana ake yi mata a daf da ita

Idannuwanta ta bude da sauri tana waige waige, a birkicen nan da kake farkawa idan ka summa, lokaci daya kuma ta shiga kiran sunnan Abdul

Da sauri Salima ta karaso mata shi tana kallonta hawaye na cika mata ido ta saka mata hannunsa cikin nata tana fadin" Gashinan RAUDA ga Abdul din fa"

Shima tunda ya ga ta farka ya dora kansa a kirjinta yana fadin" Aunty, auntyna, auntyna"

Tunda kunnayenta suka ringa jiyo mata amon muryarsa ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idannuwanta hawaye na zubowa ta gefe da gefensu dan sarai ta gane a dakin Mah suke, kuma ta gane likita ce ke kanta

Baki ya tabe yana dauke kansa a ransa ya ayana' ka ga wani rusheshen d'a ta lalata shi, wannan katon saurayin yana wani runguza mata kai a kirji? Lalle su uwa masu dadi , shi dai soyayarsa da Mah ido ne ta tsolewa mutane ama ai wasu iyayen sun iya shagwaba ya'ya, shi bai isa ya dora kansa a kirjin Mah ba yanzu zata ture tace kai meye haka dilla kauce kar ka fasan kirji!' ( wai Ni ina hadinka da mu ne mai martaba?)

Dukkan kular da ta dace likitar nan ta bata sannan ta dawo wajen da yake ta masa bayanin zata dawo dole a gobe dan ta ga yannayin jikinta, idan da sauki shikenan sai ta cire mata allurar karin ruwan in kuwa dole sai an ringa zuwa saka mata magani har ta warware shikenan, abinda dai yake wajibi idan ta warware sai ta je an duba kan a na'ura dan harkar kai ana takatsantsan da ita.

Daga nan ta tafi, shi kuwa ya mike da hannunsa ya yiwa Salima alamun ta zo

Da sauri ta mike ta je, yana sake duba agogonsa ya ce" Ki zauna da ita har Mah ta dawo, zan je part dina"

Da to Salima ta amsa ya fice shi kuwa ya nufi nasa bangaren domin a yau zai yi transfer na kudaden kayan aikin da zasu shigo na ginnin fadar baki dayanta, dan a satin nan za'a fara aiki jajir , domin ya samu da kyar ya lalaba Hajia ta yarda a yi ginnin fadar a mamakeken filin dake jikin tsohon gidan fadar, nan din ya nuna mata yana so a bar shi matsayin gidan dukkan wasu da suka shafi fadar, su waziri da sauransu......

Sunna zaune ne Salima na fama da Abdul kan ya ci kwan da ta soyo masa ama ya kasa cin wani abin kirki dan hanjin cikinsa sun gama kulewa da horon yinwa Mah ta shigo da sauri tana masu salama hankalinta a kan RAUDA dake barci Mai nauyi da kuma Abdul da Salima

Jakarta ta ajiye da sauri ta karaso ta zauna tana dubansu zuciyarta na tsintsinkewa tana jin wani abu kamar tsanar matar da bata santa ba, itama bata santa ba na taso mata daga cen cikin zuciyarta

Dubanta ta kai kan Salima idannuwanta a kausashe ainun ta ce" Matar nan ce ta yiwa yarinyar nan dukan nan? Lalle yau ba zan iya hakura ba, sai na kuleta!, kennan ita ta dauki kannin na RAUDA? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, lalle akoy mutanen da basa jin tsoron Allah, na yi ta kiran numbobinku bana samu na yi tunanin baku ji ba ashe ku tashin hankali kuka tarar a cen din? Ba zata ci bulus ba walahi , dan na daina hakura kowani banza yana takani da ahalina dan son zuciya!"
Chapter 49 · 0% Book details