← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 117

Sashe 84

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sam bata san har ya dahu ba, sai da kukan butar ta sakata juyawa da sauri ta mika hannu ta kashe gaz din sannan ta dauko abin juyewa ta juye komai ta juya da su ta fito a nutse ta nufi dakin Mah ta kai mata shayin da kuma maganinta

Maganin ta tsaya sai da Mah ya sha sannan ta ajiye sauran ta nufi dakinta ta shige ta rufe da ky

Tana rufewa ta ja ta tsaya kanta na sarawa , idannuwanta na yi mata nauyi, kirjinta kuwa na yi mata zafi

A hankali ta karasa wajen madubin dakin ta ja ta tsaya ta tsurawa fuskarta ido

dan kwalin kanta ta cire a hankali ta ajiye gaban madubin sannan ta saka hannu ta cire ribom din kanta dan siriri fari shima ta ajiye kafin ta zubawa fuskar tata ido

Hawayen da idannuwanta suka tara take bi da kallo, zuciyarta ba tsintsinkewa da wani fitinanen tashin hankali

Ta sha tsayuwa ta dubu kanta tace da kanta RAUDA kin ji kunya, RAUDA kin saka kanki a uku tunda kika ce wannan rayuwar zaki yi, me kike nufi RAUDA? Yaushe mijinki ya rasu, abin kaunarki, wanda ya nuna maki so da gata tunda ransa sannan ya rasu ya kuma Bara maki wani lasisin so da gatan a duniya wanda koda yau kika rasa mai kama hannayenki da izinin Allah ba zaki tagayara ba in dai kin kiyaye dokokin Allah, sai dai kashh, tun kafin a shafe shekara ke RAUDA shine kike tunanin wani abin da ba zai taba fisheki ba?, me aka yi aka yi namijin da ya cika takama da jiji da kai? RAUDA babu so a wajen da ba za'a iya fadarshi ba, ke mace ce mai daraja, furta so ba rashin daraja bane, ko alamuntawa, sai dai ke taki darajar abar dubawa ce RAUDA!, kin jurewa lokacin da baki da mai maki fadama bale yanzu? me aka yi aka yi soyayar kanta? RAUDA ki kama kanki, kar ki yi abin Allah wadai, RAUDA ki kama kanki!'

A hankali ta lumshe idannuwanta daga kallon fuskarta, a nutse ta janyo kujerar gaban madubin ta zauna ta sake dago fuskarta ta tsurawa kanta ido
A nutse ta shiga yiwa kanta kalaman da zasu fisheta, wa'inda ta tabata in dai ta rike to kuwa tsaf zata tsira da mutuncinta, a tausashe ta shiga ayanawa kanta magana kamar haka' Ke mutun ce kamar kowa RAUDA, kuma Allah na iya jarabtarki da abinda ke iya yi ke iya rikitaki a rayuwa har ya zo ya nemi zame maki AZAL, sai dai idan har kin rike addu'a babu abinda zai same ki, mummunar kadararki zata juya ta dawo kyakkyawa......., RAUDA kin kasance mutun mai tsare tsare da addu'ar kalar mijin da kike so a rayuwa, misali bakya son namiji mai shegen son mata ko aure aure dai da sauransu, to a kan me zaki dubi mutumen da kafin darajar sarauta ta hau wuyansa ya kasance mai rike da darajar sarautar bakin layi wace kowace yan mata ke wawarsa?, Haba RAUDA a yanzu da igiyar daraja irin ta sarauta ta hau kansa ke da kanki kin sani karya ne ace dayar nan ce, bayan wannan ki duba ki gani, ke da aka raba ake girmamawa aka ba daraja yau ke ce da zagin matarsa?, idan Mah ta ji ki ce me? hana RAUDA me ya kaiki wannan gangancin? me yasa ba zaki ci gaba da tafiyar da rayuwarki yadda take ba?, Eh lalle YUSUF shine AZAL din ki!, sai dai kuma addu'a da neman tsari ai yana maganin komai ko RAUDA?, kema mutun ce mai rai da lafiya kina iya gannin mutun ki ji ya maki, ama kuma kamar yadda kike iya gani ki ji ya maki kina iya kawar da kanki a kansa, bale idan mutumen nan kin gane take takensa, shikenan ke da shi sai ki yi ta neman tsari, ke wai menene soyayar kanta? ake rayuwa ba soyaya kuwa lafiya, to kema daga yau ba ke ba wannan maganar, bale ke da Allah ya taimaka ganninsa sai idan kin so? baki ganshi Bama bale har hankalinki ya nemi gushewa RAUDA!'
Magana take yiwa kanta idannuwanta a lumshe a cikin zuciyarta, kuma har ga Allah maganar ta Ratsa ilahirin jikinta ta yarda da hakan, domin a yannayin nan da take ciki kunnayenta suka ringa jiyo mata Muryar Jakadiya baba tana bada umarnin a kama alkyabar uwar gidansu, a yi me a yi me

A hankali ta dago idannuwansa sakamakon shigowar da Salima ta yi tana kiran sunnanta

Ido hudu suka yi ita da Salimar
Salima na dubanta ta ce" Dear, me yake damunki ne? yau ko baki da lafiya ne babyn Mah? taso mu raka aunty Amnah mana Gatacen sun fito Su Bah na yi mata nasiha"

Murmushi RAUDA ta kirkiro a hankali ta dan rausayar da kanta tana kallon Salima ta ce" Sisi am, zan yi sallah ne na dan yi karatu, ki je zan tardo ku idan baku dawo da wuri ba in sha Allah "

Gyada kai Salima ta yi ta yi mata murmushin itama sannan ta juya ta ja mata kofar a nutse

Mikewa RAUDA ta yi ta je ta rufe kofar da ky sannan ta nufi bayi tana sake dannar kanta , fadawa kanta take babu wani abinda ke damunta da su baki daya, sake fadawa kanta take yi ko me zata gani ko ta ji ba damuwarta bace in dai abinda ya shafe shi ne da matarsa, kuma in sha Allah daga shi har matarsa ta yiwa kanta alkawarin zata fita a harkar su , ba ita ba su bale ranta ya ɓaci!

Tana gama wankan da zata je barci ta saka tufafinta doguwar riga a saman pant dinta kadai ta daure gashinta sannan ta shiga gabatar da sallar isha'i, tana gamawa ta dora nafilar sannan ta cire ta shafa turarukanta ta je saman gadonta ta sake kakabewa ta yi kwonciyarta tana dora wayarta saman abin gadon bayan ta kashe fitilar dakin

Da addu'a da juye juye da kyar ta samu barci ya fara fizgarta, hakan ya sa bata san ta dauki lokaci a kwoncen ba, kamar wace ta je duniyar da bata san abinda take yi ba ta dawo haka ta tsinci kanta, har sai da ta ringa jin amon kiran wayarta sama sama sannan ta bude idannuwanta tana jin gabanta na faduwa ta lalubo wayar da sauri ta duba screen din ta ga sunnan Mah ke yawo a sama

da sauri ta daga muryarta na shakewa ta furta"Mah?"

Mah dake zaune a falo ita da YUSUF takaici ya isheta, sai shayinsa, ta shiga ta dafa masa wai ba shine ta saba bashi ba, ta tambaye shi wani irin dandano yake so yace shi bai sani ba shi dai wanda ta saba bashi idan ya zo, ita kuma tunda RAUDA ke hada mata tea bata taɓa Sannin me da me take haɗawa ba, ita dai ta san da ta mata wani mai dadi tace ta ringa yi mata shi kulun bale da ta sanar mata tana haɗawa harda kafi amarya kanshi saboda yana karra lafiya sai kawai tace a rike hadin

da Kula da kuma yannayin tausayinta Mah ta ce" Daughter, kin yi barci ne? idan kin yi barci yi kwonciyarki kawai"

Dirowa ta yi daga saman bed din har tana yarda hularta saboda murya Mah sai ta ji kamar bata da lafiya ne, ko abin barci ne ya sa ta ji haka? ita dai da sauri ta ajiye wayar tana fadin" Gani nan zuwa"

Bata tsaya daukan hijab ko wani abin ba, tsoronta daya kar aje jikin Mah ne, dan lokaci zuwa lokaci ciwonta na tashi, shi yasa ko yanzu ta fice daga ita sai doguwar rigar nan da ta sauka har kasa, sai dai tana da tsaga daya jal daga gefen cinya, gashin kanta daga gaba ya kwonta lambuk daga baya kuwa du ya nanade irin na masu gashin nan, dama dama tana da dan dogon hannu kadan rigar, ama bayan wannan rigar mai lafewa a jiki ce sosai shi yasa harta sawun pant dinta ana gani

Da sauri ta bude dakinta, kafarta sanye da takalmin daki na kusa da gado mai gashin mage mai kalar pink ta nufi dakin Mah da sauri

Har zata kama ta bude kofar, Mah ta furta" BABY?"

Da dan sauri ta juyo inda ta ji Muryar na Mah, sannan ta juyo da dan sauri kadan ta karaso ta kai zaune daf da Mah tana fadin" Mah jikin ne? ina ke ciwo? kafar ce?"

Mah ta sauke murmushi tana jin kaunar RAUDA har cikin zuciyarta ta kama hannayenta ta ce" Baby Lafiyana kalau, sorry daughterna na tasheki ne ko,?"

Sai kuma ta juya wajen da yake hakimce cikin shigar kayan barcin shima masu duhu da santsi tana kallonsa ta ga lokacin da RAUDA ta sauke ajiyar zuciya jin lafiyar mah kalau ta ce" Ji fa rikicewa, shi yasa nace ta yiwu ta yi barci, tashi ki je ki yi kwonciyarki, ko ki nuna min yadda ake yi na nuna masa ya je ya koyawa matarsa ta dafa masa, barima ka ji mun cire ka a kwanon abincin part dinmu tunda mun maka aure!"

Tamkar an dakatar da ita haka ta ja ta tsaya a zaunen nan gabanta na wani irin mummunar faduwa

Da kyar ta iya daidaita kanta bisa kwarin gwuiwar da ta ba kanta ta dan saki murmushi ta mike tana dan susar kai ta ce" A'a Mah bari in je in dafa"

NA SAKA BONANZA TA NOVELS DINA BAKI DAYA A KAN FARASHI MAI RAHUSA 1K IN SHA ALLAH, KI TUNTUBENI BISA NUMBANA LAMAR HAKA 93811618

Azl 48
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim
Chapter 84 · 0% Book details