← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 117

Sashe 105

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mah ta sake lumshe idannuwanta, kwarai dukkan abinda yake fada gaskiyar kennan, sai dai tana so ne ya zamo ya yi sadaukarwa ya kuma bata dama saboda rayuwa, da kuma fatan Allah ya dubi aiyukansa na kirki ya yafe masa na banza, dan haka tana dubansa ta ce" Ka ga, a duniya babu abinda mutane basa yi saboda dukiya da mulki, kuma a abinda ka fada sai an zauna za'a gane in ƴaƴanta sunna tare da ita kuma in sun san abinda yake faruwa da su, bayan wannan Ni uwa ce, kuma wace na ga rayuwa kala kala, ba zan tashi tashi guda in hade kowa da kowa a laifi ba, kwarai iyayenta sunne tushen tarbiyarta, ama kuma Allah mai shiryar da bayinsa ne, idan ita din da rabon hakan sai a bata dama, haka din baban jihadi ne, idan kuwa ta yi nisa a tafiyar bata jin kira sai a salhance mata ta hanya mai sauki ta yadda Allah zai yi duba da halayan da aka aikata dominsa masu kyau ya yi yafiyar wa'inda aka aikata marar kyan, ka fahimta?"

Kai ya gyada yana duban Mah

Mah ta dora da fadin" a duniya bawan da zai ringa aikata sabo yana sane ya kasa tuba ne abin tausayi, da kuma bawa mai yin tuban muzuru, bayan wannan duk wani wanda ya aikata laifi ya koma ga Ubangijinsa to ya ci gaba da astagafari in sha Allah Allah zai yafe masa......... ka yi rashin ji YUSUF, ama ka daina right?"

YUSUF ya gyada kansa yana kallonta da sauri

Mah ta yi murmushi ta ce" To ka bar sake saken munanan tunanin da suke iya tsayar maka da numfashi, idan ka haihun ka saka albarka ka kai makaranta ka yi nasiha ka yi hakuri, dukkan sauran abinda Allah ya yi mai kyau ne ka fahimta?"

Yusuf Ya ce" Eh"

Mah ta ci gaba da fadin" Dukkan wani wanda zai zageka da shi kuwa ka saka masa ido ko wanene, domin farkonsa ya sani bai san karshensa ba, idan ya zamo mai isgili sai Allah ya jarabce shi da farkon ka, a lokacin zai gane cewar jarabta ce ta Ubangiji, ka ci gaba da taimakawa baiwar Allahn nan, ka kuma jajirce wajen kwato mata yancinta, Amnah ka yi hakuri ka gyara zamanku, kar ka sauta sai idan ya zama dole, kar ka wulakantata saboda abinda ta aikata ko iyayenta suka aikata, idan ka tashi yi mata shara'a ka yi mata cikin sirri saboda iyalinka ce, ko yau ka rabu da ita ta taba zama matarka, maganar bata son mu kuwa ka bata lokaci in da rabon ta so mu fine, idan bata son mu YUSUF normal ne ba wani abu tsakaninmu da ita mu, domin iyayenta muke daga wannan ba wani abin, YUSUF zaka iya yi min haka kuwa?........."

🥹🥹🥹🥹 Allah ka gafartawa iyayenmu

Azl 62

*MAGANIN KARA KIBA 3IN1*

*Ina meneman kiba ido rufe Kuma tanason maganine ingantacce Wanda baida illah kokadan to tazo gadama tasamu yar uwa indai kibace da gyaran nono dakara hips toga Mganinmu nan 3in1 cikin kwana 7 kacal👌🏻 zakiga yadda Zaki fara murmurewa insha Allah mungwada mungani munbayar angwada munsayar angode insha Allah kawata Zaki godemin da 3500 dinki kinhuta da gorin rashin kiba munan cikin Gombe Kuma munatura kaya ko ina kedai tuntumebi ta Whatsapp ko kikirani Kai tsaye ta 08030861857 sai kunzo🥰*

*MAGANIN HIPS*
*Wannan Maganin anyisane tamasu neman hips sunsha wannan sunsha wannan to gatamunan insha Allah guarantee nakebaki hajiya inada yakini akanta matsala indai tarashin hips ne to anwuce gun 3500 kacal kinhuta kijuya kiwarwasa kisaka kayan gayu kijuyawa Oga yayikallo kawata har yanga saikinmasa ninafadamiki wannan nemeni kisamu naki 08030861857*

*MAGANIN NONO*
*Itama akwaita me inganci kamarta 3in1 data hips wasu suna korafi nifa nono kawai nakeso yaciko yayi bulbul gwanin sha'awa yadda Oga zaiyaba nasa breast cup suzauna das Amman abun yacitura Nasha Nasha magungunan Amman haryau ba chanji to ganamu Nan yakine ne Dani akansa ba Dan kadanba alhamdullahi duk Wanda yasaya saidai godiyace tsakaninmu kema zokigwada Kuma kigodemin location Gombe 08030861857*

Muryarsa a matukar sanyaye yana kallon Mah, zuciyarsa cike da sake saken abinda Mah ke son a yi wanda yana kyautata zaton da wahala ya tabatu ya amsa mata a tausashe kamar haka" In sha Allah, Mah zan yi, in dai na tabatarwa kaina cewar a abubuwan nan da na zayana din, laifin Amnah abinda ta yi a baya ne, kuma baya da niyar yin wani zan dubeta, koda kuwa na taba zmbatar kalmar haramtawa a gareta a kankin kaina zan sake neman malamai su daidaita lamarina da ita, Allah ya sa hakan ya zamo silar gogewar zunubaina "

Mah ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta cike da rauni ta amsa shi da Amen

Zaman nasu kasa daukan lokaci ya yi, ita da kanta burinta ya tashi ya fita dan tuni ta yiwa Bah msg din tana son ganninsa yanzu, burinta ya tafi ta iya daidaita nutsuwarta, shi dinma kuma gaba daya ya sake shiga a wani yannayin daban, mai kara hargitsa masa tunani, a dole ya mike yana murmushin dole ya mata salama ya kuma komawa bangarensa dan baya tunanin a yanzun kuma zai iya zuwa wani wajen, ko a bangaren nasa ya san ba zai iya samun wata nutsuwa ba sai wani firgicin da tashin hankalin

Yana tafiya Mah ta cire hijabinta ta shiga yamutsa gashin kanta hankalinta tashe idannuwanta suka kama zubar da hawaye

Innalilahi, da ace za'a shiga zuciyarta da an ga tarin tausayin yaronta dake son halakata, sai dai duk abinda take ji in sha Allah zata jajirce ya gabatar da abinda zai tsira gobe kiyama, tunaninta a wajen da ya fi tsayawa shine *SHIN YUSUF NA GIRBAR ABINDA SU SUKA SHUKA NE, WATO YUSUF NA AMSAR HUKUNCIN ABINDA SUKA AIKATA NE HAR YA SA SHIMA YA DANDANA MASU ABINDA SUKA DANDANAWA IYAYENSU, HAR YANZU ALLAH YA NUNA MASU YA SHIRYU KO SHIMA YUSUF DIN ZAI HADU DA NASA HUKUNCIN DAGA WAJEN ALLAH????????*

Tunaninta ne ya katse da zubar hawayenta sakamakon shigowar Bah

alamunsa daga barci ya fito domin jalabiya ce a jikinsa, kuma yau yana ɓangaren Hajia ne, wato mahaifiyar Salima

shi da kansa ya san kiran nan ba na dadi bane, domin idan baya bangaren Mah bata so ya zo dan gudun rigimar matansa da suka kasa girma idannuwansu a kan dan karamin abin da yake iya zama abin a ji kunya idan aka ji ya fito daga su suke jira su yi masa daukakawar da kowa zai ji a yi rikicin da bata so ace a yanzu dai , da girma ya gama kama su, suke aurar da y'aya sunna fada a kan abin da ita rabontama da shi an jima, shirme kawai sun kasa gane an riga an zama daya fiye da tunaninsu, su suke ha baba ha karami a kan lamarin nan, ita a yanzu ta lafiyarta ai ta fi komai gaskiya

Kamar yadda ya zama abokin sirrinta, mutumen da idan abin ga yi kuka da burgima ya kama shi take yima, mutumen da koda abu bai shafe shi ba takan saka shi a ciki dan ta gama yarda cewa a nan gidan duniya shi din nan shine sirrinta kuma shine mai sauraronta ya bata shawarar da ta dace koda ba zata yi mata dadi ba, ya sa a yanzunma ta neme shi a fujajan suka zauna a kan abinda yake da ruwa da tsaki a ciki kamar yadda take da shi, ta shiga sanar masa abinda ya gigita shi fiye da tunaninta harma tsoro ya shiga kamata a lokacin da ta sanar masa abinda ta fadawa d'an su, kuma Sarkin garin su, cewa eh, dukkan abinda ta zayana din nan kuma a haka zai zauna da yarinyar harda fadin a ba yarinyar chance din da ya dace dan idan ta gari ce a zauna da ita, in kuwa ta dauko maganar da ake da tabbacin in dai ta samu hanya zata dauko din sai a bata salama cikin salama ko me? ransa ya ɓaci yana kallonta, duk irin hucin zafin da jikinta ke fitarwa yau kam ya kasa hakuri yana kallonta da kausasawar da bai taba yi mata ba ya ce" NA JI, kuma na fahimci dukan bayanan nan da kika fada, sai dai abinda nake son karra tabatarwa shi ne, YUSUF ya nufo ki, a yannayin gigitar da kika ce ya yi kuka, sai kika karra tabatar masa eh hakan da yake faruwa da dukiyarsa daidai din kennan kuma dole zai dauka?"

Kallonsa take yi, gannin kamar ransa a wani iri ba yadda ta so ji ba ta ce" Eh abu YUSUF, haka na fa......."

"Dan Allah zaki iya yin shiru na second biyu?" Ya fada a tsawacen da ya sa ta zabura tana kallonsa gabanta na faduwa

Rai bace yana dubanta ya ce" Ke, kisa ake yi idan an yi shara'ar da Allah ya rubuto Allah ya yafe a yadda muke kyautata zato domin mu musulmai ne, ke Ameerah bulala kike so a masa ne? Sai na kai shi kotun musulunci a kwontar da shi da hannayena na masa, ko mu din zamu je mu sanar kafin a mana aure mun yi rashin jin da a yanzu rayuwar nan yannayin zamani da ya zama haka daidaikun samari da y'an matan ke tsalakewa suke nan kuwa su tuba su dawo su bi Allah, Allah ya dube su saboda dama d'an Adam Ajizi ne, kuma Allah yace da ace dan Adam zai rayu ba yin laifi ya tuba, da ya shafe duniyar ya zuba wasu, ko baki dan cewa ka yi laifinma ka daina babar daraja bace da zaki ringa rayuwa a matse, a takure, ki kuma takurawa yarona a kan haka har ki budi baki ke AMEERAH ki ce da YUSUF zai rayu da yarinyar nan?!" Ya karashe muryarsa a sama saman da ya saka Mah sake shiga a halin tsorata tana kallonsa
Chapter 105 · 0% Book details