← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 117

Sashe 10

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana son mahaifiyar Yusuf fiye da tunanin bawa
Ciwon ta bai taba damunsa ba
Bai taba gajiya da tatalinta ba
Duk irin tsakaninsa da mahaifiyarsa ta gaza sakawa ya saki Mahaifiyar Yusuf wace take ikirarin nauyi ce a wuyansa marar anfani, bata da wani anfani a duniya sai na karar da dukiyar yaronta, kulun ita ba lafiya kulun ana hanyar fita da ita neman lafiya, babu irin matsin da bata masu ba dan mahaifiyar Yusuf ta fita daga ahalinsu da kaffafuwanta ama ta jure ta kawar da kai take zaune a gidan ba dan komai ba sai dan yaronta daya jal dake rayuwa cikin gararin yau da gobe da yan uba gaba da baya, wanda abin ya shafo harda Mahaifinsa domin yau da gobe ta saka abinda kanwarsa da wasu ke fada masa a kan yaron nasa shima ya fara kwaikwayar yarensu yana fadin abinda ba ALKHAIRI babu kuma magani ma yaron nasu, tana zaune a wannan ahali ne dan ta sani komai tsiya adu'arta itace a sama da ta kowa dan haifa ta yi, kuma ita ta sani koda kare da sata dadawa da warinta, Allah ya kadarta mata aure a irin wannan ahali bata da yadda ta iya sai hamdallah da neman hanyar gannin shiryuwar yaronta dan babu abinda ya gagari Allah, kuma ko wa zai zagar mata ba zata rama ba, zata fadawa Allah ya isar mata ta hanyar shiryar nata gudan jinninta mai sonta da kiyaye bacin ranta, to in bandama abin fada da baya masu kadan yau har sunna da bakin gorantawa wani abubuwan rashin ji na yau da kullum? To wane ba wane ba makaho a bisa makahon doki!
Kiyaya ce an dasa a zuciyar mahaifiyar mijinta Tata tun kafin ta shigo gidansu, an fadawa mamansa cewar idan ta yarda aka auro irinta to fa zata rabata da danta, sai aka yi rashin dace dan nata na yiwa maman Yusuf makahon so din da cece kuce din mutane suka yi tasiri a zuciyyarta, tun ana boyayiyar kiyaya da shayi har aka dawo yau da gobe da zama waje daya ya sa ake abu kamar a zamanin jahiliyya, sai dai basu sani ba, ciwon da take fama da shi na gwuiyoyi bai taba kwakwaluwarta ba, hakurinta kuwa ta jima da YANKEWA kanta zata ci gaba da yinsa ne da mahaifiyar mijinta kadai, itama dan tana yar halak, duka sauran zata basu amsoshin tambayarsu a daidai lokacin da ya dace

Nemanta yake yi hankalinsa tashe har bangaren HAJIA, inda ta ja tsaki rai bace ta ce" Ni kam yau na hadu da balakin wannan mata, to yarinya karama ce da zaka wani daga hankali dan baka ganta ba? Allah ya sa Allah ne ya rabaka da kaya!"
Jiki a sanyaye ya fito daga ɓangaren hajiar ya nufi motarsa ya tayar yana tambayar masu tsaron fadar a zuciyarsa yana tunanin ina ta nufa duba da yar tafiya tsakanin fadar da cikin baban gari Damagaran, inda gidanta yake, gashi dare ya yi kuma Yusuf ya jima da tafia

Sosai kirjinsa ke dokawa, hankalinsa gaba daya ba a jikinsa ba har ya samu ya karasa gidansa

Tun daga bakin kofa masu gadi suka sanar da shi HAJIA ta dawo hakan ya saka shi sauke wata irin ajiyar zuciya sannan ya karasa wajen ajiyar motoci ya parker watsetsiyar motar da YUSUF ne ya cenza masa ita cikin sababin da suka shigo ne sai da mahaifinsa ya fara murzarta kafin ya sake su kasuwa

A sukwane ya karasa baban falonta yana ambaton sunnanta
Shirun da ya ji ya tabbatar masa bata nan dan haka ya nufi karamin falonta na cen cikin dakinta

Zaune ya sameta saman kujera waya a kunnenta tana magana a hankali, wanda ya tabbata da Yusuf take maganar dan idan ka ga ta maida hankali tana magana cikin nutsuwa da tausasawa sosai da yaronta take magana shi kuwa yana zuba mata rigima

A tausashe ta ce" Ka tabbata ka daina fushin? Idan baka daina ba nima fushi zan yi fa?"

Yusuf ya saki dan murmushi yana jin nutsuwa na shiga dukan gaban jikinsa, shin yaya suke tunanin zai iya gannin darajar duk wani mai son wulakanta masa ita? Idan ya rasata a duniya shi ya san ya gama lalacewa, ko a yanzu ya san cewa adu'arta ke tafe da shi ba komai ba

A Nutse ya ce" Na hakura Anna, ina gidana yanzu haka"

"Allah ya maka albarka ya tashemu lafiya"

Da kula da tarin kauna ya amsa ya katse kiran har yana sauke ajiyar zuciya ya lumshe idannuwansa yana jin ciwon irin yadda ake saka masa uwa a gaba a wulakanta saboda shi

A hankali mahaifinsa ya karaso inda take zaune ya zauna ya mika hannu ya riko lalausan hannunta yana kallonta ya ce" Me yasa kika tafi kika bar ni? Wa ya kawo ki? Kin san irin yadda hankalina ya tashi kuwa?"

A hankali ta janye hannunta daga cikin nasa tana kallonsa ido cikin ido a tausashe ba da rigimar komai ba ta ce" Aban Yusuf, me yasa tsanarka a kan yaron nan ke hauhawa a kulun ne?"

Dan tsai ya yi yana kallonta , a hankali ya koma ya gyara zamansa cikin kujerar still yana kallonta gannin amsarsa take jira

Da kula sosai ya ce" Ban tsane shi ba, ke kin san shi din shine mafi soyuwa a zuciyata a cikin yayana, ina yi masa haka ne dan ya ji haushi ya daina abinda yake yi, me amfanin kana aikata laifi kuma kana yi a idon kowa? Ai ko Allah ya Hanna ka ringa tonawa kanka asiri, gashi baya son danginsa, ban san me suka yi masa ba baya son su, ace du irin yadda HAJIA take da shakuwa da shi ba zai iya sonta ba? A kansa kadai HAJIA ke yin kuka a duniya ama fir ya kasa ganewa ya rabeta ko dan tsufanta?"

Kai HAJIA AMEERAh ta cire daga duban gefe ta maido kansa tana dubansa, a Nutse ta saki dan murmushi a tausashenta ta ce" Ka yi hakuri ka ringa duba furucinka a kansa, saboda mahaifi kake a wajensa , ko me yake aikatawa fatan shiriya shine ya dace ya fito daga harshenka, ka yi hakuri ka fi karfin zuciyarka domin baka sani ba abin ya fara fin karfin son ka ga ya dawo hanya ya koma abin birgewa wa zuciyarka yin daidaya da zuciyarsa"

A hankali ta ajiye maganar kafin ta dago ta saka idannuwanta tar cikin nasa ta ce" Me kake jira daga wajensa ? Ina ganin shi yana sara da duban bakin Gatari , da ace irin halayan da ake masa zai yi da an shiga uku, shin wani d'a za'a zagi mamansa yana tsaye bai dauki mataki ba? Fin karfin sa na yi shi yasa shi kuwa ya kaurace dan kar ya aikata aikin da za'a Dube shi da shi, me yasa bakwa masa adalci ne? Me yasa bakwa dora abinda yake iya ji a zuciyarsa kamar yadda kuke iya ji? , me yasa kuke gagawar yanke masa hukunci idan ya wulga koda bai yi tari ba?" Wannan karronma a hankalin ta ajiye maganarta sai dai dubanta na iya fasara daf take da tsinkewa

A Nutse ta dora da fadi " Yau da gobe nake guje maku, dan ba zan ware kowa ba, idan Ni na zamo takalmin takawarku shi a abu mafi daraja yake kallona, in ma me na aikatawa ahalinku wanda kai ake iya yafe maka Ni ake kallona a matsayin *AZAL* din da ta afko ahalinku da cikin da na ba kaina wace ba za'a iya hakuri a Dube Ni ba, shi yana dubana a mutun mafi daraja a duniyarsa, shin yaya kuke so yaron da kuke kiran uwarsa masifa shi ya zamo maku mai biyayya a gabansa? To ai koda ace shine shegen da muka yi Ni da kai ba zai taba fa......."

"AMEERAH!" Hon Bello Muctar Gali ya fada yana dagowa daga jinginar da ya yi hankalinsa na neman tashi zuciyarsa na bugawa, domin tunda suke da ita du irin abinda yake faruwa bata taɓa dubansa ta nuna bacin ranta ba, kai komai bata fadi bale har ta tado abinda shi ya birne yake kuma zaune da matarsa da zuciya daya da so da kauna Duda ita ya san ba lallai in ta iya manta baban abin da ya shiga tsakaninsu a zamanin samartaka ba, sai dai ga dukkan alamu abin na ranta har yau kunnayensa ke jiyo masa maganar dake daf da dauke nutsuwarsa

A hankali ta zuba masa ido kafin ta tari numfashinsa tana dan Bude lumsasun idannuwan da yaronta ya yi gado a wajenta tana kallonsa ido cikin ido a kausashe sosai ta ce " BELLO, idan maye ya manta uwar d'a ba zai yiwu ta manta ba, yayana da aka ciro a dakin tiyata aka nunan sun mutu ba zasu taba guguwa a zuciyata ba, ba zan taba mantawa ba!"
Sai kuma ta sasauta muryarta tana jingunuwa da jikin kujerar nan a hankali ta ce" Ina daukan zamana a ahali irin naku matsayin jarabawata ina kuma rokon Allah ya zamo silar yafewar laifin da na aikata, sai dai ka sani ina guje masu yau da gobe a kan D'ANA!, i love my love fiye da raina, ku kun san biyayar aure da shi ke rikeni ba dan bani da yadda zan yi ba!, Ni ce AMEERAH (GIMBIYA) ta DAMAGARAM, banbancin mai nisa ne!"

Daga nan ta yi shiru tana jin kanta na neman yi mata ciwo

Hon Bello kuwa sai ya rasa shin mamakinta yake ciki ko firgicin halin da take ciki? Lalle a yau an kaita bango, ashe itama tana iya nuna bacin rai a kan abinda ake yiwa Yusuf har haka?

Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya mike dan ya dauko mata maganinta da ya zamo kulun sai ta sha take kwonciya
Chapter 10 · 0% Book details