← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 117

Sashe 81

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kuma Hajia ta ce" Kamar yadda na fada maki, in dai zaman lafiya kike so da mijinki, ki girmama mahaifiyarsa, duk d'an halak ai inaga zai girmama baba koda ba shi ya kawo shi duniya ba ko AMNAH?, ki girmama ta, zaki ji dadin ta fiye da kowa a gidan nan, dan kuwa Ni sheda ce , ki tashi ki bi ta"
Hajia ta idashe zancen tana mata nuni

A hankali Mah ta dago dubanta ta sauke a fuskar Hajia,zata iya cewa ta jima tana yin sharar shanyen nan, domin lokuta da dama koda bata so bakinta ya fada ba idan tana yin fada da bada misali zata yi misali da ita ne a matsayin a yi koyi da halayarta....., abinda ke kanta a yanzu yanzu shine Hajia ta kasa yafe mata abinda suka aikata ita da d'anta ne,
da ace ta yafe mata, da ta dubeta tuni, da kuwa ta ji dadin rayuwa tare da ita

A hankali ta mike saboda zaman da ta jima tana yi, ta dan rage tsayinta a tausashe ta furta" Allah ya saka da alkhairi Hajia, mun tafi"

Hajia ta dubi Mah, zuciyarta na tsintsinkewa da lamarin sirikar Tata, lokuta da dama sai ta yi yunkurin yin wani gagarumin abin da zai shirya tsakaninsu sai ta rasa ta yaya? ta ina zata fara? bale a yanzu da YUSUF ke kan matsayin nan, takan yi tunanin idan har ta nuna wani abu daga ita din har sauran jama'ar zasu yi tunanin ɗan Yusuf ya zama sarki ne take neman sulhu da Mahaifiyarsa, ba zasu taba yi mata uzuri ba, a matsayinta Na uwar da tashin hankali ya sama rana tsaka a cikin kishiyoyi da miji da tarin makiya kan d'an da ya fi kowani yaro kokari da zafin nema a cikin y'ayanta, d'an da ita da kanta ta gama sakawa ranta cewar da izinin mai sama shine jagaban garinta, ya zo mata da gigitacen labarin da ya hargitsa tunaninta, ya kuma ja ya tsaya, ta ja ya ja , ta yi ta yi kan ya hakura da ita ya nuna gwara ya mutu da haka, duk irin tsatsauran matakin da ta dauka a kansa ya ki yin hakuri, karshema ya kamu da zazafan ciwon zuciyar da a yanzu haka emotion na dadi ko na wuya ke rikita masa lissafi har ya fita a hayacinsa ba? ba zata yi mata uzuri ta auna a kanta ba, ta tabata ko MAH sai ta fasarata , shi yasa take ta kai tubanta wajen Allah, dukda ta san cewar Allah baya yafe laifin da bawansa ya yiwa bawansa, sai idan bawan ya yafe, tana rokan sa ya bata hanyar da zata daidaita tsakaninta da *SARAKUWAR TA* ne.

A tausashe Hajia na duban Mah ta ce"

(RAUDA kin bar wajen gatanan tafe☹️)

morning alll......,

Azl 46
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

A tausashe Hajia na duban Mah ta ce" Allah ya hutar da Gajia Anmi MALIK"

Kunya ta ji ta kama ta, ta sake sada kai ta yi murmushi sannan ta mike ta yi gaba a nutse tana dan daidaita tafiyarta dan bata so ta bar AMNAH nesa sosai da ita

AMNAH kuwa, tana biye da ita ne idannuwanta na sake bushewa da tunanin dake cikin ranta, burinta daya ne kwal ya samu kanta ita kadai dan ta yi abinda zai bata damar Sannin Wacece yarinyar nan, domin ta daukarwa kanta alkawarin koda ace y'ar uwarsa ce jinni daya sai ta shayar da ita mamaki ta hanyar nuna mata kofa bata auri ƴaƴanta ba ita ba sa'ar yinta bace, bale ace tana auren MALIK!
Tana tunanin nan suka karaso Mah ta bude ta shiga tana salama Amnah na biye da ita

A lokacin Salima na falon Mah tana aiki da computarta, dan ta tarda RAUDA kicin ne su yi aikin tare sai ta same ta yau bata son magana, domin tana aikin ne ba tare da tana kula firar da take mata ba, shi yasa ta taho ta yi zaune abinta ta barta da yan kurumcinta

Da kula Mah ke amsa gaisuwar da Salima ke yi mata, ta dan ja tana tunanin inda ya dace ta kai AMNAH, a cikin dakunnan wajen

Ta so kaita dakin RAUDA, sai ta nufi dakin kusan na RAUDAR da ita a nutse ta saka ky din da Salima ta dauko mata a dakinta ta bude tana fadin" Bismillah, bari mu gani ko sai an sake gyara shi? na san dai ko jiya an yi gyare gyaren dakunnan dake rufe"

Salima ta fara shiga, ita kuwa Amnah ta yi tsaye a waje, dan ba zata shiga ba sai an tabatar mata wajen clean ne dan gaskiya ba zata iya shaƙar kayan mura ba

"Bismillah aunty Amnah" Salima ta fada bisa umarnin Mah

shigowa ta yi tana bin dakin da kallo sannan ya sauke dubanta a kan Mah, kamar yadda ta saba kallon mahaifiyarta tsai cikin ido ba wani risinawa haka ta dubi Mah din,dan bata san ita hakan Bama wani abu ne dake iya sakawa a ga rashin tarbiyarka ba kallon baba cikin ido

Da kula Mah ta ce" Ki zauna a nan , dukkan abin bukata za'a kawo maki, idan akoy wani abin da kike so ki sanarwa kannenki, ko ki sanar min, kina da bukatar kitso ko kunshi ne?......" Mah ta karashe tana sake duban kaffafuwan Amnah, dan da ace sun yi wani sabon da ya dace ta yi mata katsamandan a al'amuran ta, da tace da ita ki yanke faratunan nan ki tsaftace kanki ko dan sallar ki, sai dai a yanzu wannan yarinya mata take a wajen d'anta, matarma bakuwa, mai cike da abubuwan da suke boyayu a duniyarta

Itama kunshin dake hannunta ta bi da kallo, wanda bai jima da aka yi mata shi ba, domin mahaifiyarta bata barinta neman komai ta rasa a gidan nan, duk wani abin da zata bukata za'a turo mata ne kai tsaye, Mamanta ta fada mata kar ta yarda a ga kazantarta komai kankantarta dan a haka za'a nemi a rainata

kai ta girgiza tana sake duban Mah sannan ta nufi wajen bed din dakin ta zauna hankali kwonce, hakan ya sa Salima dan zarro ido tana kallonta , ita kuwa ba wani damuwa ta ce" A'a, bana son kunshi, ina dai son gyaran kai da mak'up"

Mah ta yi dan murmushi sannan ta juya ta fice

Tana fita Salima da ta gaza motsawa ta nufo ta da dan mamaki ta ce" Aunty Amnah, yaya zaki zo ki zauna tun Mah na nan tsaye a saman gado? har yanzu fa bakuwarta ce ke kuma hausawa sukan ce in dai da kunya y'ar halal har ta mutu tana jin kunyar sarakuwarta!"

Itama da mamakin tana kallon Salima, dan zata iya cewa a duniyarta tana mamakin Salima ainun, tunda ta san y'ar kishiyar Mah din ce, kuma a gaskiya sukan dan yi fira idan ta kama bale ba laifi tana girmamata sosai, shi yasa itama take yinta, da kula ta ce" Kunya? to meye a ciki dan na zauna?"

Salima ta dan dafe habarta, a nutse tana kallonta ta ce" Aunty Amnah, kar ki ce meye a ciki dan kin zauna, kin san ana girmama mahaifiyar miji, bale wannan din koda bata haifi mijinki ba ko a gari kika ganta zaki sada kai idan zaki yi mata magana Dan matar sarkin garinki ce fa, a irin yadda muke da girmama sarakuna tana da kima sosai a idannuwan duk wani mai mutunci fa"

"Ya Allah, Salima wai meye na yi na rashin girmamata? zama? to ai Ni Ko ubana ke tsaye ina iya zaunawa normal ne bale wace bata haifeni ba, Ni walahi mamaki kike bani Salima, matar nan kamar ba kishiyar mamanki ba, kina kallo yadda ta maida maki uwa baya a cikin gida ama ke itace abar ki raba? in dan kudin d'anta ne kema ai yayanki ne ina gannin kina iya takama da kudinsa ko? walahi ki farka tun wuri, kishiyar uwa ba zata taba sonki ba!" Amnah ta fada tana hangen wace ke neman izinin shigowa

Salima da ta yi mutuwar tsaye ce ta iya juyawa ta bada damar a shigo
Chapter 81 · 0% Book details