Sashe 73
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kasa zuwan ta yi, saboda bata taba aikata haka cikin hayacinta ba, sai dai kallonsa take yi tana murza yan yatsunta muryarta a raunane dan yannayin idannuwansa sun rikitata a hankali ta ce " Ka tashi mu je asibiti Please, ka tashi"
Nokewa ya yi yana kallonta ya ce" Na ki din, dan kawai yan lokutan da suka rage min su kare min ina barci, dan na tabata idan na je allurar barci zasu maka min shikenan na yi asara na tafi ba tare da na kalli fuskarki ba?, Please zo jikina, kin ganni fa, babu abinda zan iya yi maki koda a tsaye nake, zo in rungume ki, kin manta kin ce min idan muka yi aure zaki rungumeni da kanki, dan Allah ki ture kunyar nan da kike ji kin ji?"
RAUDA ta ji hankalinta na neman tashi sosai, a tsorace take kallon sa, irin yadda ya dage sai ta shiga jikinsa kuwa wata irin kunya ce ta gaba dabaibaye ta, kana ganninsa kuwa zaka tabatar da yana cikin matsanancin hali ne, dan haka ta rasa yaya zata yi masa, gaba daya ta mike ta ringa bincikar wayarsa a dole sai ta ga numbar likitansa , lokaci daya tana tambayarsa numbar likitan nasa? maimakun ya fada mata sai yace da ita dan Allah ta taimake shi ta yi masa kiran numbar Mah
shatakai ta tsaya tana kallonsa, sai dai gannin ya ja wani irin numfashi kanta ya sara ta shiga saka numbar Mah , a lokacin kuwa Mah din sunna hanya dan sun ajiye Atu kennan za'a nufi gida da su wayarta dake hannun Salima ta yi ta ringing
Salima ta duba mai kiran, tana ta sake dubawa kamar numbar Abdallah dan haka sai ta daga tana mikowa Mah ta ce" Mah kamar numbar Abdallah"
Mah ta amsa tana fadin" ABDALLAH kuma?, hello asalamu alaikum"
RAUDA ta yi iya yinta dan ta yi magana sak ba tare da ta yi kuka ko gargadar murya ba, ama abin ya faskara
A hankali ta furta" Amen wa alaiki salam Mah, Rauda ce"
Mah ta yi saurin fadin" Babu, kuka kike yi? lafiya?"
RAUDA ta sake juyawa tana kallonsa, a hankali ta ce" Mah, Abdallah ne, bashi da lafiya kuma yace a yi kiranki wai"
Mah ta ji gabanta ya fadi, tana kallon direban YUSUF ta ce" Mu koma gidan baby, baby ganinan ki zauna ki daina kukan ganinan in sha Allah"
RAUDA ta ja numfashi sai kawai ta fashe da kuka ta juya tana kallonsa lokaci daya tana sakin wayar nan ta koma saman gadon a hankali ta karasa inda yake kwancen a hankali ta bude hannayensa ta shige jikinsa, jikinta na rawa ta rintse idannuwanta, muryarta na rawa ta ce" Ka manta, ka ce min RAUDA in dai ina raye, ba zaki yi kuka ba, Nine mijinki, Nine yayanki, Nine komai naki, to menene kuma kaima kake wani abu kamar wanda zaka bar Ni? shikenan Ni duk wani makusanci nawa sai na rasa? Abdallah, kar ka yi min haka Please"
Murmushi ya yi, a hankali ya sake rungumeta a jikinsa, ama bakinsa ya gaza furta koda a ne, dan sosai abin ya fara motsawa, sai dai yadda yake jinta a jikinsa ya zame masa wani nau'in salama a cen cikin zuciyarsa, wato zuciya da abinda take so
A bangaren Mah kuwa direba na tuki kamar zai tashi sama, ita kuwa tana tambayar Salima da tace ko ciwonsa ne ya tashi cewar wani ciwo fa? wani irin ciwo?
Salima ta yi tsuru tsuru, dan RAUDA ta yi mata magiyar kar ta sanarwa Mah a lokacin da Salimar ta san cewa yana fama da matsanancin ciwon zuciyar da likita yace idan har bai yi gaggawar zuwa aka cenza masa ba tabas kowani lokaci yana iya mutuwa, shi kuwa yace ba zai yiwu ya je a Barka shi a cire masa zuciyarsa ba a saka masa wata bayan a cikin kashi dari daya ke rayuwa da irin aikin nan, salon ya yi biyu babu, a lokacin nema ta ji matsalarsa ta rashin haihuwa kuma a ranar ne ta gane Rauda wannan ba damuwarta bace dan itama burinta kennan rashin haihuwar
"Salima?" Mah ta fada a lokacin da motarsu ta shiga katon get din gidan tana kallonta
Salima ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Mah, yanada ciwon zuciya ne, wanda ya kai matakin karshe, shine nace ko shine ya tashi?"
Dif Mah ta yi tana kallon Salima, ciwon zuciya? matakin karshe? subahanallah, kuma yake zaune bai je asibiti an masa aiki ba?
kasa cewa komai ta yi ta bude motar ta fita har tana buge kafarta saboda tunanin halin da Rauda ke ciki ita kadai da shi, domin ko masu aikinta ba'a kawo ba Bah yace wai sai ta yi sati a gidanta an kawo masu aiki
Salama Mah ke yi tana kiran sunnan RAUDA, hakan ya sa RAUDA mikewa a hankali ta sake juyawa ta kalle shi, sai ta ga ya sakar mata murmushi kasa kasa ya furta" zaki iya kama hannuna na dan daga?"
RAUDA ta gyada kanta, a nutse ta dauki pilow biyu ta jinginar masa a jikin bed din sannan ta kama shi da kyau ta jinginar da shi a jikin pilow din ta gyara masa bargon sosai a kaffafuwansa, shi kuwa yana Binta da murmushi a hankali ya furta" Wannan kashin turaren naki akoy dadi, kin ji shi a hannayena har yanzu"
Ita dai bata tunanin kanta na iya daukar raha ko gane rahar da yake yi mata , har sai da ya sake fadin" Ki sanyo su nan Please" Sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fice
Tana fitowa ta ga Mah tsaye, Salima a gefenta, ga dukkan alamu ita suke jira,
ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta karasa jikin Mah da ta mata alamun ta zo
A tausashe sosai Mah ta ce" Jikin nasa ya tsananta ne kike kukan nan?"
Da kyar RAUDA ta iya budar bakinta, tana haki tamkar zata summe ta ce" Mah, Ni dai na ga yana ta wani iri, wai yace a kirayeki"
Mah ta furta" Ok,ki ce masa na zo"
RAUDA ta sada kanta ta ce" Baya iya tashi fa, da kyar yake magana, Mah baya iya tashi shi yasa yace ki je"
Bah ta lumshe idannuwanta saboda gabanta da ya fadi
Da kyar ta boye damuwarta ta mika hannunta ta amshi wayar dake hannun Salima ta ce" Bari na sanarwa babanku dan ya sanarwa Hajia kar ta ga mun jima"
Kai Rauda ta gyada, sannan ta karasa wajen Salima suka zauna Salimar na rike da hannunta tana fada mata ta daina kukan nan in sha Allah ba komai bane zai mike haka masu ciwon zuciya suke
Gannin ta kasa samun numbar Bah ana ce mata a kashe sai ta yi kiran ta Hajia, wace jimamin abinda take ciki ya sakata kasa gane jimawar da su Mah din suka yi, tana cen tana ta neman mafita a falonta ta daga kiran a tausashe ta furta" Andiya, kin dawo ne?"
Mah ta sauke ajiyar zuciya, a tausashe ta sanarwa Hajia basu dawo ba, har sun kama hanya kuma ga abinda yake faruwa
sosai hankalin Hajia ya tashi, ga tarin mamakin Mah sai ta ji tana fadin" Bari in nemo Bellon, idan ban ganshi ba kuwa zan sa a min iso wajen Malik dan na zo , kafin nan ku yi kokarin sada shi da likita, Allah ya bashi lafiya"
Mah ta amsa jiki ba karfi ta datse kiran, sannan ta dubi su Salima ta masu alamun su yi gaba
gaba na baya suka shigo dakin, a lokacin ya saka abinda yake tarawa idan yana tari ya gama yin tarin kennan yana goge abin jinnin da ya bata masa baki ya yi gaggawar cirewa daga bakinsa da sauri ya so boyewa, sai dai karfin jikinsa bai bashi dama ba ya saki abin a kasa, gashi du yadda ya so dagowa dan ya dauke ya kasa, hakan ya sa RAUDA da ta zubawa abin ido karasowa ta duka ta dauka ta bude
kusan a tare suka juyo suka zuba masa ido, Mah hankali tashe ta karaso tana fadin " Subahanallah, jinni ne daga bakinka?"
RAUDA kuwa sai ya kai zaune a nan kasa ta zuba masa ido, gannin yadda ya sada kansa , kunya ce ko menene? ya dai ƙasa kallon Mah ido cikin ido har sai da abin ya lafa masa ya dago yana duban Salima a hankali ya ce" Sister, Please daukowa Mah kujera Gatacen, nd ki bani wancen akwatin dake saman dayar kujerar"
Salima ta juya ta cika abinda ya ce din jiki ba karfi
Akwatin da aka ba Mah ta bude ta ringa fitar da takardu na dukiya daya cikin daya cikin daya, da wata takarda mai dauke da code na banki, da ky cike a akwatin, sunne suka saka akwatin yin nauyi
sunnan dake saman kowace takarda ya sakata dagowa, itama zuwa lokacin nata hankalin ya fara matukar tashi yana kallonsa ta ce" me kennan?"