Sashe 95
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai wannan ka barta kawai, ku ku tafi kawai Ni kam sai na ga ta nutsu kar aje in bada baya ta halaka kanta ko ta tarda su ta yi wata barnar da za'a kasa gyarawa, bata ganewa ne Ni bayan ubanta ya aureki na haife su ai ya taba gwadawa, karshema ya zama in dai ba da Ni ba baya iya anfanar kowace mace, ita ba zata bi abubuwa a hankali ba sai ta dagawa mutane hankali a kan banza, yarinyar cen kuwa da kike gani duk inda ta fito dama akoy wata a kasa tsakaninta da shi dan ban san ubanda take nema a wajen da kika ce wajen sirrinsa ne da damamen Wando ba, na jima da ce maki ki yi kokari ki bashi abinda yan waje suka sabar masa ama kamar ba mace ba kina dari dari, idan ita ke bashi ai shikenan ko me zaki mata ta shawo da ke! shashasha Amnah ban san idan ina fada maki abu inda kike sauraro ba, ki yi min shiru da ihun nan na jijika maki Wadinnan bita zaizai din ki yi duka yadda akace ki yi na kuma dafa maki na dafawar ki ci, ki kashe wayar ki saboda yan tsegumi ki barta sai mun fitar da yarinyar kya kunna, ka ga Habu ku je kawai dan a yi tunanin nima na tafi ku je ta yiwu in kwana a nan"
Dayar abokiyar tafiyar kam kasa cewa komai ta yi, dama ita din bakuwa ce a duniyar sharafin nasu, sai take kallon su a bakin sani cike da tunanin anya kuwa igiyar nan da ta riga mai kwari ce? domin ga shiga jikin Hajiar ne dan ya samu itama ta gagari zama da kishiya, sai ga wani abu da ya wanzu mai rikitar da kwakwaluwa
ita abinda ya fi bata mamaki shine ire iren zantukan da bokayan nasu suka ringa yi masu yanzu yanzu , wajen boka biyar suka je, kowane ya yi tsubace tsubacensa aka zuba masa kudi ya bada maganinsa da bayanin abinda za'a yi da shi
a binciken bokayan basu ga maganar kishiyar bane bayan ana nufin su din sun san gaibu? (Astagfrullah), To kennan su dinma makafin ne ta yiwu fiye da sauran al'umma? kuma a furucin Hajiyar ta sake shiga a cikin tunani, da gannin tabas ta riki rubabiyar igiya, domin abin kamar na mahaukata? Shin a me ta dauki gidan sarauta ne? duk inda take tunani sun shalaketa, walahi in me take tunani sun fi ta, sai dai a daidaita zama a dubi junna dan a zauna lafiya, ama ita nan har mai nema ce?......., mutumen dake zaune a gidan sarauta kansa sai ya baka abubuwan tsari masu yawa bale SARAKAI!, kofa yake shi tsafi ai kuma gaskiyar mai shi, ama ita tana tsoron irin yadda ake nuna har yanzu Amnah ta gaza zama cikakkiyar mace mai yanci da takama da aure irin na kowa ya saka take tunanin anya ba hanyan biri ne ake yi a tsakanin junna ba? ....Uhum, ta yiwu wanda suke dako ya jima da gannin makwoncinsu, dan haka ta mike da sauri tana karfafa masu gwuiwa ta fara ficewa dan ba zata so wata fitina ta haɗa su da YUSUF ba, duk wanda ya san shi a da, zai kiyaye shi a yanzu!
Tunda ya tafi sallah RAUDA ta sake kuntata zuciyarta da tunanin eh lalle auren nan ba dai ita RAUDA ba
To mana ai kowama zai ce ba dai RAUDA ba, Yaushema ta rasa miji harda wani zai kuma amsa sunnan mijinta?
burinta ta koma makaranta ta fara sana'a mai kwarin gaske, shikenan. Sai a ce haka?, me kennan? ya sameta a bagas walahi in dai a haka ta zama matarsa to tabas ta gama zubewa har kas
Idannuwanta ta rintse tana sake daukan damarar yaki da shi, dan YUSUF ba shine mijin da take mafarki ba, ita ai Bama ta son mai mace, kuma bata son namiji mai takama!
Mikewa ta yi tana kabe jikinta kamar wace ta yi dati ta juya ta bude kofar a hankali ta fice ta nufi hanyar baya dan in dai Allah ya taimaketa a bude ta nan ne kawai zata iya guduwa ba tare da an hannata fita ba, dan ta sani in dai ta wajen babbar kofar falonsa ne babu inda zata je ba tare da izninsa ba
Da sauri ta kama kofar part din Mah ta bude ta shige har tana waiwaye ta sauke ajiyar zuciya da sauri ya nufi dakin Mah ta tura ta shige ta maida kofar ta rufe tana sake sauke ajiyar zuciya ta juyo da nufin yin salama idannuwanta suka shiga cikin na Mah , hakan ya sa ta.........
Happy juma'a yan uwa
Ta juyo da nufin yin salama idannuwanta suka shige cikin na Mah, Hakan ya sa ta ja da sauri ta tsaya tana kallon Mah din ta kasa yin salamar
Mah ta bita da kallo daga sama har kasa, yannayinta ya ganar da ita ta ji abinda ya faru, dan haka ta dauke dubanta a kanta ta idasa zama saman kujerar falon tana fadin" Inaga a fitar baby an koya mata rashin salama!"
Da sauri ta kai hannunta tana shafa fuskarta, sai kuma ta karaso tana cire takalmin kafarta ta haye saman kafet din tana dan murzar hannayenta muryarta a rarrabe ta furta" Mah, ina ina yini, ina gajiya"
Mah ta sake dagowa ta biya da kallo tun daga sama har kasa, a tausashe ta furta" Lafiya alhamdulilah, ina kika baro tufafin ki?, wannan din na waye? a ina kika saka? kuma waye ya kawo ki?"
RAUDA ta ringa raraba ido, a hankali ta ce" A gidan Atu ne da na je na cenza, kayanta ne dan zan yi girki, to kuma muna fira yace ace kin aiko wani , shine na zo ban san shine ba, sai kawai ya kawo Ni nan din"
Mah ta sake tsare fuskarta da kallo ta ce" waye yace din?"
RAUDA ta sada kanta, a hankali ta dago tana kallon Mah ta ce" shi Yayanmu"
Mah ta gyada kai, sai kuma ta yi dan murmushi ta ce" Ok, je ki yi wanka ki cire tufafin nan ki same Ni a dakina"
RAUDA ta gyada kan itama
har ta juya Mah ta ce" Baby?"
Da sauri ta juyo gabanta na dan faduwa
Mah ta ce" Me zaki ci in dafa maki?"
RAUDA ta sada kanta tana jin wani irin zabi na sake ratsa mata jikinta dangane da Mah
A raunane ta ce" Komaima zan ci Mah"
Mah ta gyada kanta ta sake mata alamun ta je
Tana tafiya Mah ta mike ta nufi bangaren Hajia
Ta sameta zaune tare da Nana da y'ar gidan Nanar sunna maganar da kana gani zaka gane ba ta dadi bace
Ba tare da ta nuna wani abin ba ta gaisar da Hajia, sannan ta juya dan komawa
Kamar daga sama ta ji Nana na gaisheta, kafin ta rufe baki y'arta ta gaisheta itama
Dakatawa ta yi ta juyo tana kallon su, kamar wace ke son gane in su din mutane ne ko ba mutane ba a zaune, sai kuma ta dan dauke dubanta ta wuce dan har ga Allah bata yarda cewa ita ake gaisarwa ba, ko kadan
A raunane Nana ta kalli Hajia ta ce" Hajia , kin gani walahi Ameerah ce bata son zumunci da Ni, Ni a yanzu bani da abin fada sai dai na ba kowa hakuri, ama dan Allah ki saka baki a cikin lamarin nan , ki duba ki ga yarinyar nan a halin da take ciki, Hajia walahi Bama barci, ance aljannu ke damunta , ance jifa ne, Hajia ga lamarin YUSUF da ta kakabawa zuciyarta, Hajia itama fa jikar ki ce, kuma tana daya daga cikin jikokin ki mafi soyuwa a zuciyar ki, ama sai ki kyaleta ta shiga wani hali a kan abin da kin sani sarai kin fi karfinsa a wajen iyayen YUSUF? shi kuwa idan mahaifiyarsa tace ya yi abu ko meye yi yake yi Hajia, ya'ya za'a yi ace an karra daura masa wani auren tana raye ba da ita ba, dan Allah Hajia ki ceci jikar ki"
Hajia ta sake duban DAYANA, wace ke zaune gaba daya kamar ba ita ba, Dayana ta bushe kau, sai bakin baki da kwala kwalan idannuwa, kana kallonta ka ga zaburariya,
Kai ta girgiza tana kallonta ta yi murmushi ta ce" kin ga, Ni ba zan yi masa wani auren hadin ba kuma, wanda na yi masa ya isa, a gabanan idan yana da damar karra wata sai dai zabinsa, idan har ya yi niyya ya daidaita kansa da ita ba zan hanna ba, in kuma ya ki , ki yi hakuri,......da ace zaki ji shawarata da na baki Nana, kin ga Dayana fa a yanzu ba wai maganar aure ne ya dace a yi mata ba, ya dace ta je ta ga likita tun daga kan na lafiyar jiki, na ƙwaƙwalwa, da na harkar shaye shayen nan, idan Allah ya sa ciwonta bai yi nisa ba sai ki ga ta zama mutun ta yiwu idan ta dawo hayacinta ki ga Bama zata so shi ba, ama a yanzu fisabililahi ko ke aka ce a ba RISLAN irin haka ai kya ce a'a bale YUSUF fa sarki ne, Allah ya sanyaya ko menene ama a ringa yi ana yin abinda hankali zai dauka, Ni nan da kike gani wai ki ce na kasa yafe maki ko me? haba yaushe zan tsaya ci gaba da rike ki a rai bayan Ni na haife ki? ai da kin jima da watsewa, a kulun idan na yi sallah sai na kama sunnayen ku gaba daya da na haifa da wa'inda na rike na rokar maku gafara da shiriya da kariya da kyakkyawan karshe da sakamakon aljanna, ba zan ware ki ba saboda butulcin ki, sai dai zan yi takatsantsan dan kuwa Nana walahi ban yarda da ke ba, ina sakawa raina kina iya cutar da Ni mahaifiyar ki, tunda kika kwashe lokaci mai tsayi kina cutar da d'an zumun ki, ku je kawai Allah ya sanyaya"