← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 117

Sashe 25

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rikice ta ce" Farisa fada nake yi dan ya daukar min kudi, ama ke kin san ina son babanki ko "

Farisa ya tabe baki ta bi bayan redion da aka rotsa ta dauke ta yi dakin Rauda da ita, dan tana so ta je ta dan bincika da wuri wuri ko ta samu na samu ta dan adana gefe kafin Raudar ta dawo, fatanta Allah ya sa ta bar wayarta da kuma jakar kudinta, kai da itama ta kile dan walahi tana ji tana gani zata ce itama saurayinta ya kawo mata iphone din, ai ba ita kadai take da damar yin saurayin ba dan wulakanci!

Tuki ne ya yi mai gaggawa, hankalinsa a kan Mahaifiyarsa dake ambaton sunnan yarinyar da yanzu yanzu ne ta ji sunnan ama kamar wata wace ta saka mata shi da kanta

Sunna karasowa ya fito dan sake daukan yarinyar ya kaita ciki kafin ma a kawo kujerar dora marar lafiya ko gadon, sai ya ga Mah ta cire mata hijabi ta cire mata ribom sai faman son tahsinta take yi tana jimke da hannunta da dayan hannun kuwa tana dan shafa gefen fuskarta a hankali tana fadin ta farka mana

Kansa ya dauke a kanta ya ja gefe har aka zo aka kamawa Mah aka dora yarinyar aka fita da ita aka yi ciki da ita

Wurin zama Mah ta samu ta zauna tana dafe kanta da hannayenta bibiyu

A nutse ya karaso ya duka gabanta ya saka nasa hannayen yana cire nata yana kallonta ya ce" kamar kin saka damuwar wace bakima sani ba da yawa a ranki Mama, Please ki sanyaya ba komai fa, zata farka ne yanzu sai mu maidata gidansu mu je gida ki huta"

Bayan zuba masa ido da ta yi sai ta samu kanta da cewa" Mu maidata? YUSUF mu maidata fa ka ce?"

Idannuwa ya zuba mata yana son gane me kennan

A sanyaye sosai Mah ta ce" matar da muka bari a gidan cen sam bata cencenci rikon yaro ba, ko nata ba zata iya ba tarbiyya ba bale wannan da take kishi da ita, Yusuf cewa fa take yi wai idan bai dawo ya kawo mata kudinta ba itace ajalinsa kuma itace ajalin yarinyar nan , Ni ban san tsakaninsu ba, ban san me ta yi mata da zafi har ta tsaneta haka ba, ban kuma san ko inada hurumin shiga wannan rigimar ba, abu daya na sani shine daga nan yarinyar nan zata je ne gidana kuma a gobe gobe zan shigar da karra dan kar matar ta rigayeni, Yusuf ai dadinta muna da sarakai masu adalci da hukuma tsayayiya, kuma a yannayin yarinyar cen ta yi shekarun da ta isa zabarwa kanta inda take son zama, Ni dai ina ji a raina kamar taimako ne zan yi, kuma kamar idan na yin Allah zai dubeni da idon rahama nima ya yafe min kura kuraina "

Idannuwansa ya lumshe a hankali , bai saki hannunta ba a sanyaye ya dora gefen fuskarsa a tafukan hannayenta yana jin dumin hannunta yana aukawa a tunani
Lokuta da dama idan ya zauna da mahaifiyarsa sai ya ji zuciyarsa tana girgiza , hankalinsa na tashi da nasa shima laifin
Mahaifiyarsa bata taba daina neman afuwar Ubangiji ba kan abu daya tal da ta aikata wanda bayan aikatashin ta rike abinta har ta haifi abinta kuma ta so ta raini abinta Allah ya amshi abinsa
Ama a haka a kulun idan ta budi baki zaka ji tana tsoron haduwarta da mai sama kan wannan abu, to ina ga shi jama'a?
Ya mayar da mace abin shigarsa dan samun nutsuwa
Yana yi yana hawayen bakin ciki da tashin hankali
Bai rasa abin ajiye hudu idan yana ra'ayi ba, ama ya kasa tsayawa waje daya bale ya ajiye din, ya yi nan ya yi cen da ransa
Kwarai shi din ya kasance mai aikata aiki mai munin gaske, wanda idan ta ji wa'azi wani lokacin yakan kasa rintsawa

A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya dago idannuwansa yana kallon mahaifiyarsa
A ransa yake aiyana 'ni kuwa zan tsaya maki har sai kin kai ga cikar burinki dan samun nutsuwar zuciyarki Mah '

"Sir, ta farka, ama ta ki tsayawa mu mata allurar barci duba da bugun zuciyarta ya yi yawa ko ma samu ya dan daidaita mu yi mata gwaje gwajen da ya dace dan mu dorata kan traitment"

Mikewa ya yi , Mama ta bi bayansa suka nufi dakin
Budewa ya yi ama ya ki shiga sai Mama ce ta shiga sannan ya bi bayanta ya tsaya yana kallon Mama

Gadon Mama ta karasa da sauri ta zauna ta dago kan Rauda ta janyota ta rungumeta a jikinta da dan karfin da ya saka Rauda dawowa duniyar mutane har ta dan saurara daga rizgar kukan da take yi hancinta na shakar sansanyan turaran ruwan mama kunnayenta suka shiga jiyo mata kalamai a sanyaye kamar haka" me yasa zaki rikita kanki har haka ne? Kina son kamuwa da wata cutar ne? Waye ya fada maki ya rasu ne? Da ace sun kashe shi da wahala su kawo wayar nan, ina mai kyautata zaton yana raye sun yi haka ne dan su rikita mutane ya zamo da zarar sun yanke kudin da suke so a basu dan a amshe shi, kuma kin ga Honorable ya amshi wayar yanzu haka da ya ajiye mu ya tafi wajen commisiona na police dan ya masa maganar, Haba Rauda sai kace ba musulma ba? Koda rasuwar ya yi sai ki kasa yin tawakali ne? Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi RAUDA, idan har Allah ya so zai dauke maki kowa ne ya barki ke kadai, saboda wannan sai ki kashe kanki kema? Hana Rauda ki yi hakuri kin ji?"

Tamkar wace Mama ta tuno mata da wani gibi, ko kuwa kalmar hakurin daga bakin uwa ne bata saba ji ba ta ji a yau? Ko rungumeta a rarasheta ne bata saba samu ba? Abin dai ya shige mata zuciya har ya saka ta dago idannuwanta ta zubawa fuskar Mama mai dauke da ni'ima da haske mai daraja kallo kafin a hankali ta fashe da kuka tana saka hannayenta a hankali ta rike na Mama ta kai kanta a hankali ta ɗora saman kirjin Maman tana sake riƙe maman tana kuka irin na cikin makogwaron nan mai zafi da ratsa zuciya muryarta na sarkewa ta ce" Dama iyayena da kanaina sun rasu, shine kawai gareni sai Abdul, shine kawai gareni , su ne kawai dalilin da yasa nake tafe da karfina, idan na rasa su Ni na san Bani da karfin dazan iya jurewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, dan Allah Hajia ku taimakeni a samo min Abanmu, ko nawa suka yanka min zan biya su bani shi, ki nawa suke so zan basu Ni dai su bani shi"

Mama, tausayi, tashin hankali, mamaki duka sun hadu sun rufe mata zuciya, haba koda ta ji ta san wannan kam da wahala idan ta haɗa jinninda yarinyar irin yadda ta ringa jaza mata alkaba'i, haka kuma jin iyayen yarinyar duka sun rasu sai ya sake daga mata hankali, uwa uba kuma jin wai ko nawa ake so zata bada, aikin me take ne?

Shigowar docter da baban file a hannunta ya saka Mama bada hankalinta wajen docter, har zuwa lokacin kan Rauda a kirjinta tana dan dadabata a hankali, Yusuf kuwa yana tsaye ne yana sauraronsu

" wannan ba itace aka kawo jiya ba? " Docter ta tambaya

Mama ta tabbatar mata itace

Docter ya fita , jim kadan ya dawo tana sake bude takardar hannunta ta ce" To ai a jiya duka abinda ya dace na gwaji mun mata, sai dai idan kunna da bukatar a sake wasu to, dan jiya sir yace a mata komai dan lafiyarta"

Murya a shake sosai Rauda ta ce" Lafiyana kalau, gida nake so na je, Lafiyana kalau "

Mama ta dago daga kallonta ta kalli YUSUF dake tsaye bai ce masu komai ba, a tausashe ta ce" Eh yanzunma summa ne ta yi shi yasa muka dawo saboda wani abu da ya daga mata hankali, idan ba damuwa sai mu juya gida ?"

Likitar ta karaso ta fitar da abubuwan aune aunenta ta shiga auna RAUDA, wace lebenta ya yi Jajajir, hakama saman hancinta da wajen idannuwanta du sun kumbure sosai hakan ya sa da kyar take daga idannuwan , leben kuwa sai haske yake yi na abin kukan da ta ci

Da kula sosai likitar ta ce" kunna iya tafiya Madame, ama a sayi wannan maganin ta ringa shan daya idan zata kwonta na tsayin sati guda saboda bugawar zuciyar nan, kuma ta yi kokari ta cire damuwar dan yawan yanke jiki a fadin nan daga nan ake haduwa da mugun hawan jinni mai naci, Allah ya bada lafiya"

Daga nan ta yi gaba da kayan aikinta a hannunta

Mama ta dubi Rauda bayan ta dago kanta a tausashe ta ce" Kin ji abinda likita tace ko? Ki daina kukan hakanan, mu je gida ki huta za'a ganshi kin ji?"

Shi kam mamakin mama ya fi komai damunsa, su mata me yasa suke da saurin sabo? Haka kawai daga gannin yarinyar sai rungumeta take yi tana faman neman dagawa mutane hankali a kanta? Kai shi kam bai san me zai ce ba kam, ama Mama akoy rigima Allah kuwa, meye hadinta da wannan ne? Shi ba abinda ya bashi haushi sai jadadawa da take yi wai ko a je ko nawa ne zata biya? Shin aikin uban me yarinyar take yi da bata jin kunyar kowama ya ji? Kai subahanallah ashe rashin jin maganar mace haka yake da kayan haushi? Shi haushima take bashi kamar ya buge mata baki yake ji idan tace din nan ko nawa ne zata biya, aikin banza aikin wofi yarinya tunda ya santa cikin kaya kaya take? Shirme kawai!
Chapter 25 · 0% Book details