← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 117

Sashe 101

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido suka karra zarrowa, kamar an juyar da dubansu suka kalli RAUDA wace itama ta zarro nata idannuwan jin wata rantsatsiyar karya tana kallon Amnah da yannayin mamakin nan a ranta ta ayana' ok, na zata ai gaskiya za'a fada har na tsorata, tunda karya kika zaba fine'
A fili ta ce" Ni wai kike nufi aunty Amnah? innalilahi wannan jikin naki duka to da me? ina Ni ina ke aunty Amnah da zan iya ko dukan ki ko me? innalilahi wannan me ya same ki haka?"

Ido ya zarro lokaci daya ya kai hannunsa wajen bakinsa a hankali ya furta " Lah "
Ita kuwa Amnah sai ta ji kamar zata summa ɗan tashin hankali, mikewa ta yi da sauri ta shiga dage abayarta har wajen cinyarta da duwawunta hankali kwonce ba tare da ta yi tunanin hakan wai wani abin a ji kunya bane a gaban iyayenkama bale sirikai, ita dai burinta su yarda da abinda ta fada tana duban RAUDA ta ce" Kar ki raina min wayo kin ji, kin yi kadan na maki karya kin ji? kina nufin du abin nan da kika min baki san kin yi ba? to ko aljannu gare ki baki sani ba? wannan ai karyar banza zaki yi munafuka kwarariyar yar iska.........'"

"kin ga, Amnah ke, zo nan zauna, kuma ki kiyaye wasu furucin a nan dan ba zan dauka ba!" Hajia ta fada da karfi, hakan ya sa Amnah zuwa ta zauna din sai kumbura take tana kallon RAUDA tana harare harare

Hajia ta dubi RAUDA ta ce" RAUDA kin san wani abu a kan abinda take nufi? kin doka mata karfe sannan kika shamaceta?"

RAUDA ta girgiza kai tana kallon Hajia sannan ta mayar da kai ta soke, a ranta tana ayana' A'a kam , ban rotsa mata komai a kai ba, kuma ba fadan shanmata bane tana kallona ina kallonta kuma belt din wandon jikinta ne ai na tatafka mata sai dan marinta da ba yi!'

Hannu ya sa yana shafa gemunsa yana kallon makaryata biyu a gabansa, kuma matansa abinsa

baki ya dan cije yana kallon RAUDA da ta soke kai, ko shi da ace ba shine ba idan ya kalli wannan innocent face din ba zai taba cewa zata aikata ba, sai dai ga shima shedar ta aikata din a jikinsa fa, kuma jira yake alkaliyar ta nemi Shedu zai gabatar da sheda tabas!

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tana dubansu a tausashe ta ce" Yaushema daren ya yi bale har a kai loma a hanci?, Ni baban abinda yake bani tsoro gani nake yi kamar ja gaban da ya dace ace ya ja gaba a lamarin gidansa bai damu da gidan ba"
Ta karasa fada a tausashe tana sauke dubanta a kan MALEEK
A hankali ta ce" Ka yi hakuri Allah ya ja da tsayin rai, komai daga farko ake farowa, kuma komai girman mutun da darajarsa in dai magabantasa na raye dole za'a ringa shiga huruminsa koda baya so,"
Ta sake ajiyewa tana kallon sa, a tausashe ta ce" Koda da zabin da kake hange a duniyar ka a nan gaba, dole ka kiyaye yanzu saboda gobenka, MALEEK ya zama wajibi ka dubi gidanka komai girman abinda ke kanka ka basu lokacinka ka daidaita fitintinnun dake tashi mararsa ma'ana ka sauke dukan hankin dake kanka nasu sannan ka zame masu kariya na zama a rayuwar duniya!"

Ta karashe tana kallon Mah, wace ita dinma shi take kallo, kuma sun ga ya sada dubansa alamun dauka yake yi maganar da ake yi masa
Hajia ta dawo da dubanta wajen AMNAH, a tausashe ta ce" Haba Amnah, ko me yake faruwa a tunanina mu zaki fara gani idan kin ga ba'a yi maki adalci bane zaki nemi iyayenki, ....domin a sanina idan iyayen mace suka shiga lamari ya bace ne, ko ba haka ba?"

Amnah ta kalli Hajia, ita idan ta kalli Hajia tsoronta take ji a ranta, bata tunanin zata iya wata fira da tsohuwar nan dan tsoro take bata

Hajia ta ci gaba da fadin" Zaman kishi muka yi da mata kala daban daban a rayuwa, ba wayonmu ko dabarar mu suka kwace mu ba, domin an yi zamanin da mu da miji sai ido, muna ji muna gani miji ya fi karfinmu dan a lokacin ya auro mana shu'umar da ta sa ya dawo gannin munin mu, to idan zama ya yi zama dama an yi haife haife da sauransu kai da miji ai sai kyautatawar yau da gobe, shi kuwa yayi nasa rawar gannin ta hanyar nuna diyauci da darajar da iyali, ama ba wai ci gaba zai yi da gannin mahaukacin kyan nan naki da kike takama da shi ba , komai kyan naki, ki dauki misali a kankin kanki, zaki ga kina son wani abu ki siya, kafin ki siya irin zumudin da kike yi da tunanin idan kika samu ai shikenan kin gama siyan wani abin kuma ɗan wannan din karshe kennan aka baki, sai ki samu ki siya, a hannunki fa abin yake zaki ga wani lokacin ko sati bai cika ba kin rage zumudinsa, wani Sa'in kuwa kikan dauki watanni kamar biyar kina daukinsa, daga baya zai zamo abu da yake da daraja sosai a wajenki kike rike da shi kam da kam, ama ba wai wanda ya fi kyau ko ya fi birgeki ba, idan da zaki samu wani siya zaki yi ki karra ba tare da kin bada naki ba, Amnah haka rayuwa take tsakaninmu da maza, ke matar farko idan har baki iya takunki ba sai kin rasa wannan babar darajar da muke da ita kina ji kina gani, da wannan nake baki shawarar ki yi hakuri, ki iya kawar da kai, ki koyi halaya na manya, ki kasance mai dauke da darajar da mijinki zai rike ki taf, da kishin ba wani ke wato rabuwa da ke, koda ya ga wace ta fi ki a idannuwansa, ta haka zaki fi jin dadin gwagwarmayar rayuwa da rigingimun yau da gobe lami lafiya kin fahimta? ki yi hakuri ku zauna lafiya ke da mijinku da abokiyar zaman ku"

Ta karashe tana kallon RAUDA, wace har yanzu kanta ke kasa,
ita fa har yanzu gani take yi ko tsokanarta MALEEK ke yi dan Allah? wannan abar tausayin me ta sani baiwar Allah harda za'a ce ta daki wannan da idannuwanta ke kiririta?
Sai ta samu kanta da fadin" Zo nan , taho nan in ji"

RAUDA ta dago a hankali daga jikin Mah dan tun dazu Mah ta sa ta dawo daf da ita, ta kalli Hajia ta ga eh da ita din take, dan haka ta mike a hankali ta karasa ta zauna daf da Hajia, Hajiar kuwa ta kama hannayenta tana kallon fuskarta ta kai hannunta wajen fuskar Tata ta ce" meye wannan idon ya yi jajaja ko baki yi barci bane?"

MALEEK ya sake duban Hajia da kyau ya kalli RAUDA itama, sai ya mike yana tsintar dan fruits din tunda da wahala in ya samu abinci kafin ya fita yau kasa kasa ya furta" To ai shikenan Ni na wuce tunda ba'a bukatar shedu"

RAUDA kuwa a sanyaye ta ce" na yi Hajia, girki dai nake , daga kicin ne na taho da aka ce ana kira, shi yasa ban zo da wuri ba"

Hajia ta kalli Mah tana kama baki ta ce"

😍😍😍😍😍😍😍😍

Azl 60
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Hajia ta kalli Mah tana kama baki ta ce" Lah, ki ga y'ar nan da neman fitina? waye ya aike ki? haba nima fa safiyar shiga kicin din na maki, haba dai, sai kace ba amarya ba, kin ga kina ji?, ki kula kin ji? a zamanku ki kiyaye haki, ki kuma girmama y'ar uwarki, ita abokiyar zama tana da dadi domin a rayuwa idan har ka zauna lafiya da ita zaka fi kowa jin dadin hakan, saboda yau da gobe ta fi karfin wasa, idan kunna jituwa ko abin dadi ya samu ko na wuya sai kun fara kama junna kafin mu ji, bana son jin wata fitinar kin ji ko?"

RAUDA ta gyada kai tana sada kai, ita kuwa Amnah sai kawai ta mike ta fice , dan ba zata iya gannin wannan abin bakin cikin da rainin hankalin ba, ko a me Hajia ta dauketa? lalle Hajia ta gama daukarta a wata shashasha, wato ita za'a nunawa an fi son wancen banzar tsintaciyar magen a kanta ko? ba damuwa su zuba su gani!
Chapter 101 · 0% Book details