Sashe 87
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunsa ya dan kai wajen hancinsa kadan dan maganar da nauyi a yita da iyaye, kawai ya ga ne abokinsa akoy taurin kai shi yasa ya zo din
kai ya sake maidawa ya sada a tausashe ya ce " Tun kafin aurenta da ABDALLAH, MALEEK ke son ta", Ya ajiye maganar a hankali yana dan dago idannuwansa ya sauke dubansa a fuskar Hajia da ta saki baki ta zarro idannuwa ta kuma dago hannu kamar zata tare wani abin, sai ya ga Mah kuwa babu irin matsanancin mamakin nan a fuskarta
"Allah ya kadarto auren na farko ba shine mijin ba, a yanzu da Allah ya yi haka sai nake gannin take takensa, ya ki yarda da abinda nake son nuna masa, ina yi masa gudun yace zai nuna zuciya da girman kai a wajen da bai dace ba, shine nace zan zo na sanar sai a yi abinda ya dace" Ya idasa maganar wannan karron yana dubansu baki daya
"Innalilahi, innalilahi, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, wai YUSUF nawa? RAUDA tawa ta gidan nan? SO? wani irin SO ?, kai, Ni du na rikice, wai tsaya kana nufin YUSUF na nan?" Hajia ke fada da mugun mamaki tana tafa hannayenta da tarin tunanin kai ba wanda take tunanin bane
Murmushi SHAHEED ya iya yi yana sada kansa
Ido ta karra zarowa ta dubi Mah yana fadin" Andiya kin ji wani salamamen tashin hankali? Yanzu yana son nata yana kallo yana ji ya yi shiru har wani ya shigo ya dauka? yau da ace tana cen da yaya zan yi? innalilahi yau ga wani abin mamaki abin rikicewa, to wai dama haka abin nan yake? to ita fa ta sani ne ko bata sani ba? ita din tana son sa ne?, koda yake ai ba zancen tana sonsa, jikana ko y'ar waye idan ta gani ai zata so walahi talahi ma kuwa, kai ai ka gama d'ana Allah ya saka maka da alkhairi aure an yi an gama , ka san ba komai ke wahalar da MALEEK ba sai jinnin nan naku na sarauta, shi ya fi yi masa ila fiye da kowa dan kuwa kana ji kana gani ka yiwa kanka ila dan wani dalili naka ai bai dace ba, kai subahanallah ashe haka ake yi ban sani ba? ikon Allah ikon gaske, ALLAH ya saka maka da alkhairi, wannan zance ai faduwa ya zo daidai da zama tunda har gobe take fita sai ta sake daukan igiyar daraja, dama zuciyata a kulun dokawa take yi saboda abinda na jajibo masa, shikenan yanzun alhamdulilah!"
Duk irin farin cikin da suke yi Mah bata furta ko A ba,domin shi din da kansa Shaheed murmushi yake yi na farin cikin abinda yayi tunani ya tabata, dama ya san in dai Hajia ta ji an gama, duk wani na gidan mai yi mata biyayya ne, sai dai Hajia na kai kawo sai tafa hannaye take tana murna, shi kuwa yana shirin yi masu salama Mah a tausashe ,kanta a kasa ta furta " SHAHEED zauna, inada magana"
Daga shi har Hajia sai da suka kalleta basu shirya ba
Hajia da ta dauko waya ta dawo ta zauna tana dubanta ta ce" Andiya lafiya? yannayin nan naki bana so,me aka yi ne?"
Mah ta sake sada kanta, kafin ta dago tana duban Hajia a tausashe ta ce"Hajia,Ni na jima da tunanin haka, harma na gane eh haka din ne, ama matsalar ita din ai bata son shi Hajia"
Hajia ta tsura mata ido kamar tana son gane mutun ce ko aljan, a hankali ta ce" Ka ji wata bidi'a kuma, shi YUSUF din nawa ne ba'a so?, dama kin san da shi yana son yarinyar nan kika ki sanar min Andiya? me na maki da zafi haka?, kika kyaleni na je nake rarume rarume har na rarumo mai saka farcen matatu na aurawa bawan Allah?, haba kema Andiya to so meyema so din Allah na tuba da ake yiwa Yaren auren so din su je zama ya gagara?, ai sa so junnan nasu idan suka zama miji da mata, kuma Ni na tabata yarinyar nan zata so jikana, tana da wanda ya fi shi ne? meye aibunsa? Gaskiya Andiya ki daina wannan maganar haba , ko wani abin kikeda a rai sai ki bari ki huce a kaina Ni,ama ba a wajen da zan gaza dauka ba gaskiya!"
Kai Shaheed ya sake sadawa yana adu'ar Allah ya sa kar Mah ta kawo wani tsaiko a lamarin nan,sai dai kash tun bai gama adu'ar ba ya ji a tausashe sosai Mah kanta a kasan nan tana fadin" Ba hala bane Hajia, babu wani abin dake zuciyata, gani na yi yarinyar nan yar amana ce, kuma sunnanta bazawara yanzu, hakan na nufin tana da damar zabar mijin da ya yi mata ba a yi mata zabe ba, kuma ni na tabata bata wani sonsa, a yi hakuri kawai ya yi zamansa da matarsa, dukama yaushe ta tare? idan ya so daga baya abinda hali ya bada sai a yi in sha Allah, Ko shi din, ko waninsa "
Hajia ta sake zuba mata ido, sannan ta dago ta dubi Shaheed wanda ya gama ayanawa kansa ta faru ta kare, Hajia kuwa a yau harda mamaki sai da ya kamata na Mah, dan zata iya rantsewa tunda suke bata taɓa ce mata fari, Mah din tace ja ba sai yau
Itama muryarta a tausashe wannan karron ta ce" AMEERAH, kina nufin ba zaki bamu auren y'arki ba dan bata son mu ko me?, kina nufin wani za'a kuma daurawa yarinyar da YUSUF ke so?, Ke fa kika haifi YUSUF , inace ko me yake so, ko a ina abinda yake so din yake ke mai zuwa ki nemo ki bashi ce, sai kawai in ga wannan abin kuma?, mu da aka mana auren hadin mutuwa muka yi? mu mazan basa son namu ma aka basu, muka rayu lafiya bale ita da ake so?"
Mah ta sake yin iya yinta ta budi bakinta wannan karron ta dago tana duban Hajia a tausashe ta ce" Hajia, ke uwata ce, kuma ke kakar RAUDA ce kamar yadda kike ta YUSUF, na san a hada din ba komai bane, sai dai ki min uzuri ki bani dama har su kawo kansu da kansu, idan suka ki za'a kuma daura mata wani shi kuwa ya yi ta rike bakinsa, dan in har yana so din zai magantu ko wani irin jinni ke yawo a jikinsa, dan Allah ki yi hakuri Hajia "
Ta idasa fada tana sada kanta, ta dan yi jim kamar yadda wajen ya yi dif, sannan ta mike jiki duk a sanyaye ta yi gaggawar guduwa dan bata san abinda zai je ya dawo ba kuma, abinda ta sani daya ne, ta shirya ja da kowa a kan maganar nan, babu wanda zai lalata mata amanar da ta dauko dan son zuciya, idan suka duba zuciyarta ta fi su murnar abin nan in dai haka din ne, sai dai ba zata so ta yi shi matsayin hadi ba, ita da kanta zata so ace ta samu SARAKUWAR da hankalinta zai kwonta a kanta, ba zai Amnah ba, Amnar nan tana tafe da kalar rashin da'ar da bata san a inda zata yi waje ta ajiye ba, abu daya tak ta sani ita da ita idan hanya ta hado su su san yadda hanyar ta ishe su, bayan wannan babu wani abu da zata nema na hadi tsakaninta da ita, dan ta kwatanta nuna mata daraja ta nuna bata san haka ba!
Tunda Mah ta mike ta fice a falon wajen ya dauki shiru, shiru mai girman gaske wanda har sai da shaheed ya ji mugun nauyi ya kama shi da tunanin dama Mah din ya samu kafin Hajia ta ji, dan shi bai taba tunanin Mah zata ji abu mai mahinmanci irin wannan amsa irin wannan ta fito daga bakinta ba, bai san dai abinda ya sa Mah din ta fadi haka, kuma shi bashi da shedar eh lalle RAUDA na mugun son YUSUF, abinda ya sani shine amsar da ya gani a wayar YUSUF amsa ce ta idan an damu da kai, sai dai bai sani ba har ina girman damuwar ta kai
Ajiyar zuciya Hajia ta sauke jikinta a mugun mace tana duban Shaheed ta ce" Ka san me yarona? ban san yaya zan yi ba yanzu, dan daga Ni sai Allahna na daukarwa kaina alkawarin daidaita mu'amalata da AMEERAH, inada damar daga hankalin kowa a gobe gobe a daurawa yarinyar cen aure, sai dai wani abu nace min kar na yi haka, ya dace in bata damar ta itama, dan ta nuna tana son a yi adalci kuma ta nuna ba za'a hanna mana yarinyar ba ko?"
Murmushi ya yi yana duban Hajia, dama shi ya san akoy ranar da irin maganar nan zata fito daga bakinta a kan Mah, lokuta da dama idan suka samu matsala ita da YUSUF a kan Mah yakan ce masa ya koyi kawar da kai a cikin lamarinsu, ya ringa tausasa Mah, in sha Allah duk wani abinda ke rikita masu lissafi zai daidaita, Mah zata ji dadi fiye da tunani dan a yi hakuri a bari Allah ya daidaita abinsa ya fi ace za'a yi garaje
A tausashe ya furta" Ki yi hakuri, ki yi addu'a, ki kuma kamanta tayawa, daga wannan idan har wani ya kuma fito mata ba shi ba ki yi hakuri cen dama ba shine mijinta ba!"
Hajia ta hadiye yawun dake wuyanta tana tunanin zata iya kuwa? jiki ba karfi ta yi masa rakiya, sunna tatauna maganar har wajen get na farko sannan ta juyo tana ta sake shawara da komawa kan shawararta ta farko, bata san in har ita zata iya hakuri tana ji tana ganni a yi haka ba, sai dai Shaheed ya fada mata ko me za'a yi ba za'a tsallake hukuncin ubangiji a kan lamarin ba, ya kuma fada mata adu'ar itace ta fi fiye da tada zaune tsayen...., da wannan ta karasa ta shige bayi saboda kiraye kirayen sallar magariba da aka fara.