Sashe 106
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kausashe ya ci gaba da fadin" Inaga dan kin haife shi, yana karkarshin yi maki biyayya ne kika kasa yarda da darajarsa da kuma girman da Allah ya bashi, ina tunanin dan YUSUF bashi da wajen zuwa ya zubar da hawaye sai jikinki ne kike aiki da wannan damar a tunaninki so din ne kina karra daba masa wuka a zuciya, Ke Ameerah da yawa sarakan ne suke badalar kuma da matayen na kirki sun kilace, manyan masu koyar da tarbiyyar ke aikata badalar kuma sun kilace iyalansu, ban san me iyalansu ke aikawa a boyen ba, abinda na sani shine Allah gafurun rahim ne, ban ce d'ana bai yi laifi ba, d'ana ya yi laifi sosai, kuma na fi kyautata zaton dan na taba y'ar wani Allah ya jarabceni da d'ana mafi soyuwa a zuciyata ke wannan halaya marar dadi, yake fitinar kowa a da, kuma Allah ya amshi adu'ata har aka wayi gari YUSUF ya bar aikatawa ke kin san ba dan yana tsoron dan Adam ba ya daina dan na wannan tsarin a duniyarsa, dan yana tsoron Allah ya daina, kuma mun yarda da tubansa domin baya rayuwa dan ace ko a gani, shine zaki duban min yaro ko rikita shi?.......... AMEERAH!"
Bah ya sake fada yana dafe kansa da hannayensa bibiyu
ya sake dubanta idannuwansa sun gama yin ja, ya ce" Inaga Nine baki yafewa ba, da ace kin yafe min da baki min haka ba, Ameerah a me kika dauki sarauta?"
Mah tana kallonsa hankalinta gaba daya a tashe ta ce" Bello, dan Allah ka kwontar da hankalinka mu yi magana, a ganina d'a ai duk na kowa ne, kuma yarinyar nan idan an bata dama an rungumeta ina ga ai aikin lada aka yi ko?"
" Tabas baki san menene sarauta ba, kuma kallon nan da kike yiwa d'anki a bagas ya sa kike tunanin irin kowani mutun ne da yake iya daukan wannan rayuwar!"
Bah ya sake katse Mah, sannan ya juyo ya fuskanceta ya ce" Ki yi hakuri da kiyayar da Hajia da ahalina suka nuna maki koda kuwa mu din nan mune ke dauke da gagarumin tabo na rashin ji a gidanmu, sai dai kuma sarauta gare mu!, ki yi hakuri da kika ga sun kasa yafe maki da wuri yadda ya kamata ba dan kin fi kowa laifi bane ya sa yadda lamarin ya zo mana ne, ki gane Nine na ja maki tsana da na kasa hakura da ke na kasa baki lafiya, na kasa barinki ki yi rayuwarki da wani, tunanin wanina na iya daukan ki bayan ke tawace, rayuwata ce ya sa na kasa baki damar ki rayu cikin farin ciki na saka maki kunci mai tsananin da har kika kasa gane Allah kika yiwa laifi ba uban wani ba da har za'a kasa dubanki a cikin al'umma bayan ke din mai kyakkyawan tuba ce, tunda kika yarda da abinda na saka ki kike kuka har zuwa yau, a haka na jajirce bayan na san in na aureki ba Ni ba sarauta, na yarda na auri abata dan na zabe ki a kan sarauta, kuma na san zaki zabe Ni a kan farin cikinki ......sai dai baki sani ba Ameerah, baki sani ba, an yarda an aura min ke ne dan an san iyayenki, Ameerah walahil azim sarki ya aura min ke ne dan an san tsatson da kika fito, kuma sarki ya fadawa Hajia ta taka a hankali, kar ta yarda ta yi abinda zai bata hutun rayuwa tsakaninsa da ita, ya yarda Kadara ce ta fada tsakanina da ke, domin mahaifinki malamin tarbiyya ne, mahaifiyarki jinnin dan sawani ce, kuma yan anguwa sun sheda tarbiyyar ki!, saboda wannan ne kika samu rayuwar nan da kike gannin ta fi ta kowa muzanta a duniya AMEERAH, me zaki iya cewa da tsatson da AMNAH ta fito da kuma tarbiyarta?!"
ya ajiye maganar dan ya karra sanar mata a shirye yake da ya yi jayayya da ita wannan karron, duka wanda bai taba jin kansu ba zai ji sannan ya dora da fadin" Na ce, me zaki ce a kan tarbiyarta?, me zaki ce a kan mu'amalarta da talakawa?, inace nan na taya ki kashe maganar korar macen da ta yi mata salama dan tana waya a aiki a masarautar nan da ta yi, kuma a dan zaman da aka yi da Ni na abinda ya shafeta kafadata da tawa ke jere a saman kujera a lokacin da ke duwawunki ke kasa dukda kina da ciwon kafa saboda taki SARAKUWAR a saman kujerar!, kin ce an zo da dan daudu da magungunnan da d'an daudun ya kwashe wanda ke tabatar maki koda bata san waye ubanta ba ta san asiri ke tafe da mahaifin da take yiwa kallon uba a gareta hakan har yana birgeta dan kuwa gashi an kawo mata har gida ta kai katon dakinta na sunna , kuma mahaifiyarta ta kwana a nan din, Ameerah so kike yi sai an wayi gari YUSUF ya kore mu daga fada bisa umarnin matarsa zaki yanke jiki ki fadin min ko me?, ko so kike ki ce min ko a tarihi baki san cewa SARKI baya auren muguwar mata a sanin kansa, sai dai idan daga baya zata aikata masa da muguntar a cikin gidansa, rayuwa ta yau da gobe ta sa ta zama muguwar?..........., shine dan kin dauki SARKIN GARINKI abinda kike iya juyawa yadda kike so, da tunaninki zaki yi masa umarnin zama da macen da aka tabatar masa ga abokin shashancinta? kin san girman abin nan kuwa? ace namiji ya ga mutumen da matarsa ke shashanci da shi koda matar kiyayarsa ce kuma ace ya yi rayuwar aure, rayuwar da ba sirri tsakanin mata da miji ? haba Ameerah......." Bah ya karashe wannan karron muryarsa a tausashe, yana dubanta ya ce" Ina laifin ki ce a yiwa yarinyar nan sassauci, a yi lamarinta a siri sannan a dauki nauyin ta, a kilacewa a bata tarbiyya kuma a kaita dakin aure nesa da kasa a bata damar gina rayuwa in har ba hannunta a cikin dinke laya a bakin gawa? ama sai ki ce a rayu da ita a haka bayan ana magana ne ta uwar al'umma ba uwar jikokinki kadai ba, ana magana ne ta gimbiya ba wai matar YUSUF kadai ba, muna magana ne ta gidan tarbiyya ba y'ar aminin uba ba?"
Ya karashe kirjinsa na daukan zafi yana rintse idannuwansa hadi da rike hannunta da karfin da ya sa itama dantse lebenta
A kausashe ya ce" Ba zan iya ba, ba zan iya raka ki a wannan tafiyar ba, idan kuma kika ja zan ja, dan ba zai ce min komai na kai kararki a kan wannan maganar ba, AMEERAH a kan maganar nan zan ja da duk wanda yace zai ja da Ni, kuma ki yi hakuri tunda kika sanar min dole a gaggauta neman iyayen marigariyiyar nan idan sunna raye a sanar masu tashin hankalin nan, hukuma dole zata shiga sannan dole Sarkin garina zai shiga, za'a je a tono kabarin koda an dora wani a kansa, za'a ciro layar nan cikin lokacin mafi sauki, domin ba zan yarda ba dukkan wani abin da ya dace sai an yi ANDIYA sannan a yiwa Amnah adalci, laifukan da kike tunanin nan mun tuba zamu ci gaba da neman tuba a wajen wanda muka yiwa su, kuma zamu jajirce da aikata wasu aiyukan ladan ama ba dai wannan da kike so ba!"
Daga haka Bay ya saki hananyen Mah ya mike ya fice zuciyarsa na karra tukuki......, walahi ransa bai taba ɓaci da Ameerah ba irin na yau, kuma walahi sai ya yi mata matsanancin fushin da zai bata mamaki, sannan a dole zai dau mataki a kanta koda abin nan ya taba kwakwaluwarta zai fara nema mata magani, dan kuwa irin yadda ta daukaka lamarin rayuwarsu da zafi ya wuce misali!
A lokacin da Bah ke cikin rikicin nan da Mah, YUSUF kuwa ya jima da karasawa falon gidansa baba ya ja ya tsaya ya kalli gabas, ya kalli arewa ya kalli kudu ya kalli yamma, gannin ya rasa alkiblar da ta fi masa sanyi sai kawai ya nufi dakinsa kansa na karra sarawa da matsanancin karfi ya dauro alwallah ya je saman salaya ya zauna hannunsa rike da carbi yana ja yana sauraron masalaci, domin yana ji yana ganni fita masallacin ya gagareshi saboda matsananciyar juwa da ciwon kai , gashi ko kari bai yi ba, sai abin ya yi yawa ya sa ya kasa zuwa masallacin sai a nan dakinsa ya ringa bin salolin nan har ya samu ta isha'i sannan ya lumshe idannuwansa daga kwoncen da yake yana jin wayoyinsa agaji suke nema, ama ya kasa tarda su , daga baya ma sai kukansu ya fara damunsa ya rasa yaya zai yi sai ya rintse ido kawai yana kama sunnan Allah a zuciyarsa
*RAUDA* ta jima rike da wayarta a kunnenta da kuma plate din shayinsa a gefe, tana jin Muryar Mah dake cen kasa, wace ita take cikin wani halin tsaka mai wuya na tunani ta rasa yaya zata yi da tunani kuma rashin gannin ya dawo ya shiga damunta karshe dole ta dauki waya ta neme shi da kanta, ama ba'a dagawa, hakan ya daga mata hankali, ta sani duk rintsi in dai wayarsa na hannunsa yana daga kiranta, shi yasa ta yi kiran RAUDA tace ta je ta gano mata, shine ta dauki lipton dinsa gannin yana inda ta ajiye bai dauka ba, haka abincin rana da na daren sunna yada suke sai ta nufi dakin nasa da lipton din, ama kuma ta kasa shiga dan tsoron abinda zata tarar, ta yiwu ma tare yake da Matarsa
A hankali Mah ta ce" baby, baya nan yayan baku ko?"
Da sauri ta rintse ido ta kama ta bude ta shiga, sai kuma ta shiga kallon dakunnan da tunanin to ina zata duba? duba da daki biyu ne, a hankali kuwa sai ta ce" A'a Mah ban karasa ba, na bude nan din kuma kin ga ashe dakunnan biyu ne ina ne nasan?"