← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 117

Sashe 30

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia ta lumshe idannuwanta tana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da karfi, a sanyaye ta ce" MALIK!, kana nufin Ni na isa na nada ko na sauke?, kana nufin kace a cikin wannan tsarin ka ga maganar mutun a ciki? YUSUF a jiya ko Ni ban san zan rasa d'ana ba, bale har wani d'an nawa ya fadi rashin lafiya, kana tunanin inada ta cewa a wannan tsarin? YUSUF na sha fada maka, ka sanyayawa zuciyarka ka kuma dawo da hankalinka dan babu tamtama abinda ke yawo a jikinka tabbatacce dai dai idan lokaci ya rigayi fata......"

"Dan Allah ki daina min magana kamar Ni kadai na yi saura a cikin jikokin ki, kin san ko ina yaro abinda na fi gujewa kennan, ko aure ban yi ba , ban san darajar abin ba, girma ne da ya fi karfin mutun irina, Ni dan kasuwa ne, Ni mai tafiye tafiye ne, rayuwata ba irin ta sarauta bace!" Ya fada wannan karon a kasashen da ya saka Nana dubansa ta dan matso ta tausasa muryarta tana dubansa da kyau ta ce" Haka nake ta kokarin kwatantawa Hajia, ama har ta mareni, na fada mata ga RISLAN nan, ama ta kasa yarda, ko kasar nan ba zasu yarda da sarautarka ba, tunda baka boye waye kai, ka fita ka ji yanzu haka cikin rigimar da ake a kan maganar nan, Hajia, Hajia...."

Ta fada tana duban Hajia ta sake fadin" Hajia kina da damar fada koda a kwonce kike a aikata maki, dan kin isa, ki bashi abinda yake so ki dora wanda ya cencenta "

"Tabas a kan maganar nan, kowa zai gane Wacece Ni, na rantse maku a kan wannan sai dai raina ya fita daga gangar jikina, ku rubuta ku ajiye a yau idan girma bai kamaka ba, mahaifinka ya mike ya fansheka, kai har kana da bakin ce min ya hau sarauta? Mahaifinka ne zaka bari ya hau sarautar? Ciwonsa ba na sarauta bane, domin abu kankani na saka shi fita a hayacinsa!, idan ya hau na dan lokaci ne, kuma babu wanda ya isa ya saka Ni ce za tsarin tarihin kasata, Nana ki fita a gaban idannuwana, MALIK ka je kaima ka je kawai!" Hajia ta fada muryarta na cinkushewa kuka na neman barkewa daga bakinta hankalinta gaba daya a tashe

Rai bace YUSUF ya cika hannunta ya mike har wayarsa kirar iphone ta fadi kasa ta yi ratsa ratsa ƙafarsa ya dora Mata sakamakon yada jikinsa ke wani irin abu na bacin rai, sannan ya juya har zai fito ya juyo yana kallon Nana wace ta mike din itama rai bace ya ce"

Azal17

Rai bace ya ce" Ki yi gangami, ki tara majalisar dokokin kasar nan, idan mun dawo daga rakiyar Aba a yi zabe, shin zasu yarda su dora mashayi, mazinaci, kuma wanda bashi da aure saman kujerar mulkin garin nan? Ko zasu zabi naggartace malami, mai mata da ya'ya?, kar ki yarda damar nan ta kubuce maki, domin idan kika yarda suka nada min sarautar nan sai na adabi rayuwarki a kan addabar tawa rayuwar da kika yi Nana!"

Yana gama fada ya yi waje ya koma bangaren mahaifinsa ya shige wanka yana ta ambaton sunnayen Allah, fiye da yadda ya saba ambata a da, dan tunda yake bai taba doguwar addu'a irin ta yau ba, burinsa yana fitowa ya ga mahaifinsa ya farka, burinsa yana fitowa ya ga komai ya zama tamkar mummunan mafarki a wajensa, dan ba zai taba iya misalta wannan mummunan labarin mai dauke da *AZAL* tiryan a kansa ba, ina shi ina sarauta? Ina shi ina sarauta jama'a?

Yana fitowa daga wankan ya saka tufafi a cikin tufafin mahaifinsa, yadi ne ya dauko marar nauyi ya suturta jikinsa, kuma yadin ya dauki jikinsa sosai , rigar cema ta so yi masa kadan wajen kirji da danatsunnan hannayen, sai dai kasancewar ya san a yanzu babu wanda zai yarda ya fita a dole ya saka , a ransa yana adu'ar a gama dukkan abinda za'a yi ya je ya kai mahaifiyarsa asibiti sannan ya wankawa wannan marar kunyar marin da zai saka ta san waye shi da har zata ja masa kashedi a kan Mahaifiyarsa dan raini.....wato abubuwa sun masa yawa ne ta yadda ya kasa tantance me zai yiwa fushi, sai yake kame kame a cikin zuciyarsa kala kala

Yana fitowa ya sake dukawa daf da gadon mahaifinsa ya rike hannayensa, a hankali ya dora gefen fuskarsa a tafin hannunsa na dama, yana so ya yi magana ama abin ya ci karfinsa zuciyarsa ta gaza bashi damar amayar da abinda ke ransa, sai kawai ya mike ya daidaita kwonciyar mahaifin nasa ga nufi waje yana ji zuciyarsa na sake tsintsinkewa ya nufi ayarin taron mutanen dake zaune a manya manyan shinfidu na alfarma kowa ka gani yana addu'a ne, ana zaune ga dukkan alamu shi din kawai ake jira domin a lokacin da ya karaso tun kafin ya je wajen da zai zauna manya manyan malaman garin da limamai suka mike sai sarakunan, hakan ya sa gaba daya jama'ar gari suka mike ya zamto kusan hankalin kowa a kansa da tarin idannuwa

Dakatawa ya yi yana bin mutane da kallo, sai kuma ya sada kansa yana jin bayanin limamin baban masallacin masarautar da kuma masallacin idi

Ajiyar zuciya ya sauke ya gyada kai ya kai dubansa wajen RISLAN da ido ya masa alamun ya karaso mana, hakan ya sa RISLAN karasowa daf da shi suka fara yin gaba dan zuwa dakin da aka killace gawar aka gama kimtsata

Su ne suka fara dauka daga gaba, sai mutane hudu wasu daga tsakiya biyu daga karshe aka fitar da ita aka ajiye aka salaceta sannan aka nufi makabarta aka binne aka juyo

Tunda aka wakilce shi wanda ya fara shiga kabarin mamacin yake jin tamkar hawan jinni na daf da buge shi, dan ya san me hakan yake nufi, ama kuma tarin abinda ke kai kawo a zuciyarsa a yau din ya fi komai karfi, dan duk yadda ya so hanna hawayensa zuba sai da ya zubar a lokacin da ya ga yau an turbune baba baba a karkashin kasa shikenan an kare, duk sarautar shi, duk arzikinsa, komai da komai ya tsaya a nan an kare, shikenan a yanzu mamacin sai shi sai halinsa, ko me ya aikata a duniya daga yanzu zai fara girba, ba zancen sai kiyama ya tsaya shi tasa kiyamar ta tsaya kennan, hakan ya sake rikita tunaninsa bale da ya rintse ido ya hango shi din waye sai ya ji inama zai ga mamansa a yanzu? Babu abinda zai hanna shi dukawa ya fashe mata da kuka da fadin yaya zai yi da ransa?

Tamkar a mafarki suka karasa fada, kamar a mafarki yake kallon yadda aka je dakin mahaifinsa da manyan sarakuna da likitan mahaifinsa wanda ya gabatar da jiga jigan dalilan da mahaifinsa ba zai iya rike sarauta ba, wace manyan garin da sarakuna makotan garin suka yi amana da bayanin likitan da kuma abinda idannuwansu suka gane masu mahaifinsa a kwonce tamkar ba rai yana amsar ƙarin ruwa kan wani, a irin lokacin ne suka tisa keyarsa, jiri na dibansa, ya saka hannunsa da sauri ya kama kofar baban falon mahaifinsa idannuwansa a kan matan mahaifinsa su dinma a tsaitsaye suke labarin zukatansu a bayane a saman fuskar su, tashin hankalinsu da damuwarsu ya kasa boyuwa a saman fuskokinsu sunna yiwa abin kallon wani iri, sai dai basu fida rai ba, dan tunda aka sanar cewa kafin a tabatar da ko waye sarki sai an yi zaman da akan yi idan abin ya zo da rikici, sun tabata da wahala a dora YUSUF sarki a yau

Cikin kamilaliyar murya bayan an yiwa dogarai dake rakadi alamun su fice sarki SHAHEED Dan Abubakar ya karaso daf da YUSUF dake tsaye ya saka kwayar idannuwansa mai dauke da abin kwali cikin nasa, dukda rawanin dake jikinsa da kuma shiga irin ta sarakai bai hanna shi sassauta rawaninsa , dudka tsaurinsa da rikon da yake yiwa rawani matsayin abin da ya fi komai kusanci da shi a suturar jiki sai da ya sassauta rufewar fuskarsa har fuskar ta bayyana a idannuwan YUSUF, fuskar da dama ba bakuwar Yusuf bace domin kyar ta san kyar ne, sukan hadu a filin basket ball a matsayin freind su buga kwalo , shi SHAHEED fuska a bayane ama babu wanda ya san waye shi sai biyu ko ukun mutanen wajen, shi kuwa YUSUF a matsayinsa da tasa darajar wace take hanna shi walawa dan ya tsani ya fita a ringa sada masan nan baya so

A tausashensa da yannayin isar sa ya ce" Faduwa zaka yi ne MALIK?"

YUSUF ya zuba masa ido, yana ji tamkar ya budi baki a gaban kowa yace SHAHEED bana son rainin hankali, ko ya rike shi yace ka rufa min asiri ka gudu da Ni? Ama ba dama dan kowa idannuwansa a kansa ne ciki harda Sarkin agadaz wanda ya yiwa likitan abu alamun kar ya fita dan a yau ko a sume ne sai sun tabbatar da wanda ya cencenci mulkin talakawa a kujerar da ta dace da shi, zasu ga su da wadinncen masu akidar waye asalin mai akida , sarki ko masu rike da mulki!

A hankali ya kai tatausan hannunsa wajen goshinsa dake yamutsa masa ya dan murza, hakan ya sa likitan matsowa da girmamawa ya ce" Ko zaka zauna na auna jikinka sir?"

Sosai ya so yin rigiza ya zube a wajen nan, koda zai dada keyarsa da kasa ne dan ya zamo ya samu summa mai kyau wace zata dan ja shi har a nada sarki RISLAN, sai kunnayensa suka jiyo masa magana ta aboki kuma tsara a wajen mahaifinsa wato Sarkin agadaz a tausashe ya ce" Ba maganar zama, in sha Allah koda a summe ne sai mun tabatar da shi a dakin taron cen, daga nan kuma sai mu tsaya da jajircewa da addu'a har Allah ya tabatar da shi a kan kujerar da take tasa, in yaso sai mu farfaɗo shi ya amshi abinda yake nasa dan aiki ne baba Malik"
Chapter 30 · 0% Book details