Sashe 65
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kiraye kirayen sallar magariba ya saka Bah mikewa ya mata alamun zai je sallah ya dawo
tare suka fita da RISLAN suka nufi masalaci bayan sun yi alwallah
sun gabatar da sallar sunna hanyar dawowa bangaren na Nana Bah na gwada kiran layin matansa gaba dayansu yana ji a ransa kamar ransa na daf da bacewa sakamakon rashin ganninsu bayan da aka sanar babu wace bata ji ba, ama shiru basu zo ba RISLAN ya dukar da kansa zuciyarsa na sake neman tarwatsewa saboda irin yadda suka zamo tamkar mujiya a cikin familly din saboda halayar mahaifiyarsu, babu mai yi da su, babu mai daraja su, domin a lokacin da ta yi abin nan yadda kuka san yaɗuwar mutuwa aka abin ya yadu, kafin kace kwabo kowa ya ji kuma kowa ya sani nan da nan aka shiga tofin Allah tsine domin wannan abu da ta yi Babu abinda ya kai shi abin kunya da muzantawa, karrara ta fito ta nuna son kai a kan abinda bata da tabas, koda tana da tabas a kan ɗan dan uwanta uwa daya uba daya? hakan ya sa a yanzu dai mahaifiyarsu bata da wani abokin hulda a cikin garin nan sai masu hali irinta, ita da kanta du a takure take ga matsaloli na yau da gobe, domin ba matsalar son a dora su a mulki kadai ke yayube da rayuwarta ba, ga ta yaya ga ta wajen aiki.
Bah na gama kiran daya bayan daya ransa bace yana fadin me kennan?, me yasa bai gansu ba, yana huci ya kalli RISLAN ya ce" Wai me yake damun yarinyar nan har ya kaita da shan guba? me yake damunta a rayuwa ita kuma da har ya fi karfinmu muna zaune a cikin gidan nan?"
kai RISLAN ya sake sadawa yana fitar da hucin numfashi mai amon "HUMMMM." Ama ya kasa fadin komai
Bah ya sake dubansa a lokacin da suka shiga dan get din bangarensu yana hangen daidaikun kuyangin da ya tabata na Hajia baba ne ya ce" Tana da wata matsala ne da ban sani ba?"
RISLAN ya rasa yaya zai yi, domin irin yadda Bah ya tsaya yana nufin sai ya ji abinda yake damunta kennan?
kai ya sake sadawa a nutse ya furta" Bah, shirme ne kawai ta sakawa ranta da abinda bata isa ta bawa kanta ba, da ace ta bi maganar da na fada mata ta fawalawa Allah na tabata da ta ji sauƙin abin cikin ruwan sanyi, domin tabas da Allah ya bata mafita nagartaciya, idan har abinda take yiwa din dama nata ne sai ta ga ba tare da ta daga hankalin kowa ko zubar da wata kima Tata ba Allah ya kawo hanyar da shi kadai ya isa ya kawo ta samu biyan bukata,ama sai ta ki, a kulun da irin abinda zata fito da shi, a kulun da irin fitinar da zata bilo mana da ita, shine na dawo da ita nan tunda maman rashida na nan koda yaushe tana hankalce da ita, shine yau ta yi anfani da damar nan da ta ga ta fita anguwa gidansu ta sha abinda zata bar duniyar gaba daya, ko me take tunani, ko ina karatunta? ko bata san du wanda ya kashe kansa ɗan wuta yake ba? Ni dai abin ya matukar gigita min tunani"
"To ai baka sanar da ji damuwar da take sakata hakan ba, sai zagayeni kake yi da nuna min kun ishi kanku kai da mahaifiyarka ko? ba damuwa bari ita aishar ta sanar min!" ya fada ya juya ya nufi ciki dan sarai ya gane akoy abinda RISLAN ke zagayewa, sai dai ya makaro haihuwarsa ya yi ba shi ya haife shi ba bale ya zagaye shi a magana ya yi shiru ya masa biyayya!"
Bah na shigowa ya tarda Hajia zaune saman kujera, Nana na zaune saman cafet hannayenta duka biyu a saman kanta tana kuka kasa kasa Hajiar kuwa na magana mai kama da fada
har ga Allah bata san cewar Bah ne ya shigo ba, da ta yi shiru kamar yadda YUSUF ya nuna baya so mahaifinsa ya san abinda y'ar uwarsa ta aikata dan ya kula yanzu Bah yannayin ciwon zuciyarsa na so ya zama abu kankanima na tada shi, dan kuwa da ta ita ne da tuni ta sanar masa walahi, Bama kamar in ta ga Nana na fira da Bah normal sai abin ya ringa bata mamaki da tsoro, ta rasa a wani bigiri zata ajiye wannan halaya ta Nana, sosai take tsoron irin halin Nana, har ga Allah ko ita mahaifiyarta ta tabata idan abin son rai ne ya tasowa Nana tsaf zata zabi kanta ta barta, shi yasa itama ta yi watsi da ita take rayuwarta dan bata son mutun mai irin halin nan
Hajia ta ci gaba da fadanta tana fadin" Yanzu wa gari ya waya?, kin ga tun qq duniya kema Allah ya baki mai irin halinki sak, kuma ya saka maki kaunarta a ranki, sai ki ji abinda nake ji, Nana sai ki ji abinda nake ji a raina nima, kina dai ji kina gani , baki isa ki tsawatar mata ta daina abinda kika san ba zai taba yiwuwa ba, kina kallo ba zaki iya hanna y'arki son makiyinki ba"
Nana ta dago da sauri tana kallon Hajia, murya a rikice ta ce" Makiyina kuma Hajia?"
Hajia ta zabga mata harara ta ce" Makiyinki mana, azaluma! makiyinki mana, yaron da tunda ya fara wasu yan rashin ji kika sako shi a gaba, a hankali kika saka mahaifinsa ke jin haushinsa, kika saka yayanku ke jin haushinsa, sannu a hankali Allah ke nuna maku shi yake da damar yi ko hannawa ama kuka kasa ganewa, ki zage shi ya ciyar da ke, kina ji kina gani da aikin naki da gadon baki yake ciyar da ke da mijinki, duk bai ishe ki ishara ba kike ci gaba da zagi nai, a gabansa a gaban iyayensa bakya jin kunya ko tsoron zuciya, kina tafka rashin mutuncinki yadda kika so, Nana kika janyo min comitin kare hakkin dan Adam Ni? dan kawai ance ba za'a dora danki sarauta ba saboda Yusuf na raye? kika zo kika kwashi kayan kunyarki duk irin yadda kika mike gaban duban al'uma kika zage shi kika ce mashayi ne, mazinaci ne ba zai yi sarauta ba aka bashi sarautar, kika ci gaba da rayuwa karkashin sa dan rashin kunya ance ku kauro kika kauro , kika ci gaba da rayuwa karkashin sa, to ta yaya Allah ba zai kama ki ba?, Allah ya bata lafiya kawai idan da rabon ta tashi ama Ni dai ba zan taba tarban YUSUF da maganar ya auri Dayana ba, sai dai ta mutu in mutuwa zata yi!"
idannuwansa ya saka cikin na Nana wace ta dube shi a yannayin tsorace, hakan ya sa Hajia juyawa itama da sauri dan har ga Allah ba zata so ya jin ba dan itama jimawar nan da ya yi cikin rashin lafiya Allah kadai ya san Irin halin da zuciyarta ke ciki, komai sai ya so cakule mata, domin sai ta zama ita kadai ke kai kawo a kan lamarin rigimamenta, danma yana jin maganar mahaifiyarsa ai da sai ta yi kuka da idannuwanta na rikicewar tunani, sai Allah ya taimaketa yana jin maganar mahaifiyarsa, ita kuwa mahaifiyar tasa tana yi mata biyayya tamkar y'ar da ta haifa da cikinta, dan ita da kanta tana jinjina kawar da kai da biyayar AMEERAH, tana kuma godewa a ranta, bata taɓa nunawa bane.
"Bello, kun dawo?" Hajia ta fada tana kokarin mikewa dan har yanzu bata kaza kazar da kaffafuwanta , kai tama hakura da samun kuzari irin na da ta saka a ranta ta yiwu tsufa ya sa kuzarin tafiyarsa , danma tsufa ne na mai jin dadi, dan tuni daidaikun wa'inda suke raye da suke shekaru kusan daya suka yi yarinta tare tsufan ya gama kai su kassss , dan harda wanda abin shirficewa ta same shi, ama ita da sauki sosai
Karasowa Bah ya yi a hankali ya kamata ya mayar da ita saman kujerar ya zaunar da ita sosai sannan ya zauna shima daf da Hajia sannan ya sake kallon Nana yana jin irin yadda zuciyarsa ke babalewa
a hankali ya furta" Haka kika yi wasa da zumuncin Allah? ashe dama irin yadda kike aibata shi dan naki ya samu shiga ne? ama Ni ai ban taba bambanta yayanmu ba, na dauki wa'inda kika haifa tamkar Ni na haifa, ashe Nine ban iya son d'a ba ko ban san zafin haihuwa ba? shine kika so ki sa na tsine masa, Ni nawa ya bi duniya ko? ashe kema kina son taki duk irin abinda yake yi? kina mancewa da irin yadda Allah ke nuna mana YUSUF mai daraja ne?, kar ki manta lokacin da kika kaini wajen wani mutun wai mai bada magani yaro ya bar rashin ji, mutumen yace ki fita yana son magana da Ni, kin san me yace? cewa ya yi daga Ni har ke sai mun ji kunya idan bamu daidaita mu'amalarmu da wanda Allah ne ke tsaye a kansa ba mutun ba, yace mu kiyaye domin shine zai ciyar da mu a gidan duniya?, duka Wadinnan abubuwan da kike ganni basu isheki ishara ba ko?, Nana kin ji kunya, kuma kin ci amanar zumunci, ama Ni a wajen Allah nake nema, kuma ko yanzu zan yi domin Allah ne, Hajia dan Allah idan har ba damuwa ki bani dama na kwatanta sanar masa ya aureta, idan har ya yarda shikenan sai a hada da ita a Daura masa biyu, na san zai yarda ne bi izinillah , ai hannunka baya taɓa rubewa ka cire ka yar, Allah shi kyauta"