← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 117

Sashe 21

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A irin wannan lokacin Rauda na cikin yannayi biyu ne, na tashin hankalin yannayin uncle dinta, da kuma wani iri gannin itace aka titsiye kan wa ya bata kudi , kuma daga ina take

Mama kuwa ƙarara tashin hankalin gannin yannayin uncle ya nemi damunta har ta kasa hakuri ta tare shi da fadin" to wai me kake nufi Umur? Yaya zaka wani tisata kana son sai ta fada maka inda ta samo kuɗi?, in dai zata samo din ai da kyau zata kama min wahala da ku a gidan nan tunda kai ai hoto ne , kwarar shinkafa baka kawo mana bale cefane, ga wuta ga ruwa ga haya, ga diyar yaya ta yau da gobe, kuma kudin nan sisi ba zan baka ba dan bashi nake binta, ina dalili mutun sai kace wani na Allah , ko mema ya hannaka zuwa ka sha abinda ka saba gashi kana neman fito min da sababin sirfa? Kai walahi in dai hakane ka fi kyau a maye, gaskiya kar ka wani tambayeta inda ta samu kudi , ai tafiya ta yi kyau gobema a maimaita"

Jikinsa sanyi ya karra yi ya sada kansa cike da kunnar zuciya
Rauda dake hawaye ta budi baki a sanyaye ta ce" Baba, walahi babu abinda na yi, kudin nan da ka gani turo min su aka yi daga......."

"Rauda ki je ki huta, zan neme ki" ya fada a harhade yana dafe kansa dake sara masa
Sosai ta ji hankalinta ya karra tashi, da kyar ta iya barin wajen ta shige dakinta ta rakube tana barkewa da kukan da take ta danewa, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, lalle ta bata ran marikinta mai kaunar ta da son gannin ta zama abin kirki a rayuwa, ya Allah da ta san fitar nan bata da wani alkhairi da bata yita ba, yanzu yaya zata dubi tsabar idannuwansa ta fada masa da Yaren bahaushe kudin da aka sako a asusunta akace ta saka kati kawai? Ta ina zata fara fahimtar da shi abinda yake tsoron nan ita RAUDA ta fi shi tsoronsa da adu'ar Allah ya sa baya cikin mummunar kadarar dake iya samunta, ita dai ta san bata kiyaye wasu abubuwan ba, ama kuma ta san har zuwa yanzu mutuncinta na tare da ita
, kunci ne ya sarketa sosai, kunnayenta na jiyo mata Muryar uncle dinta da Mama sunna abu mai kama da kokowa, domin tana jin lokacin da ya rantse cewar sai ta fitar da kudin nan ya kaidawa mai su , ita kuma tace bai isa ba ai hakinta ne, tana bin Raudar kudi ne,
Wannan ya karra hasala shi suka kama kokowar karfi da karfi har ya dambarata da kas ya shige dakin nata ya ringa zubar da kayan dakin yana neman kudin da kyar ya gansu karkashin katifarta dake saman gadon karfe mai runfa ya fito da su ya sameta sai ihu take wai ya ƙaryata kuma yau sai ya dauko masa motar yan sanda wai ya satar mata kudi, ga yarta zaune tana kallonsu tana tabe baki, dan ita ko a kwalar rigarta haka ya zo ya sake ficewa a gidan ya nufi inda zai ga liman domin abin nan na Mama ya masa yawa, inama ace yana da halin yin wani auren? Da ya salami matar nan ya kawo wata ko Allah zai sa ya samu mai daɗin halin da zata taya shi rike marainiyar ALLAH, a yanzu haka yana daga mata kafa ne saboda abubuwa da dama, wajen aikin nasa an kore shi dan da ya je dazu aka nuna masa dama an bashi dama ta karshe ne, dan a kulun idan aka yi albashi sai ya kusan kwana goma ba'a saka shi a ido ba, ana daga masa kafa ne saboda abokin ogan dake rokar masa alfarmar nan, zuwa yanzu kam ya gama cinye duk wata alfarmarsa ba zai ci gaba da masu aiki ba, idan har ya saketa bai riga ya riki abinda zai ringa biyan hayar da suke ciki da abincinsu ba wani halin ne zai sake saka su bayan wanda suke ciki,
Si abu na biyu ba zai yiwu ba zamansa a yanzu daga shi sai Rauda da Abdul Hakim
Eh lalle uncle dinta ne shi, ama rayuwa abin gudu ce, bale shi da ya ringa jin wa'azin da malan ke yi akan mashayi sai ya gama tsorata da rayuwar kanta, ga wani irin mugun bukatar ya sha dake damunsa, ji yake yi idan bai sha ba har kamar yana iya rasa numfashinsa, dan ko a jiya da ya rasa Rauda sai damuwar ta so fin karfin tunaninsa har ya fara tunanin inda zai samu abin korawar da kyar ya danni kansa ya hakura

A cikin gidan kuwa Mama tamkar zarariya da kyar ya iya kama abu ta mike tana ihun a taimaketa kudinta kar ya je ya sha giya da su dukansu, fadi take yi Umar tsaya na yaga maka na shiga uku ina ya nufa? Sai dai ba shi ba alamarsa, hakan ya hadasa mata muguwar juwa da ciwon kai, a dole ya yi wani irin kwonci tsakar falon a kasa tana kukan babu mai hannata rufe Umar a garin nan in har ya taba mata kudi, babu mai hannata mayar da rayuwar Rauda ta tantiriyar ƙaruwar da ko namiji mai bin mata sai ya ji tsoron ta, dan walahi sai ta maida ita tamkar karya in dai ya yaba mata kudinta!

A dole Rauda ta sake kama kanta a wurin ranar kaf, sallah kadai ke fitar da ita ta zagaya ta yi alwallah ta labe a dakinta, domin ko abinci gagarar shiga bakinta ya yi

________________________________
Cikin nutsuwa ya silala motar dake dauke da mahaifiyarsa da mahaifinsa yana jin takaicin isa irin ta Hajia, yanzu ace mahaifiyar ta yi jinya ta gama ba zata barta ta huta ba, a'a dan mulki irin na Hajia shine ta bada umarnin anna ta zo ta ga yaya jikin nata ta wartsake ne ko ciwon dama ba wani bane ta wani ja mata d'a ya yi watsi da matansa ya je yake jinyar saura, mace kulun ba lafiya sai tsomarewa take yi uwa akuyar maya

Wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa saboda gaba daya yannayin gidan nan komai ya tsufa ya lalace harda wajen parking space, ama dan bakin hali irin na Hajia da A'isha kiri kiri sun nuna gida babu abinda ya yi, shi kam yana da niya daya a kan gidan nan shine duk ranar da ya tashi ya samu isashen lokaci gidan nan sai ya saka an rushe shi sannan a tayar da gini na yayi na mamaki, ginni na sarauta ba wannan ginnin da du waje ya hade ba!

"Ku shiga wajen Hajiar , ina zuwa" mahaifinsa ya fada da dan sauri ya fice a motar ya nufi bangaren matansa biyu da yayansa na wajen su

Da sauri YUSUF ya kalleta ya sake bin hanyar da Mahaifinsa ya bi yana mamakin to ba yace masu na zai shiga ba su shiga su fito su maidata su je inda zasu je da shi su dawo? Ikon Allah, a dole ya fito ya budewa mahaifiyarsa ya bata hannu ta kama ta fito suka jera tana tafe a hankali cikin nutsuwa shi kuwa yana duban hanyarta kamar wani wanda ke janye da makauniya har suka zo kofar shiga ya duba ya dauki takalmanta da ta cire ya saka daga ciki inda ake ajiyewa idan an zo suka shige cikin da salama a bayane a bakin Mama, shi kuwa ya yi ciki ciki, duda ya ga yau zaman Hajiar ce kawai sai masu tayata zama, ba A'isha da ƴaƴanta da wasu cikin jikokin Hajiar na bangaren sarki da Mahaifinsa

Ba laifi Hajiar ta amsa ba yabo na fallasa, ko dan ta ga YUSUF a wajen ne ko ta fara yin sanyi ne? Ita dai gatanan ama tunda ta amsa lafiya wa tambayar da Maman Yusuf ta mata cewar yaya jikinta suka ja baki suka yi shiru, Hajia na kallon YUSUF dake zaune a kasa kafar mahaifiyarsa saman cinyarsa yana amsa waya yana zuba turanci yana dan mamatsa kaffafuwan nata a hankali a hankali

Kai Hajia ta dauke a zuciyarta yana ayana' yaya kike so mu shirya da ke, bayan kiri kiri kin shiga tsakanina jikana? Me na maki da zafi da kika zabi rabani da abinda na fi so a cikin zuciyata fiye da kowa? Ba zan daina gannin bakinki ba tunda bakya sona da alkhairi bakya son farin cikina'

A birkice ya shigar masu baban falon gidan, wanda yake kyautata zaton a irin lokacin yana iya samun su biyun a falon koda babu yanyansu tare da su

Ai kam ya same sun, su dukansu kowace na abinda ta fi kwarewa a rayuwa

Bai tsaya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwansu ba ya fuskance su yana fadin" Haka kuka zabawa kanku rayuwa ko? Ba zaku yiwa kanku wa'azi ba? Tun da jan sawayenku har shekaru sun ja kunna fama da abinda bashi da wani alkhairi a tare da ku ? Me zai rage ku ko ya cira a jikinku idan kun je kuma kun umarci yayanku su je su mata sannu? Babu wace zata ce min bata ji ba ko bata sani ba, ko dan yaronta dake dawainiya da ku ai kwa mutunta ta, shin me ya rage mana a zamanmu da ya wuce mu gyara makwoncinmu? Ace kunna nan idan ta kwonta sai dai Ni zan yi jinyarta? Kun san dai ba bari zan yi a turo mai jinyarta daga gidansu ba bayan nima inada ahali, shin me yasa ba zaku yiwa kanku fada bane a zamantakewar mu ku yiwa kanku adalci?" A tausashe ya ajiye maganarsa yana duban su ya dora da fadin" Walahi bakwa min adalci, bakwa min karra, kuma hakan ya bata min sosai"

Daga wannan ya fice a falon ya yi tafiyarsa ya bar su zaune sunna bin maganarsa a zuciyarsu
Chapter 21 · 0% Book details