Sashe 40
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Layin Ameenu mai adaidaita ta shiga kira tana kokarin rufe dakin da ky, sai dai yana ta ringing ba'a dagawa hakan ya sa ta nace ita kuwa a dole sai da ya daga a lokacin tana tura kofar dakin Mah da salama ta shiga ta tarda dakin a tatare fess dan har kanshin turare yake fitarwa na wuta, domin yan matan Mah basa wasa da tsafta dan babu wace take son saboda kazanta ta rasa maki
A lokacin da Ameenu mai adaidaita ya daga wayar ya yi salama , Rauda ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Malan Ameenu ina ta kira shiru ko ka bar wayar a gida ka fita nema ne?"
"Raudar ce ke magana?" Radau Muryar Inna ta shiga kunnuwan Rauda hakan ya sa da dan zumudi ta ce" Lah , Ameenu wajen su inna ka zagaya? Dama kiran nan da na yi maka dan nace maka ne yau zan nemi alfarma wajen Mah a kai Ni na ga Abdul sai na taboka mu tafi, ashe ka rigayeni zuwa, dan Allah bani su , ta bani shi na ji rigimamena, na tabata yana nan yana mata rikicin a kai shi aunty"
Magana take yi da zumudi, ta zauna saman cafet hannayenta na dan shafa gefen fuskarta a hankali tana murmushi har ta ji salamar inna da Muryar innar wani iri, sai dai bata saka komai a ranta ba duba da yannayin girma da kuma rashin lafiya da mutun ke iya kuwa da shi, dan haka ta ce" Barka da yama Inna, ya gida yaya kwana biyu? Ina mutumen inna na kawo maki ban dawo ba ko?"
Inna ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin nauyi da tsoron abinda zata fada fiye da yadda ta sanarwa uwarsa kai tsaye ba wani kwane kwane, sai take jin kamar Rauda zata fi koya shiga tashin hankali idan ta ji abin nan, sai dai ba yadda zata yi dole zata sanar mata da fatan Allah ya sa hakan zai zamo sanadiyar maganin damuwar
A tausashe sosai inna ta ce" bari, bari y'ar nan wahali kin ganshi ya zo Malan Ameenu ya sameni bana nan, dan yanzun nan daga gidan mai anguwa na sake fitowa, yau din nan ruwa bai shiga cikina ba bale abinci, na rasa ta inda zan dafa matsalar ban bale har na ga mafitarta, na bayar a min rokon Allah nima ina ta yi, mijin rabona da shi tun jiya da na kai shi makaranta na dawo daukansa malan yace ai ya jima da fita shi ya zatama Ni din ce na je daukansa, y'ar nan na yi kuka na yi kuka na yi cigiya ban ganshi ba, yan anguwa sunna ta tayani dan ko yanzu da Ameenu ya zo mun leka Ni da innar baraka ne gidan mai anguwa dan tun jiyan muka je muka kai cigiya harda gidajen rediyo ama shiru kake ji ba'a da labarinsa ba'a ganshi ba"
A hankali RAUDA ta dakatar da murza gaban goshinta da take yi, muryarta na gaza fita, da kyar da dan karfi daidai lokacin da Mah suka nufo dakinta ita da MALIK, sanye cikin shigarsa ta sarauta, dan shigowarsa kennan saboda likitan da aka kawo daga kasar waje sun zo da likitoci biyu shine suke son takardun Bah da aka masa bincike na lafiyarsa kaf, takardun kuwa a wajen Mah suke a cikin akwatinta ta dakinta dan tunda ta zo idan aka bata ko menene basa takan zo nan ta adana gudun kar a batar a dakin nasa dukda ba kowa ke shiga ba sai ya su ya su, shine ta mike dan ta zo ta dauko ama yannayinta sai a hankali, domin karfin Hali ne Mah ke yi fiye da kowa a gidan nan, dan bata so ko kadan ta nunawa YUSUF bata da lafiya ko wani abin dan ta tabata idan ya ga haka zai tare a kanta ne, bayan yanzu da da ba daya bane, shine fa da ta mike ya kula kamar tana layi ya mike bai yiwa kowa magana ba yake biye da ita ita din da kanta sai da ta ganshi ta yi masa murmushi, shima ya mayar mata ama ta ga alamun ba zai koma ba sai kawai ta yi hakuri suka jero suka nufo dakin nata dan ba wani nisa tsakanin dakinta da bangaren Bah, sunna kawowa daf da kofar zata bude ne ta ji maganar RAUDA sama sama hadi da ruwan murya mai nuni da kuka Raudar na fadin " Inna, wai Abdul din ne ba'a gani ba tun jiya? Tun jiya bai kwana a gida ba ama ba'a sanar min ba? Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une ganinan zuwa Inna ganinan "
Tana fada ta mike daga zaunen da take ta shiga neme nemen abinda bata ajiye ba, sai da ta tuna jakarta karama na dakin Salima da sauri ta nufi hanyar fita tana tunanin tabas ba zata rasa kudi a jakar ba
Tun kafin ta bude kofar Mah ta bude ta shigo dakin hakan ya sa RAUDA ja baya da sauri dan bata tsamaci gannin mutun ba, sai kuma YUSUF ya shigo shima kamar yadda Mah ke kallon RAUDA haka shima ya dubeta ya dauke dubansa yana ɗorawa saman fuskar Mah wace ta fara magana tana kallon RAUDA da fuskarta ta cika da hawaye a tausashe sosai ta ce" Lafiya na ji kamar kina kuka ga kuma fuskarki da hawaye?"
A hankali Rauda ta kifta idannuwanta, hawayen suka sake zubowa, ta kasa rike abinta sai kawai ta karaso ta rike hannun Mah dan ta sabar mata da haka tana kallonta ta ce" Mah, Abdul ne , Abdul ne ba'a gani ba wai tun jiya kin san wajen kakarsa na kai shi, to ban san ba'a ganshi ba tun jiya, shine take fada min yanzu da na kira, dan Allah Mah ki yi hakuri yau na fita na je na neme shi, sannan ki bani dama na sake bincikar uncle dina, zan dawo Mah ama zan nemo su, dan Allah ki barni na je dan su din duniyata ne, Abdul bashi da cikakkiyar lafiya kar aje ...kar aje ya fada wani waje ya rasu........." sai kawai ta barke da kuka ta yi cikin Mah ta rukunkumeta.....
Ita dai idannuwanta a rintse ta ji kamar zasu fadi kuma sai ta ji su basu fadin ba , tana dai jin Mah na dadaba bayanta tana mata shiiiiiitttt kamar wata baby bayan a halin nan da take ciki bata jin shiiiiiiiii zai saka ta yi shiru, sai kawai ta idasa rikicewa tana kuka bilhaki tana kiran ta shiga uku
Har sai da abin ya ishe shi sosai ya girgiza kai a riken da yake da su ya dan yi gyaran murya da kakaurar muryarsa ya ce" Dan dagata mana ke kar ki kayar da ita"
Dif ta yi da kukan da take rairawa wai ita ta ji dadin rungumar uwa, har sai rusheshiyar Muryar nan ta wani katse ta, dan haka ta dan dakata sannan ta dago a hankali tana za sauke ajiyar zuciya, nan ta ga daga ita har Mah din a saman kaffafuwansa masu ɗauke da takalmin fata da damatsunnan hannayensa dake sanye cikin lalausan yadi blue an yi gari da yar ciki ɗinkin sarakai, sai rawaninsa da har ya shafi kanta suke, daga ita har Mah din, karfin rungumar da ta kai ta damki damtsunna ashe nasa ne, hakan ya sa da sauri ta saki ta yi baya tana jin faduwar gaba da dokawar zuciyar da Salima ke yawan fadi a kan yayan nasu
Mah ta dan daki gefen hannunsa ta ce" YUSUF kar ka tsoratar min da yarinya mana, zo nan yar gidan Mah taho babyna" Mah ta fada tana karasawa wajen kujerar dakin ta zauna
Shi abin ya ba mamaki, wai Babyna, ita sam bata wani ji mamaki ba domin ba yau Mah ta fara kiranta da sunnan ba, dan haka ta karasa ta zauna daf da Mah din ta sada kanta
Mah ta kama hannayenta tana kallonta da kula ta ce" Bana son yawan kukan nan RAUDA, saboda mace kike kalubalan rayuwa Allah na iya zubo maki masu girman gaske kin ji? Tabas na san akoy tashin hankali, ama zan fi so ko menene ki fara dubansa da jajircewa, dan kuka da saka damuwa a rai na saka mutun ya kamu da ciwo marar magani dan ciwon stressa ya fi komai kashe bawa , maganinsa kuwa shine baban abinda yake mystere kin ji?"
A hankali RAUDA ke gyada kanta
Mah ta ce" Zaki iya yin hakuri a jima a yi magariba mu je tare ko a saka direba ya kai ki sai na tardo ki?"
A tausashe ta ce" Mah, ina so na je sai na fara dubawa kafin ki karaso"
Mah ta yi murmushi ta ce" To ina da ina zaki duba din?"
RAUDA ta gyara zamanta ta ce" Zan duba makarantar su, mu yi maganar da malamin su, sai kuma mu duba ko'ina a anguwannin na tsakanin gidan da makarantar tasu"
Mah ta gyada kai ta ce" To shikenan, tashi ki bude cen akoy abayoyi ki saka abaya a cikin hijabin nan kar ki fita daga ke sai rigar nan a kasa dan ana ganewa rigar bata da nauyi, bari na yiwa direba magana sai ya ga inda ya ajiye ki in an jima ya zo ya daukeni mu nemo Abdul dinmu ko?"
RAUDA ta mike ta ja hijabinta ta yi masa diban albarka a gaban mutane , a gaban mutane jama'a dan sam.ta sha'afa a dakin nan ba daga ita sai gyatumarta bane, da maza a tsaye kikam jama'a ta je wajen akwatin ta bude ta shiga dubawa har ta ciro bayar da aka ce ta dauko ta juyo ne ta ga kato a dakin nasu wanda sam ta manta yana wajen, Mah na bashi takardu tana masa bayani hankalinsa a kan Mah din
Da sauri ta juya ta diba ta yi bayi da dan gudu har kamar zata kifa, hakan ya sa Mah dagowa ta rakata da kallo, shi kuwa ya yi tsai har sai da ta mako kofar bayin gam ya rintse idonsa sannan ya bude ya gama amsar sakon Mah yana kallonta a tausashe ya ce"Mah ina zaki je?"