← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 117

Sashe 38

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwa ya bude da suka masa nauyi yana tunanin me kuma tsohuwar nan ke nema da shi? Mah ta ce" Ba zaka tashi bane?"

Kin motsawa ya yi, dan yannayinsa ba abin kallon mahaifiya bane, hasalima sai ya sake luluba da bargon nan sosai muryarsa da amo irin na ingarman namiji sannan a shake na mai barci ya furta" Mah, zan tashi, ina zuwa , to ama me zan mata ita wancen din?"

Mah ta yi murmushi, lalle Yusuf yana neman fitina,
Ta juya dan ta bashi fili ta ce" Uwar tawa ce wancen din? Zaka fada ne YUSUF, ka tashi ka yi wanka za'a shigo a kimtsaka ne, saura na ji wata gardama Allah ma kuwa in dandali bakin mutun"

Shiru ya yi idannuwansa da launin ja na abin barci da guguwar da yake farkawa da ita a kulun na ALLAH
Sai da ya ji Mah ta rufe kofar ya sauke ajiyar zuciya ya sauko daga gadon yana jin takaicin Hajia, dan shi itace abar su gwara ba kowa ba

Wankan ya shige, wankan da ya dauki lokaci a ciki sosai domin sai da ya gama dukkan wasu uzurinsa sannan ya fito jikinsa da digo digon ruwa ya daura tawul daya a kugunsa yana rike da karami yana dan goge ruwan kansa ya karasa wajen kofar ya bude ya leka kansa ɗan ya ga a inda yai ga Mah , idannuwansa suka sauka a kan su su hudu, Hajia a saman kekenta , matan Bah a tsaitsaye babu wace ta isa ta koma ko ta zauna

Dan kura masu ido ya yi, gannin du sun sada kai banda Mah da ta kawar da kanta gefe , sai Hajia wace take kallon kofar ta ce" Barka da safia Malik, na tabo Sarkin nadin ne ko ba yanzu ba?"

Harara harara mai kama da jin haushi ya dan sauke mata, yana ayana' tana abu kamar wace nake da zabi salon nadan kiya ta hadani da uwata'

A bayane kuwa sai ya juya ya bar kofar a bude ya komawarsa cikiya shiga saka abinda ya danganci gajeran wando da riga ta ciki da su turaruka sannan ya dauki wayarsa ya shiga amsawa ISHAK tare da bashi damar zuwa fadar da wasu takardunsa muhinmai da suturunsa tare da litafin zanensa, wanda a ciki yake zana duk wani abin da ya danganci gini

Hajia ta yiwa Mah alamun ta fara shiga, sannan ta dubi sauran ta ce" Ku je falo har a gama sai na maku magana"

Da wani bakin cikin hakan suka bar wajen, Hajia ta saka wayarta ta sanarwa Sarkin nadi ya karaso, sannan ta tsaya har ya shigo ya karaso dauke da wata akwati mai shegen kyau mai ruwan maroon

Gaba ta yi ya bita har suka shiga falon YUSUF da salama a bakinsu su duka

Sunna shigowa Sarkin nadi ya duka har kasa kansa a kasa ya shiga mikawa YUSUF gaisuwa, dan a tsaye yake da tawul baba a kugunsa da riga fara yana ta faman dannar waya yana barin sakon msg wa tarin mutanen da suke da daraja sosai a duniyarsa har suke ta rokon son ganninsa da yi masa fatan alkhairi

Ido ya dan zubawa Sarkin nadi, sai kuma ya girgiza kai kawai ya dana kira ya amsawa ISHAK sannan ya katse ya juyo yana kallon Hajia wace ke masa murmushi tana kallonsa dan so take yi su yi zaman lafiya bata zo da rigima ba

Kai ya dauke yana sakar mata hararar kasa kasa, hakan ya sa Mah zarro masa ido da idannuwanta ta masa alamun ya gaisar da Hajiar, hakan ya sa ya karasa yana miko mata hannu ya ce" Cava?"

Murmushi Hajia ta sauke ta kama hannunsa tana kallonsa ta ce" Malik, ka ce zaka kai Ni asibiti baka kai Ni ba, kuma madarata ta kai gangara, sannan ka ga gadon nan ashe ya min tsayi sosai? Bana son sa Ni dai a min marar tsayi" duka maganar nan ta yi su lokaci guda dan burinta ta ga ya sake sakewa, ta san du rikicin da zasu yi da zarar ta yi irin haka yakan sasaubto har ya rarasheta

Kafarta ya zubawa ido, a hankali ya saka hannunsa ya dan bude zannin wajen ciwon ya saka hannunsa yana kallo ya dago muryarsa cen ciki ya ce" Ciwo take maki ne?"

Hajia ta dan gyada kai, hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya ciki ciki ya ce" To ki yi hakuri ai haka karaya take, an kusa kunceta kin ji?"

A ranta dadi take ji ta yi sharar fage dan yi doguwar fira da shi, a bayane kuwa ta amsa shi sannan ta sanar masa Sarkin nadi ne gayanan ya zo dan su fara lesson na nadi sannan ya masa nadin yau ya tafi

Duban Sarkin nadin ya yi ya mika masa hannu da nufin su gaisa sai ya ga ya sake dukawa yana neman fasa masa kunne da kirari

Gaban goshinsa ya dafe ya je bayan kujerar ta ya shiga Turawa har kusan gadonsa sannan ya mikkar da abin kujerar ya mikar mata da kaffafuwanta ya zauna bakin Bed yana gannin yadda mamansa ke nutse , bata da sakewa sosai idan Hajia na waje, ya maido dubansa wajen Hajiar ya ce" Hala kulun sai na je na wunin nan a fada? Tun safe sai dare?"

Hajia ta girgiza kai tana kallonsa ta ce" A'a, a yanzu zaka samu hutu fiye da kulun, zaka fita fada ne idan ka yi ra'ayi, ko in kana son wanzar da shara'a kai da kanka, fitarka fada ba kulun bane in ba baban abu da ya zamo dole kaine zaka tsawatarwa abin, ko karshen wata lokacin albashi dai da sauransu, kana da hutu sosai fa , shine nace wani bangaren kake so a gyara maka muhallin zamanka da iyalinka idan Allah ya nuna mana?"
Bai ce mata komai yanzu kai tsaye ba, mikewa ya yi ya amshi tufafin da Mah ta fitar masa ya shige ciki

Bayan ya shige din Hajia ta kalli Mah, dan a lokacin da aka bada tufafin Sarkin Nadi fita ya yi daga bakin kofar dakin ya dakata
Hajia ta ce" Wannan yarinyar tun yaushe kike rikonta?, ina iyayenta suke ne?"

Mah ta dubi Hajia, sai ta sada kai a tausashe ba da wani rawar murya ba ta ce" Marainiya ce, iyayenta sun rasu, ta dan kwana biyu a hannuna "

Hajia ta kalleta da mamaki ta ce" Shine ba'a taba sanar min da maganar ba?, dan ban isa ba?, bayan wannan ki sani a yanzu lokaci ne da zaki tashinma kanki ki kuma san ciwon kanki, dan Ni tunda nake ban taba ganin yan uwanki sun rabeki ba, yau shine harda barin ƴaƴansu sunna yawo da wata irin shiga a falo? Ki san abinda kike ciki dan a yanzu babu wanda ba zai rabe ki ba saboda daukakar nan!"

Mah ta yi murmushi bata ce komai ba, a ranta kuwa ayanawa take yi' Hajia, Ni ai ba mahaukaciya bace, kuma ina gannin zuwa yanzu idan ban biyawa wani karatun mecece duniya ba da wahala wani ya biya min, Allah dai shi kyauta kawai'

Shi da kansa da ya saka wannan tufafi ya jima yana kallon madubi kafin ya dauke kansa ya sake daukan turarensa mai tsadar gaske ya bi jikinsa sosai da shi sannan ya juya ya fito da hular a hannunsa da kuma macaji dan sumar kansa bai cajeta ba da ya fito a wanka

Da tatausar murya Hajia ta sanarwa mai nadin ya shigo ya bude computer hannunsa ya ringa hasko masa kalolin nadi har sai da aka tsaya kan wanda ya ji a ransa tabas ya masa ya bada damar a yi masa shi

Cikin nutsuwa yake naɗa masa yana masa bayani har ya gama ya dako madubinsa ya haska masa nadin tun daga baya har gaba bayan ya gyara masa rigar da takalmin da ya saka kafa ciki da Safa

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Mah dake kallonsa da murmushi

A sanyaye ya lumshe mata ido wanda ke nuni da zuwa yanzu kam ya fara zubar da du wani makamin yaki, dan shi da kansa da ya kalli hoton nan a madubi abinda ya karanta ba YUSUF din da bane ke zaune, wannan din wani Yusuf din ne wanda Allah ya yi wanzuwarsa a cikin jikinsa..............

Daga nan ya mike Mah ta ci gaba da masa barin turare tana masa addu'a a cen kasan zuciyarta, shi dinma yana adu'ar ne, Hajia kuwa Tata a bayane take har Mah ta gama ta dauki alkhyabarsa ta ɗora masa , ita da kanta sai da zuciyarta ta ringa tsintsinkewa, saima da Sarkin Nadi ya kai kasa kansa a kas ya shiga zuba wani irin kirari mai tayar da tsigar jiki har sai da YUSUF ya masa alamun ya bari hakanan sannan ya mike ya je ya bude kofar ya rike yana fadin" Takawarka lafiya saraki, Takawarka lafiya hamshaki, Takawarka lafiya makaranci, Takawarka lafiya uban talakawa, tafiya salama zama salama mai jinnin Bello Abubakar, talakawa na gaisheka, masu kudi na gaishe ka, sarakai sun kawo gaisuwa, kai ne mai zamani mai tafe da karfin ikon Allah, makiyan ka fadawanka suke MALIK;, ku duka ga MALIK....'

Irin yadda yake jan MALIK din ya hanna da yawa dukar da kawunansu dan zumudin da kunnayensu ke masu da idannuwansu na son gannin MALIK din a yau da ya kwana ya tashi matsayin Sarki, ba nadin ba zatar da aka masa ta jiya ba, bale kannensa dake falon nan da bakin Mah , iyayensu sun dukar da kawunansu ne dan basa son ganninsa koda wasa

Tsayuwa ya yi idannuwansa suka shige cikin na Salima, wace hawaye suka wanke mata fuska, jikinta har tsuma yake na shauki da farin ciki, haƙoranta a fili muryarta har kamar ba Tata ba ta furta" BAH, URS MALIK!"
Chapter 38 · 0% Book details