← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 117

Sashe 11

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya je ya dauko ya kawo ama fir tace ba zata sha ba, wannan shi ya karra daga masa hankali domin idan ta yi fashin sha da wahala in bata KWONTA rashin lafiya ba, a hankali ya so sake fahimtar da ita ba zai taba iya kin gudan jinninsu ba, ama akace ka guji fushin wanda baya gagawar fushi, cikin wani bacin ran kafin ta mike ta nufi dakinta ta ce" Ka shiga tsakanina da A'isha!, ta fita a hanyata, abinda na hadiye na shekarun baya ba zan iya hadiyewa yanzu ba, kanwa take a wajenka , koda yaya ce ina iya dakatar da ita bale kanwa, ta guji budar bakina dan idan ta kirayi YUSUF mazinaci mashayi bata san me zan kirayi nata ya'yan ba wa'inda ba hasashe nake yi ba ko Kazafi, tana yawan kirana *AZAL!* idan aka bibiyi tarihi kalmar AZAL ta yiwa ahalinta kadan , a kan YUSUF babu abinda ba zan yi ba ciki harda rabuwa da UBANSA!"
Daga nan ta yi dakinta ta rufo ta saka ky ta murza da karfi sannan ta karasa wajen gadonta tana rike kanta ta KWONTA jiri na neman summar da ita daga kwoncenma

A falo kuwa da kyar Mahaifin Yusuf ya iya samun waje ya zauna yana dafe kansa da hannayensa bibiyu

A hankali ya bude idannuwansa sakamakon tuno ranar da yayansa ya fito da wani zannin gado a hannunsa rungume da jajirai biyu farare sal masu kama da shi tak tak Duda jajirtakarsu kamar ya yi kaki ya tofar kamanin har sun bace ko dan Allah ya nuna masu cewar ba gardama abinda suke gudu nasu ne? Yan jarirai sun yi fari fat na alamun ba rai a tare da su ya nuna masa, bai ko bashi damar runguma ba ya fice da su yana fadin abinda aka tsara za'a sanarwa duniya cewar ba kumburin cikin haihuwa bane ta yi dawainiya da shi, kumburi ne na kari dake girma tamkar cikin haihuwa yana ji yana gani bai san inda aka birne masa yayansa ba, haka uwarsu ko ganninsu bata yi ba aka yi rufa rufa ga zafin haihuwa na cs ga radadin rashin ƴaƴanta aka dawo gida aka daura masu aure a ranar tare da wasu matan biyu, wa'inda HAJIA ta zaba masa yana ji yana gani bashi da ikon furta ko kalma daya kuma aka nuna aurenta shine karshen daurawa kai fin karfi dai aka nuna ba zata tare a gidanta ba a kalla ta kusan shekarewa a tare da HAJIA , galazawa babu irin wace bata gani da Hajiar da kanwarsa A'isha, yayansa kuwa dama basa ko ga maciji da ita, shi dai bai nuna mata tsana ba ama kuma bai nuna mata kauna ba, a wajen su HAJIA kuwa nan ta ringa tsintar sababin sunnaye masu girgiza zuciya, gashi a lokacin ba damar ta je wajen Tata mahaifiyar saboda ta yi fushi da ita sosai, sai a rasuwar mahaifinta suka amsheta suka yafe mata har suka janyota jikinsu, ama Duda haka babu ruwansu da damuwar dake damunta na dakin mijin da a ganninsu ba gidan aurenta bane, gida ne mai hatsarin gaske , gida ne da jita jitar da ake yadawa a kansa ya sa da yawa ke masa wata irin fasara, su tasu sarautar mai hatsarin da baki ba zai iya misaltashi bane, wani abin ne a bine a ahalinsu ya sa haka ko Allah ne ya kadarto masu haka a rayuwarsu? Allah shine masani, ama yannayin matarsa na yau ya girgiza shi fiye da tunanin bawa

Menene bata gani ba? Bata taba nuna masa ba
Idan yana fada ma Yusuf takan kauda kai ta yi murmushi ne ta ce" Sai addu'a Aban Yusuf"
Ama a yau ta fadi abinda yake gannin shi dai bata yi masa adalci ba
Shin yaya take tunanin zata haifo masa d'a tsatsonsa ya tsana? Yau ko ba nasa bane in dai daga jikinta ya fito ba zai taba tsanarsa ba, bale nasa ya Allah yaya zai iya tankwasa zuciyar wace bata cika fushi ba?.......

🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*

*PAID BOOK*

_Bismillahir rahamanir-rahim._

*7*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳

Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*

A gidan su RAUDA

Tun karfe shida na safe hayaniya ta kaure a tsakar gidan, wace ta hannata mikewa bale ta je ta samu ta dauro alwallah ta gabatar da sallar asubahi, rikici ne wanda yake tashi sama sama, fada ne irin na matar mashayi da mashayi, fadan da farkonsa aka sani ba'a san karshensa ba, fadan da du tsiya da zarar ya nuna zai rabu da ita take komawa ta yi mikis kamar ba ita ba, du gorin da take yi, du masifar da take yi cewar an hadata da balaki an aurota ba'a ciyar da ita, ba'a shayar da ita, an kawo mata rikon ya'ya an zuba mata irin tsiya gayar tsiya ba zata iya ba fatanta Allah ya rabata da masifa da BALAKI, domin auren Umar masifa ne da BALAKI ba komi na, ba karuwa sai raguwa , babu farin ciki sai bakin cikin rayuwa, na kulun hauhawa yake yi ba raguwa ba, da zarar ya nuna wai su saki hannun junna mana sai ta shige daki ya labe ba zaka kuma jinta ba sai ya fita ta fito ta wulakanci su RAUDA da dan uwanta wanda tsoron maman nasu ya saka ko muryarta ya ji sai jikinsa ya kama rawa ya shiga neman wajen buya

Ido Rauda ta rintse sakamakon wata ashariya da Mama ta kyatsa tana fadin" WALAHI baka isa ba, baka isa ba Umaru, kudin da nake binka ai sun fi haka, a kan me zaka ce zaka siyawa RAUDA kayan makaranta da kudina? Kar ta yi karatun mana, karatun nata da ba anfanar uban kowa zai yi ba, yawon banzan da take fita ne kake kira karatu ko me kake so ka daukeni? Yau da ace wannan yarinyar ba y'ar zumunka bace har na yi maka wata fasarar, ama Duda haka zan zuba ido sosai dan WALAHI karya ne ba'a yi y'ar da zan gogi arzunzumi ta goga ba.... ba z........."

Wani irin karan duka da ya shiga kunnayensu ya saka su duka biyun rintse idannuwa, hawayen da RAUDA ke rikewa suka samu damar fita da gurbin idannuwanta shar masu zafi da radadi, shi kuwa kannin nata ya rarafa ya boye a jikinta jikinsa na rawa kirjinsa na dokawa kamar zai summa

Ihun kukan Mama da y'arta ke tashi sama sama tana fadin " Allah ya isa tsakanina da kai, dan na fadi gaskiya zaka dakeni? Menene ba'a yi a duniya yanzu? Ni dai da RAUDA da iyayenta sai Allah ya mana hisabi, tunda suka fadi suka mutu ka zama mashayi ka kawo min ƙatuwar budurwa ka saka min ga wani dama da nake riko, ba zan yafe masu ba kuma kaima ba zan yafe maka ba dukana da ka yi, kuma na fada sai na saka ido a kanku dan ban yarda da mashayi ba, in kuka sha kun san abinda kuke yi ne? Ba zan kyaleka ka wulakantani ba Umaru!"

Shi din da kansa a tsayen da yake yana haki zuciyarsa tamkar zata balo kirjinsa ta fito hawayen ke wanke masa fuskarsa

Gannin idan ya zauna yana iya kasheta ya saka kansa a uku ya saka ya juya kansa na sarawa ya nufi hanyar fita

A lokacin da ya fito waje idannuwansa suka sauka a kan makocinsa da kuma limamin anguwarsu sunna tsaye daga nesa da gidan kadan ama ga dukkan alamun gidan hankalinsu yake

Yana yin ido hudu da su kunya da tsananin takaicin kansa suka rufe shi, a hankali ya dakata ya so juyawa sai dai makocinsa ya ki bashi wannan damar ya karaso inda yake tsaye ya mika masa hannu yana masa Salama
Chapter 11 · 0% Book details