← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 117

Sashe 31

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, ama kuma sai ya rike kansa da kyau yana binsu da kallo har aka bar shi daga shi sai SHAHEED

Da murmushi SHAHEED ya mika hannunsa ya rike nasa na dama , da dayan hannun kuwa ya mayar da rawaninsa ya rufe sosai fuskarsa sannan ya masa alamun su je

Bashi da yadda zai yi sai daga kafa da bin bayansa, domin ya sani dole zai je dakin cen, sai dai abinda basu sani ba shi din da kansa zai zabi RISLAN ne a matsayin ja gabar talakawan Tsatsunburum

Sunna fitowa aka dora masa alkyaba fara dal mai tsayin gaske, bai ankara da sauran rigimar dake gabansa ba ya ga yamadidin mutane a kansa, duk kuwa da rasuwar da aka yi bai hanna busa ba, wato daya daga cikin abinda ya fi kona masa rai, dan ba zai taba mantawa a lokacin da aka naɗa baba baba sarauta an dawo daga binnar mahaifinsa aka saka masa busa, hakan ya sa ya fashe da kuka, yana yi tun karfinsa ama sai da aka naɗa shi, yana kuka Hajia na hawaye Honorable na taya dan uwansa kuka

A lokacin da suka nufi baban dakin taro a lokacin matar Honorable mai dakin tsakiya ta yanke jiki ta fadi, sumamiya domin dif ba numfashi a tare da ita

A rikice ƴaƴanta da abokiyar zamanta wace ta yi iya yinta ita din bata suman ba suka yi kanta , ƴaƴanta na kuka da kiran sunanta su hudu, yan mata uku namiji guda karaminsu , sai ya'yan uwar gidan da ita uwar gidan sunna kiran sunnanta da kokarin bata taimako, da kyar salima ta tuna da waya ta je da gudu ta dauka ta shiga kiran numbar likitar su mace wace ke duba su ta sanar mata ba lafiya a gidan sannan ta dawo ta samu itama Tata mahaifiyar kokari ne kawai take yi dan wani irin gumi ke karyo mata da tashin hankalin da ƙarara yake bayane a fuskarta, ko a jiya bata rintsa ba, a lokacin da Salimar ta tashi tana sallar dare ta ga mahaifiyar Tata zaune ta zubawa waje daya ido, da ta tambayeta sai tace mata rasuwar nan ce ta girgizata, shi yasa ta zauna sosai ta bata hakuri da sake rarashinta kafin ta je saman salayarta ta shiga gabatar da nafilfilun da suka gama zame mata jiki, dan salima babbar makaranciyar Alkur'ani ce, tana matukar ba musulunci mahimmanci, tana karatun lauya ne, wadda a yanzu take mataki na karshe, kuma mai biya mata yayanta ne, shi yasa a kulun take kokarin dan dawo da mahaifiyarta kan hanya a kan lamarin yayansu, duda mahaifiyarta bata fitowa fili ta nuna abinda yake ranta, ama ai su ko da ido ta yi magana sun san abinda yake zuciyarta shi yasa take sakata a addu'a tana nema mata sauƙin abin a wajen Allah, dan ta san ba komai ke rikitata ba sai tunanin yau ko mulki ya dawo hannunsu ba a dakinsu yake ba, dan da wahala a tsallake manya a diro kan kananun gidan, domin kuwa kannensu maza kannanu ne sosai, in dai da ran Bah karami kamar yadda suke masa kiranye, dan sunna kiran mahaifinsu Bah, sai su ce da yayansu baba Bah karfi da yaji Salimar ce ta sa sauran ma suke kiransa haka koda iyayensu basa so, ita a ganninta idan Bah karami ya samu sarauta su ne a cikin gata ba kowa ba, a yanzuma likita kawai zata zo ta duba iyayensu itama ta je dakin taro, fatanta Allah ya sa ta zamo cikin wa'inda zasu zabe shi matsayin uban talakawa, dan ba gudu ba ja da baya a san shine daidai da mulkin zamaninsu, halayyarsa wa'inda yake aikatawa na rashin dadi kuwa ita ta san in sha Allah zai daina, zai daina ne zai kuma nemi yafiyar Ubangijinsa a lokacin da lokaci bai kure masa ba, dan a kulun cikin adu'o'in wa'inda yake kyautamawa yake
Azal 18

"Ka zauna aka ce mana YUSUF" shine Muryar wace ta fi kowa bashi mamaki da ya gani a wannan waje, wace ke cikin tarin taron duk wani wanda ya isa ya saka shi ko ya hanna shi, ciki harda yayunta maza da mata, wa'inda rabonsa da ya gansu da idannuwansa har ya manta, wasu lokutan sukan wucewa ta kusan junna a mota ama baya taɓa barin shi dai su gane shi, kuma rabonsa da ya saidawa masarautarsu mota tun wani taro da suka yi suka daga hankalin mahaifiyarsa ta yi kuka ya kurce su a tsarin bangon litafin rayuwarsa, sai gasu summa a tsaye kamar yadda duk wani mahaluki ke tsaye ana jira sai ya zauna kafin su zauna, zaman da aka ajiye kujera daya tak a tsakiyar filin ake jira ya zauna masu ja in ja din taron su yi, wato MAH

A raunane ya sake duban Mah, a idannuwansa yana yi mata kallon kin san me suke nufi? Mah kin san ba zan iya ba, ama bakinsa ya kasa budewa bale har ya furta wannan kalamai, hasali ma shi a tunaninsa yaya aka yi ta mike ta iya fitowa? Wa ya fitar da ita? Yaya aka yi suka yarda aka fitar masa da uwa cikin zafin ranar nan? Sai kuma lokaci daya ya ba kansa amsa ta hanyar kai dubansa kan Hajia wace ke zaune cikin motar turawa ta asibiti tana kallon nasa itama

Gwauron numfashi ya sauke ya shiga takawa a hankali, cike da sabon abinda ya ratsa jikinsa da karfin ikon izar da Allah ke wanzarwa a duk jinnin jinnin bale kankat ja gabar

A hankali ya kai zaune saman kujerar ya lumshe idannuwansa da kansa dake sarawa kunnayensa na jin umarnin da aka bada daga Sarkin gida cewar kowa ya zauna

Baban wanda ke kare yancin talakawan a rukunin mulki ta gwamnati da yawun gwamna da duk wani mai fada a ji ne ya mike ya karaso ya mika gaisuwarsa wa kowa sannan ya budi baki cike da girmamawa da jajanta baban rashin da aka yi ya dora da fadin " Sako ya same mu a jiya da dare, a lokacin har mun yi shirin zuwa wajen jana'iza da sannin wanda zai maye gurbin mamacin, sako ya same mu cewar ba shi zai hau ba yaronsa zai hau bisa tabbacin da likitoci uku suka bamu cewar eh lalle sarauta ba tashi bace dan rashin lafiyarsa ba wace zai iya jure hawa da sauka bane na cece ku ce da firgicin sarauta na yau da kullum ina fata kowa ya gamsu da bayanina kuma ya yarda da maganar ? Idan da wanda yake da ja ko tunanin akoy wani lauje cikin nadi kan wannan bayani ya yi mana bayani ta yadda zamu katse komai kafin a yi nisa da maganar"

Shiru ya yi sannan ya ringa bin kowa da kallo, har kusan minti biyar, sai ya dora da fadi " Tabatuwar zancen daga gare ku zai saka Ni ajiye jayayata a filin da ya dace na ja "

"An sanar mana cewa ganganci zai saka a ba wanda bai cencenci rikon mulki ba, an ce mana ana so a ba mashayi mulki? Shaye shaye fa ake nufi? Ana nufin shan giya wace Allah ya haramta shanta? Dan kuwa duk wanda ya zamo cikin maye zai iya aikata aikin da bai sani ba , an hanne mu kusantar kanmu da sha, dan sha na saka mu aikata zunubi mafi girman da zamu yi dana sani a rayuwa har mu koma ga ubangijinmu, an tabatar mana rikicin na son rai ne? An ce bayan akoy wanda ya cencenci hawa mulki ake so a ba YUSUF BELLO?, a yau muna tsaye da karfinmu dan dakatar da wannan magana, mulki zai hau wajen da ya dace ne domin rikon talaka ake magana ba rayuwar bariki ba, kamar yadda muka sani talaka rikonsa sai mai Addini, sai mai jin tsoron Allah, wanda zai kiyaye hukuncin ubangiji ta yadda zai ji kan talaka, ina da ja da wannan magana!"
Yana kaiwa karshen abinda ya kawo shi ya koma kujerarsa ya zauna, a matsayinsa na wanda ya isa ya fadi abinda ya fadan shi da kansa ya fada zuciyarsa na rawa, sai dai ya zama wajibi a bi komai yadda ya dace , a ba talaka hakinsa dan ba zasu taba bari a dora wanda bai cencenci hawa mulki ba!

Tunda mutumen nan ya fara magana, maganar dadi take yi masa har aka zo abinda zai kira da cin zarafi da munanawa da kuma wulakantarwa a gare shi, a irin wannan lokacin da ake zaginsa da abinda Bama shine aikin nasa ba, dan kuwa aikinsa shi dai a saninsa taba mace ne, ama baya sha, sai dai ba kowa ya san haka ba, a hankali ya maida kansa ya sada dan ba zai iya duban idannuwan mahaifiyarsa a daidai wannan yannayin ba, shin me zata ji? Yaya zata ji? Ga yan uwanta dake zaginta da abin kulun, shin yaya zata iya jurewa? Bai taba jin takaicin munanan halaya irin na yau ba, dama ta sha fada masa shi mugun aiki ana kiyaye shi, dan idan aka tashi kalubalantarka ba'a ware cewar ka yi kaza baka yi kaza ba, za'a hade jiji da jan kanwa ne a yi maka tawa tsine a duniya, gashi dai ta sake shi

"Asalamu alaikum wa rahamatulah, sunana Jabiru jikan Baba sarki, kwarai nima ina ja da maganar dora mutumen da bashi da iyali wanda ake radi radin halayyarsa mararsa dadin da bai cencenci rikon daraja irin ta sarauta ba, ba zamu iya bashi sarauta ba dan bai dace ya zama sarki ba, a matsayina na dan uwan mahaifinsa wato cousint din Honorable Bello ina da ja a kan wannan magana!" Mutanen da ake yiwa kallon idan sarauta ta kubuce daga hannun famillyn Honorable hannunsu ne zata shiga kennan, wannan shine wanda idan ba YUSUF ba Honorable a wannan karni zai hau karagar mulkin da take ta jinni da jinni a kansa, hakan ya sa kowa ya fahimci ma'anar mikewarsa da kuma karshen furucinsa, ciki harda wace ta janyo dala da Gwauron dutsen wato Nana
Chapter 31 · 0% Book details