Sashe 8
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yannayin da yake ciki na damuwar gannin dare na neman tsalawa bata shigo ba bai gushe a fuskarsa ba ya ce" Daga ina kike yar gidan Abu har dare ya yi haka baki shigo ba? Tara fa je neman yi"
Ajiyar zuciya ta sauke, tana ji a cen kasan zuciyyarta tanada wanda idan yana cikin hayacinsa yake tunawa da ita, tanada wanda ke damuwa da shigowarta in har yana cikin hayacinsa
A sanyaye ta ce" Ka manta yau ne auren Bara'atu? Daga kaita muke Abu"
Ajiyar zuciya ya sauke mai nunin ya samu salama a zuciyarsa a sanyaye ya ce" Raudana ki yi hakuri da yannayin rayuwa kin ji? Ki ci gaba da sakani a addu'a, kin ga wannan lokacin ban kashe kudin ba na dawo da na tuna da ke da kanninki, in sha Allah Ni na san zan daina abinda nake yi na zo na kula da ke, ki kama mutuncin kanki kin ji yar gidan Abu?"
Idannuwanta ta ji sun cika da kwallah ya Allah, inama ace ta wayi gari bafanta ya daina dukkan rayuwar nan da yake yi ta wulakantar da kai? Da sai ta fi kowa farin ciki, kuma tana kyautata zaton samun yanci irin na wasu ya'yan masu yanci, sai dai kashhh, haka yake fadi kulun, kuma Adu'ar kuwa yi take yi, ama ko yanzu alhamdulilah mutumen da idan ta yi zafi za'a kawo shi a watsar ya sha bashin giya yau har ya riko cenji? Kwonci tashi wata rana ana iya wayar gari a ga ya daina abinda yake yi din, babu abinda addu'a ta bari da izinin mai duka
"Nima burina ki samu miji na maki aure, in sha Allah kafin na mika ki dakinki sai na daina shan komai kin ji Raudana?" Rauda ta sakar masa murmushi ta mike ta shige a hankali ta fitar masa da yar yololuwar katifarsa ta shinfida masa sannan ta koma ta dauko sangenta ta daura masa ta masa sai da safe ta shige dakinsu ita da kannin nata ta raba ta KWONTA ko tufafinta bata cire ba, dan burinta ta samu hutun dake hadasa mata ciwon kai, sosai kanta ke ciwo rashin gata ya sakata bin rana dan nemowa Mama kudi
_______________________________
Fada
Tunda aka sanar da shigowarsa fadar ya saka duk wani mai motsin kai daidaita kansa
Ba harkar kowa zai shiga ba, ama kwarjininsa da jinnin dake yawo a jikinsa ya saka duk wani marar ji ke kama kansa idan zai shigo gidan koda na second daya ne
Gannin motocin dake parker ya saka shi dan tabe baki ya bude motar ya fice da hannunsa ya yiwa su Ishak alamun su zauna a ciki kar su fito, dan mahaifinsa na nan , ko me yake tsakaninsa da kakarsa ba zai so mahaifinsa na fada baya ji ba
Bai damu da muryoyin da yake ji sama sama kadan na tashi a baban falon ba
Ya dana kai yana salamar da shi kadai ya ji abinsa a cikin zuciyarsa
Hular dake kansa ya cire bayan ya sauke idannuwansa a kan duniyarsa, mahaifiyarsa, wace bai san cewa harda ita a irin zaman nan ba, duba da ba lafiya ne da ita ba kulun cikin ciwo bai yi tunanin tana nan ba da daren nan, tunda ba gida daya suke da sarakuwarta ba wace ta dora Mata karan tsana tana kiranta da lalura ce zama da ita kulun ciwo har ta karra rikita mata yannayi da masifarta, har hakan ya zo ya shigar da fitinaniyar gaba tsakaninsa da ita , dan ba zai taba iya amincewa yana ji yana gani haka na faruwa ba!
Bai iya kallon kowa ba sai da ya karasa har daf da mahaifiyarsa ya cire hular kansa ya duka har kasa ya kamo hannayenta da ya ji su dumi sosai ya dora a gefen fuskarsa kasa kasa ya ce" Khalb, me kika fito yi bayan na shinfidar da ke dazu?"
Murmushi ne ya subuce mata a saman lebenta, tana kallon yaronta, wai ya shinfideta sai kace yarinyar goye ya dai kofar mata y'a ya sakata hawa gadon dole wai jikinta da zazabi , to bayan fitarsa ne mahaifinsa yace ta fito su gaisar da HAJIA
A hankali ta ce" Baka gaisar da mutane ba BIYA MARADI"
Sai a lokacin ya sauke dubansa a kan mahaifinsa, wanda shi dinma shi yake kallo da tarin abubuwan dake cikin zuciyarsa
Dan musmushi ya sakar masa yana dauke dubansa a hankali daga kansa da girmamawar da ta zame masa wajibi wace mahaifiyarsa ta yi yaki kan dorashi a haka bayan ta fada masa cewar ya guji fushin ubangiji a kansa, babu ruwansa da tsakaninsu, ko me zai mata nasa ido ne babu ruwansa, ama ina, sai da suka yi abinda ya daina gannin girmansu, domin du irin yadda ta ringa gujewa wasu yan wulakanci lokaci zuwa lokaci tsakaninta da su sai da suka ringa yi a gabansa, ya zamto du irin soyayar da kakarsa ke masa shina yake yi mata tsana mai karfi Tata ta shiga zuciyarsa, saboda bata ragawa mahaifiyarsa a gabansa
Sai da ya gama bin kowa da kallo, daga inda yake tsugune gaban mahaifiyarsa ya yi masu gaisuwar jimula ta hanyar fadin" Sanunku dai"
Kanwar mahaifinsa ce ta tabe baki tana dauke kanta a ranta tana ayana' Haka fa, dan so wanda aka daurewa, ana iya zagin namu ya'yan tassss ama banda shi, in iskancin ne da rashin mutuncin ya dame kowa, nan dan rashin da'a har ware kansa ya yi daga cikin familly ama kuma a haka ake masa tarbar da ta fi kowace mutunci a cikin ya'ya, ba damuwa shi din da ake so sai ya kawo abin kunya a wannan ahali da izinin mai sama!'
Sai dai du bacin ranta ba zai fito fili ba, bakinsa a zuciyarta, dan HAJIA dake wajen, dan du abinda za'a fada banda zaginsa a gabanta, basa shan inuwa daya da junna ama kuma kowa ya san tana shayinsa
"YUSUFA, gaisuwar Kennan ?" HAJIA ta fada, da muryarta mai dauke da tsufa da alamun rashin lafiya
Sarai ya ji ta, ama ya yi tamkar baya wajen, har sai da suka ringa mintsininsa bibiyu mahaifiyarsa da mahaifinsa sannan ya yi dan murmushi ya kallo wajen da RISLAN ke masa alamun ya gaisheta mana, ga janwar RISLAN din tunda ya zo kanta ke sade tana wasa da yan yatsunta zuciyyarta na dokawa da rigimar da take son rajabowa kanta
Kansa ya cire ya maida kan hajiar, kamar daga sama ya ce" Sanu fa"
Sai kuma ya daure fuska yana dauke kansa
Sai da HAJIA ta sauke ajiyar zuciya na bacin rai tana kallonsa ta ce" Shikenan gaisuwar? Shin baka ji na karye ba? Ko baka ji ba da ka shigo yanzu ai ka gani ko? Ama maimakun ka min gaisuwar da ta dace da tausayawa sai kace da Ni sannu? Haba YUSUFA "
"Haba HAJIA, haba HAJIA, wai kar ya gaishe kin mana, dan Allah kar ka gaisheta Yusuf sai me? In ba dan sarkafa irin ta HAJIA ba yaya za'a yi uwarsa ta ki ki shi ya so ki? Ba zai taba sonki ba HAJIA ko me zai same ki ya same ki ba damuwarsa bace, to wai da wane zai ji ne? Mutumen dake fama a gidan giya da kuma bin mata yaushe yake da tunanin tausayin wani nasa ko jin kai?" Kanwar mahaifinsa ke fada da yannayin hayaniyar da ta dan lafa bayan shigowarsa
Mahaifinsa me ya fara maganar shima ransa bace ya ce" A'isha kar ki saka mahaifiyarsa a ciki, yaro ne ka haife shi baka haifi halinsa ba, da ace halayar mahaifiyarsa ya yi da mun ji dadi, ama yaron nan sam baya jin magana, ba sai kin hada da mahaifiyarsa ba, bata da laifi a halayarsa, itama babu yadda zata yi da shi ne, giya kuwa da mata ai su ya ba gaba sai hakuri"
Kansa ya sake sadawa sakamakon matse hannunsa da mamansa ta yi
HAJIA itama ta budi baki rai bace ta ce" Kin cuceni Balaraba, ban san me na maki da zafi ba, kin yi tsaye tsayin daka kin hadasa gaba da jikana, Ni da ke sai dai Allah ya saka min dan ba zan taba yafe maki ba, domin inada iko a kan yaron nan kuma Allah ya sani!"
"Dan Allah ku yi hakuri" RISLAN ya fada a sanyaye yana jin zuciyarsa na karyewa, da yake da fashewa da kuka kamar yadda kanwarsa ta fashe da shi dan ana zagin Yusuf , dan sauran ya'yan tunda ya shigo suka fece, itama tana zaune ne saboda Mamanta na wajen, bata san haka zata faru ba da bata zauna ba, shin yaya zata yi da ranta a kan kiyayar da mahaifiyarta ke yiwa Yusuf?, Mamanta na masa kiyaya wace ta kazanta ita gashi Allah ya jarabeta da jarabtar dake neman halaka tunaninta, a Tata kadarar rayuwar tana ji a ranta koda makashi ne Yusuf tana so, ko menene hakayansa ta ji ta gani zata iya rayuwa da shi a haka, dama tana daya daga cikin masu masa yaki a gidan nan, ko yanzu itace ta tunawa kakarsu baya so fa yana waje kishiyoyin mamansa na nan ai kuwa kakar tasu ta salami kowa sai su ya su, gashi su dinma sunna neman daga masa hankali, dan a yadda kansa ke sade daga inda take tana gannin tarin zufar dake taruwa a goshinsa
Itama muryarta a sanyaye sosai ta ce" Mama dan Allah ki yi hakuri ki bar yiwa Yaya biya maradi haka"
Idannuwansa da suka kada suka yi ja ya dago a karro na biyu ya zubawa mahaifinsa su, sai kuma ya dauke ya sake duban mamansa wace kanta ke kasa ba zaka iya gane hallin da zuciyyarta ke ciki ba
Hannayenta dake kafadarsa ya kamo a hankali ya dan murza sannan ya mike daga gabanta ya maida hularsa saman kansa ya juya da nufin tafiyarsa
HAJIA ce muryarta na rawa ta ce" Tafia zaka yi ko kallona ba zaka yi ba?"