Sashe 82
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
shigowa ta yi ta duka har kasa tana miko jakar Amnah sannan ta juya kanta a kasa, dan a yanzu a gidan nan idan akace an aikeka wajen gimbiya ka kama adu'ar Allah ya raba ka lafiya da ita kennan , dan abu kadan zaka yi ta saka ka a uku, ta janyo maka tashin hankalin da zai sa ka tsani kanka ka tsani zama a masarautar
Jiki ba karfi Salima ta kawo mata jakar ta ajiye mata, tana dubanta a tausashe ta ce" Eh lalle ba ita ta haifeni ba, kuma matar mahaifina ce , sai dai Ni tunda nake da ita alkhairinta na sani ba sharinta ba, rayuwa na juyawa kala kala, na yi wayo tun daga yarinta, zan iya ce maki ban taba haduwa da abinda zai sa na ji ta daukeni kamar wadda bata haifa ba, kin san menene aunty Amnah? ita rayuwar kanta idan ya zamo ka sakawa ranka kowa na iya cutar maka shikenan, ka shiga uku, domin babu wanda zaka yarda da shi ko ka yi mu'amala da shi da zuciya daya, bale idan kai dai a rayuwa tunaninka za'a yi maka asiri ko an yi maka ne? to in sha Allah ka ginawa kanka mugun ramin da zai hannaka kwonciyar hankali........, Bana tare da Mah dan arzikin dake tare da ita, idan arzikin ne kamar yadda kika fada iya wanda ya zuba min a matsayina na kanwarsa ya isheni rayuwa, bale ban cika saka buri a raina ba, sai dai jinina ne shi, mahaifiyarsa kuma yawa ce Amnah....ki huta lafiya"
Daga nan ta ajiye mata jakarta ta fice, tana jin gaba daya matar yayan nata na fice mata a rai, dan walahi tunda ta zo take son gane wace ita? ta gane wasu halayar ama bata gane wasu ba , a yanzu kam tana kukan wannan jigo da aka yiwa gidansu, dan bata tunanin in har ya isa a kirayeshi bango , ko kuwa uwa mabada mama!
Tana fita itama ta ja dan siririn tsaki, kasa kasa ta furta" Dama yaya zaki yi ya kasa isarki? daga ke har uwarki abinda ke iya isarku abin siyan jakata ne, kuma fa ban ga laifin ki ba, kawai dai mamaki kike bani , ama kuma kina da wayo daidai misali tunda kika iya bin inda zaki ji zuma ziryan ba mai haɗe da shuga ba, sai dai dukanku zaku yi bayani ne, dan walahi walahi babu shegiyar da zata rabar min miji idan ya shiga hannuna, zan ci gaba da nuna masa ban san ciwon kaina ba har ya shiga hannun nawa, a nan ne zaku san *AZAL* ta shigo maku gida
Rai bace ta ringa neman layin abokinta, abokin sharholiyarta, dan daudun nan
wayar na fara ringin ya daga a lokacin yana restaurant dinsa, domin abinci yake yi na siyarwa, da kararamba ya kama kirari yana fadin" Barka da yamaci uwar dakina, amarya kike kuma uwar gida a gidan SARKI SULTAN MALIK YUSUF DAN BELLO, ke dama matar manya ce bale kin gama tabatar mana, ci uban kannanun kwari masu rike jakar jaka dari, ke ce uwar masu gida, ke ce uwar masu kudi ke ce......."
"Habu!" Amnah ta katse shi, duda irin yadda take jin dadin yadda habu ke wasa ta, a yau sai ta ji batta bukata, ta fi son jin abinda take son ji
Da yannayin bada umarni umarni ta ce" Ka hau whatsup zan turo maka hoton wata yarinya, ama ban sani ba a yadda na dauki hoton ko zaka gane ta?, ka dai hau ka gani na dauki hoton ne ranar da ake sadakar satin mijinta dan ina son Sannin Wacece a yau yau!"
rigar dafe dafensa ya shiga kuncewa yana fadin" Yanzu kuwa"
Dan yannayin muryarta ya sa ya gane akoy wata gwarama tare da uwar dakin nasa, shi kuwa ba zai yi sanya ba dan a duniya ita fa uwarta ne gatansa, sha nawa yake karyewa, su ke tada shi a nemansa na yau da kulun,
Zama ya yi ya bude data sannan ya shiga wajen sakwaninta
bude hoton ya yi, ya shiga zooming din hoton a ransa yana ayana' in dai ta kwana ta tashi a Tsatsunburum ba zata boye min ba, kai ko a Damagaran ne makociyar Tsatsunburum da wahala ta bace min'
Zooming din hoton yake da mamakin Wacece dare dare a saman cinyar Hajia baba? Hajia wato kakar MALEEK, domin halayar Hajia babu wanda bai sani ba bako da dan gari, an san wace Hajia a fannin tsaurin halaya da kamewa da kin yin wasa da jikoki, an sani a duniya YUSUF kawai ke rikitata ya yi yadda ya so da ita, bayanshi babu wanda ya isa har baban shi
Fuskar yake kallo yana karawa
Hoton ya dauka ya turawa Nafeesa yana sake dan zarro idannuwansa da tunanin kai anya? kai a'a, ba haka bane
ya yi katari Nafeesar na online, yana tuna mata ya dana mata voice note ya ce" Wannan kamar RAUDARIYA y'ar larabawa?"
Nafeesa sai da gabanta ya fadi jin sunnan RAUDA, kawarta a da, ko tace kawar kawarta wace a yanzu bata fatan ko hanya daya su hada bale wani abin ya haɗa su, hoton ta sake kallo, ita dai bata gane Hajiar ba, ama kuma ta san cewa lamarin RAUDA a yanzu ya fi karfin ta tunda ta koma rayuwa gidan su Ogan oganta wanda yake sarki a yanzu ta san ita dai ta sai hange
Voice note din ta danna itama ta sanar masa kwarai itace
kasancewar ya fi son ya tura mata rikakakiyar sheda sai kawai ya sake danna wani voice din yana fadin" Dubata da kyau Nafee tamu , itace wanda ta yi maki shashawar nan? dubata da kyau fa"
Nafeesa ta maida masa amsar cewar itace ko mutuwa ta yi ta dawo na zata mantata ba, dan haka ya tura mata voice din baki dayansu, a lokacin har an fara kiraye kirayen sallar magariba, ama babu wanda ya yi alamun zai tashi dan gabatar da abinda zai kwace su gobe kiyama, sai suka fi gane karasa zancen da suke gannin shi ne a gabansu a yanzu
Da yannayin mamakin jin abinda ya sake fada mata na Wacece RAUDA kamar yadda Nafeesa ta sanar masa a lokacin da ake rade radin an yi mata shashawa ya je ganewa idannuwansa tsaf ya zube mata, ya dora da fadin" Ni baban abinda ya dameni shine ganninta a jikin Hajiar sarakai, to me hakan yake nufi?"
Da wani bacin ran da kuma mamakin karfin halin Rauda Amnah ta danna masa kira, yana dagawa ta ce" Kana ji? ka tambayi kawar nan taka ta sanar maka dalilin da ya hadata da dangin mijina, ina jiranka komai dare ka ji?"
Sosai ya gane akoy baban abinda zai hada Amnah da RAUDA, dan Amnah bata cika bin didigin abu ba, idan ka shiga hanyarta ka kure bata mata rai a sawake zata saka a koya maka hankali ne, dan ta zuba makudan kudi a daukeka a baka wahala baya ce mata komai, dan haka da gagawa ya dannawa Nafeesa kira, ya ringa yi mata tambayoyin har ta dire masa aya, ayar da ta firgitashi, dan tunda akace Balarabe mai kyautar manya ya rasu, kuma dukiyarsa ya barawa matar da ya aura gaba daya dukiyarsa yake cigiya da neman Wacece, dan kuwa burinsa ya ji ko Wacece ta yadda zai je ya zama ɗan dakinta, dan ya san idan ya samu karɓuwa ya warke daga cutar talaucin dake damunsa, sai dai wata cutar ba dai wannan ba
Bayan ya kashe kiran ya jima yana tunanin amsar da ya dace ya sanarwa AMNAH, dan kuwa ya fi so ya fara jin musababin neman Sannin Wacece RAUDA da Amnah ke yi kafin ya san irin amsar da zai bata, saboda nasa aljihun ba dan komai ba!
A lokacin da ya yi kiranta sanar mata ya yi gashi ga Nafeesa ama tace sai an dire mata kudade zata fadi wacece RAUDA
Amnah kuwa a lokacin an zo yi mata kwaliyar be kamar yadda ta buƙata, a dole ta sasauta maganarta kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata, cewa ta kula daga nan har a sadata da dakinta ta kiyaye duk wani abin da zai sa ta shiga ido ko bakin makiya, ta bari har ta je ta ga takun uban kowa kafin ta maida martani daidai da amsar kowa
A hankali ta furta" Ka ajiye min accunt numba, ama ka tabatar har tarihin uban ubanta ka jiyo min da kuma abinda ya hadata da dangin mijina ka ajiye min labarin a nan zan saurara idan halin saurarar ya kama!"
Jiki na bari ya tura mata account numbar, sannan ya fice a restaurant din ko sallar bai yi tunanin yi ba yace sai ya gama kashe wannan wutar zai yi, ya haye mashin dinsa ya nufi gidan su Nafeesa, dan samun cikakken bayani daga bakinta ya sanarwa AMNAH, dan ya san yau sai ya shaki kudin da bai taba shaka ba a zamantakewarsa da ita, tabas ya san akoy balaki kuma in sha Allah sai ya karu da wannan balakin!
Tana yin transfer na makudan kudi ta maido hankalinta kan mai kwaliyar da aka kawo mata