← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 117

Sashe 12

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun nasa ya kalla, sai ya ringa jin dari darin bashi nasa dan na makocin nasa a wanke tasss ga tabjinsa a hannunsa yana ja har wani kanshi yake, shi kuwa nasa harta miyar da ya ci jiya da dare bai wanke ba, sai kunya ta saka shi kallon nasa hannun ya nemi nokewa

Karasowar liman ya riko hannun nasa suka yi musabahar dole yana kallonsa shima a tausashe ya ce" Shin ka yi sallar asubahi?"

Wata kunyar ce ta sake kama shi, to rabonsa da yin Sallar asubah a kan lokaci ai har ya manta, dan haka ya sada kai yana cike da jin da kunya

Ajiyar zuciya liman din ya sauke a tausashe ya ce" Mu je ka gabatar da sallah, itace abinda take gaba da komai a yanzu, bismillah"

Kamar kanninsu ko dan gidansu suka saka shi gaba, ba da niyar tozarci ba, a'a da niyar taimakonsa, dan kuwa kasancewarsa mutum dake rayuwa cikin halin maye bai Hanna masa girmama duk wani mutumen Anguwar ba, datijawan Anguwar na binsa da Adu'ar shiriya, da kuma fatan Allah ya shiryi matarsa, dan babu wanda bai san wacece ita ba, dabi'unta a bayyane suke ba a boye ba, irin yadda take yiwa Rauda kuwa da kanninta ya zamo kowa na yi mata wani kallo, gashi dai kiri kiri tana son mayar da yarinyar kamar wata mai zaman kanta, a koda yaushe cikin zance da masu motoci a kofar gida, a koda yaushe tana karbar baki a kofar gida

Makocinsa na hannun dama ne da liman din suka zauna sai da ya gabatar da sallar asubahi har karfe bakwai na safiya ta gota sannan suka zauna tare da shi, cikin nutsuwa da kula suka ringa yi masa nasiha da nuna masa irin illar wannan rayuwar, abinda ya riga da ya sani, ya kasa zaunawa ya yiwa kansa fada ne saboda bashi da mai tunatar da shi

A tausashe Liman ya ce" 300Babu yadda rayuwa bata zuwarwa bawa, kuma komai girman laifinka idan ka tuba Allah mai karbar tuban bawansa ne, babu abu mafi hatsari irin maye, maye bashi da anfani Malan Umar, mai yin maye bashi da daraja kuma bai san abinda yake yi ba , kana da ya'ya yan mata, ga namiji masu bukatar taimakonka, dan Allah ka ceci kanka ka daina wannan halaya, ka rufawa kanka asiri kar ka samu matsala a wajen aikinka, domin rayuwa yau kana gannin idan mutun bashi da aikin yi damuwa ce, gashi kai din nan uba ne kuma Magidanci ne malam Umar"

Makocinsa Elhaji ashiru, mutun ne mai abin hannunsa daidai gwargwado kuma mai kyauta da taimako, ya jima yana da burin gannin sun samu kusanci da makocin nasa dake gaishe shi idan ya ganshi ko a ina ne Allah bai yi ba sai yau, ya Dube shi da kula sosai ya ce" Kowani bawa da irin tasa jarabawar makan Umar, kuma kowa lalube yake yi , babu abin tsoratarwa da wannan duniyar sai irin yadda babu wanda ya san ranar mutuwarsa, idanma babu mutuwa malam Umar Akoy tsufa wanda ke yiwa mutuwa fadan garaje gareta ta bar bawa da shi ta gani, malam Umar duniyar nan mutun ya yiwa kansa abin kirkima yaya ya kareta bale yana wasa da damar da Allah ya bashi? Bama kamar sallah da kiyaye hakokin ubangiji, ga nauyi a wuyanka a rataye, kaine uba kuma uwar ya'yan nan, ka yi kokari ka fi karfin zuciyarka ka fuskanci rayuwarka ka daidaita abinda ya dace ka daidaita, idan kana bukatar taimako ko na menene ka same ni in sha Allah Ni zan kawo dukkan talafin da ya dace, kana da halaya masu kyau, domin kaf Anguwar nan babu wanda zai ce ga abokin gabarka ko wani abin ya haɗaka da wani saboda dukiya ko ya'ya, hakan kuwa baban ALKHAIRI ne shi yasa yanzu na zo shiga gidana daga masallaci na ringa jin hayaniyar nan na kasa hakura na tabo liman muka yi jiranka, ba dan mun saka maka ido a shige da ficen gidanka bane, a'a, damuwa muka yi da dan uwanmu musulmi muka kasa hakura sai mun sauke nauyin hakin makotaka "

Sosai uncle din Rauda ya karra jin zuciyarsa ta yi sanyi, hakan ya sa shima ya gyara zamansa yana sauraron nasiharsu da kuma tunatarwa a kan gobe kiyama da kiyamarsa, ya shiga halin tunanin idan mai kasancewa ta same shi a irin wannan halin? Me zai cewa ubangijinsa? Tsoro ya kama shi ainun hakan ya sa ya zauna tare da su sunna ta zamtawa

A cikin gida bai san ya fita ya balowa RAUDA gagarumin rikici bane

A lokacin da ya fita Mama ta gama kukanta ta mike ta nufi dakin su RAUDA ta bankada kasarin dake kofar dakin ta shiga rai bace ta mika mata hannu ta ce" Bani!"

Gaban Rauda ya yanke ya fadi, dama ta san a rina wai an ari zanin mahaukaciya

A hankali bayan ta sake riƙe hannun kanninta dake ta rawa ta ce" Mama jiyan dare na yi gudun kar ya min shi yasa na dawo gida dan kar na yi dare ki kasa barci ba'a rufe gida ba"

Sai da maman ta dan kankance ido tana kallonta kafin ta shigo gaba dayanta ta ja yar kujerar tayani tsegumin da ita ta sanyota dakin ta zauna tana kallon Rauda ta ce" Ama ban taba gannin yar bakin ciki, marar mutunci irinki ba, ban taba gannin munafuka algunguma irinki ba, dan ubanki na taba zaman jiranki idan kika fita ne? Nan ko zance kike yi sai ki kai karfe goma sha biyu na dare a waje kina yi na taba zaman jiranki ne? Ko saurareni da kyau na rantse Miki karya kike yi, kin ga a yau idan har baki bani abin kirki ba sai na maku horon yinwa ta wata guda cir kuma sai kun bar min gidana , tunda kin san ba ubanku ke biyan haya ba, ke in banda raini da wulakanci da bakin ciki har nice zaki kawowa wannan maganar? Ai ba ubanki ya kawoni duniya ya tafi ya barni da wahala ba bale na zauna ina ciyar da gandamemiyar kamarki a banza ba, na fada maki kirarki ta ki nemo min kudi ce, ba ruwana da wa ta yaya! Matsalata kudi, idan kuwa tsiyar da iyayenki suka mutu cikinta zaki nuna min ba matsala, dama ke kin san har ki mutu ba zaki mallaki abin kanki ba, ama Ni WALAHI sai kin nemo min in ba haka ba......."

Da karfi ta janyo Abdul Hakim ta rike hannayensa ta kashe shi da marin da ya saka RAUDA saurin mikewa ta janye shi jikinta na rawa ta kafe fuskar Mama da kallo Maman kuwa ta mike tana kallonta itama ta ce" Dukana zaki yi yar mararsa mutunci? To WALAHI na fada maki idan baki nemo min kudi ba sai na halaka wannan kafin na halaka uban baki kema na halaka ki, ba kin fada min saboda su nake taka ko ba? Zan ci gaba da taka ki ko bayan na halaka su in dai kika yarda kika yi wasa da umarnina y'ar matsiyata mai shegun idannu kawai, ki miko min shi ya je ya kai surfen masara tunda ba ubana dake kabari zan taso ya kai ba!"

A hankali RAUDA ta sake tare hannunta tana kallonta a tausashe da yannayin tsarin halitarta ta ce" Ki ba almajiri ya kai zan biya, ki bi Ni bashi zan kawo maki"

Dan tsura mata ido ta yi kafin ta juya ta fita tana sababi da aibata RAUDA, da yawan lokuta takan so ta kai hannunta jikin RAUDA sai dai tun ranar da RAUDA ta riki y'arta ta yi mata wani tsinanen duka dan ta ga Maman na zagin iyayen Rauda ana zama lafiya itama ta kalleta ta zageta ita kuma ta nuna mata bata da hankali Maman ta yi ta yi ta kwaceta ta gaza karshema da Raudar ta yi kukan kura ta hankade Maman da y'ar Tata sai da Maman ta fi wata tana zuwa ana murza mata bayanta dan ta baya ta je ta fada ta ji rauni sosai, shi yasa idan Raudar ta mike tana huci sai Maman ta ringa kiyaye abinda ke saurin sakata fita a hayacinta wato zagin iyayenta

Mama na fita Abdul Hakim ya rukunkume Rauda yana fashewa da kuka ya ce" Aunty tsoronta nake ji, kasheni zata yi"

Itama zuciyyarta ce ta karye ama ta ki nuna masa a hankali ta zaunar da shi ta zauna ta dora kansa saman cinyarta tana shafawa a tausashe ta ce" Dama Akoy wanda ya isa ya karar da kwanan wani in ba lokacin mutun ne ya yi ba? Haba boy din aunty, ka daina fadar haka ka ji? In sha Allah babu abinda zai sameka sai abinda Allah ya kadarta maka ka ji? Fada minda me zaka karya yau? Zaka je ka siyo ne ko na je na siyo maka? Yau zaka je makaranta kuwa an kanena?"

Ajiyar zuciya ya ringa saukewa a jejere da sauri ya gyada mata kai ya ce" aunty zan je, kin ga Malamin mu na islamiyya yace ko me aka yiwa bawa ya barwa Allah, sakayar Allah ta fi ta kowa, Allah zai saka masa ya saka shi a aljanna ama kuma yace bawa ya kasance mai yafiya, na yafewa Mama aunty kin ji?"

A hankali ta dauke hawayen gurbin idannuwanta ta lalubo kudin dake cikin rigar Mamanta ta mika masa dan idan bata saka kudi a nan ba tana kwonce za'a lalubeta a kwashe Abinda ta ajiye, gashi nauyinta da na Abdul Hakim a wuyanta yake, Mama na ikirarin hana masu abinci dama ba basu take yi ba ai
a tausashe ta ce" Maza karbi je siyo mana abinda ranka ke so bari in zuba maka ruwan wanka idan ka dawo ka yi sai mu je na kaika makarantar daga nan na kaika wajen inna kaka zaka je?"

Cike da farin ciki ya amsata kan zai je kafin ya mike ya tafi da gudu daga gidan danma kar ya hadu da Mama ko yayarsa su daki banza su kwace kudin
Chapter 12 · 0% Book details