← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 117

Sashe 114

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe ya ce" Sir, dan Allah idan wani laifi na yi ka yi hakuri ka yafe min, na kasa gane dalilin da yasa ake hannani zuwa inda kake bayan kaf cikinsu babu wanda bai san tskaanina da kai ba, ya zamanto Taj har hannani zuwa gidanka na cikin gari ya yi, dan Allah ka yi hakuri"

Yusuf Ya idasa cire babar rigar da ya wuni da ita yana jin da wahala kuma ya iya mayar da ita jikinsa dan yau an sha gumurtu da ita, a nutse ya ce" Ka san dare ya yi yanzu, kuma inada iyali, zan tabo ka"
Daga haka ya katse kiran ya idasa tubewa ya bar gajeran wando a jikinsa sannan ya nufi bayi da takalmin wankansa ya shige a zuciyarsa ya gama sakawa ransa tabas zai yafewa ISHAK a ci gaba da zaman tare ama idan shima ya daina halayan da suka hadasu abota, sai dai zai yi zama da shi na zumunci ne kawai, daga wannan baya tunanin akoy kari dan a zuciyarsa ya riga ya kamu da tsarguwa da lamarinsa

RAUDA na shiga kicin dinta ta kunna fitilun kicin din ta shiga nazarin abinda zata dora

A dole ta karasa wajen wayar dake jikin bango ta daga ta yi kiran bangaren masu aiki

Wayar na daukan ringin aka daga da salama

A nutse ta amsa sannan ta furta" A turon mutun daya kicin "

Da sauri chef din kicin din ta amsa da " Yanzu kuwa ranki ya dade" Sannan ta ajiye kiran ta taso ta taho da kanta saboda aikin uwar gidansu ne baki daya

Tana zuwa ta samu RAUDA har ta fitar da kayan aiki, ta fara wa'inda zata fara dan ta gama da gagawa
da girmamawa ta gaisheta , itama ta amsa da kula sosai da kuma ba chef din girma ko dan finta da ta yi a shekaru da kuma sabon da ya shiga tsakaninsu, dan tunda aka kawo RAUDA kulun tare suke yin girki, gaba daya firarta suke yi idan suka zauna da fatan Allah ya sa ita din ba kamar Amnah bace, domin Amnah suma bata masu da sauki ba, sak ta nuna masu bayi suke bauta zasu yi mata,kuma ba ruwanta takan shigo a lokacin da mazan nan suke ta sa a yi mata girki , har ta taɓa nuna ita ta fi son abincinsu fiye da na matan cike da gadara da kaskanci take masu magana koda aiki take son saka su, RAUDA kuwa aikin girkin gaba daya da ita ake yi, cikin mutunta junna da girmama junna tamkar ba itace matar MALEEK ba

Abubuwan da take buƙatar a yi mata ta nunawa chef din sannan ta ci gaba da aikin

Nan da nan suka gama girkin abincin kala daya mai sauki sannan ta haɗa drinks na lemun aya da kankana ta kilace komai ta kuma hada kayan tea din nasa da kula ta ce da chef" Ina zuwa Chef "

Chef ta dan dukar da kai ta ce" A fito lafiya Gimbiya"

Ita dai Rauda bata kuma cewa komai ba ta nufi dakinta tana jin ba zata iya kai abincin ba tare da ta dan watsa ba, rabonta da wanka fa yau tunda safe, gaba ɗaya ita bata san abinda yake faruwa ba, ta wuni gefen Mah ne dake fama da jikinta dan kaffafuwanta dake ciwo, sai Hajia dake kiran Mah din lokaci zuwa lokaci ta je ta dawo, ta tabata a kan wannan ihun da Amnah ta ringa yi ne, ko me yake damunta da zafi haka? gaba daya Amnah lamarinta a rikice yake sai adu'a

Wanka ta yi ta fito jikinta na digar ruwa ta dauki tufafinta riga da dogon wando na barci mararsa nauyi ta saka sai turare da ta shafa a duk wani lungu da sako na jikinta dan ko mai bata shafa ba, so take yi daga ta kai masa ta dawo ta samu ta kwonta ko zata samu yin barcin ranar da bata yi ba yau, sai a lokacin ta turawa Atu mesg cewar zasu yi magana gobe in sha Allah

A nutse ta dawo kicin din ta tararda chef ta haɗa mata komai a saman baban faranti mai ruwan zeba mai nauyi sai Khali yake, kayan kuwa sun jeru masha ALLAH harda tea din, ta rike da kyau tana yiwa chef din godiya, ita kuwa tana sake tambayar zata iya kuwa? har sai da ta ga ficewarta sannan ta sake kashe komai na kicin din ta kulle da ky din kicin din ta fice ta baya ta kulle ta koma bangarensu na masu aiki , domin dama dokar bangarensa da zarar sun gama aikace aikace suke tafiya nasu bangaren, sai manyan dake kula da wajen ne ke zuwa lokaci zuwa lokaci su saka turare su karra kakabe kakabe koda kuwa babu wanda ya fito, sai ko idan an yi kiransu dan wata bukatar kamar yadda RAUDA ta yi kiransu yanzu, dokokin YUSUF ne Wadinnan , Hajia sai da ta nuna hakan ba zai gyara matan gidan ba ya nuna shi haka yake so, yana son bangarensa ya zamo wajen sakewarsa ba wajen buyansa ba!

A nutse take knowking a kofar dakin bayan ta ajiye kayan, domin ba zata iya bugawar da kayan a hannayenta ba, idannuwanta kuwa babu abinda suke yi mata sai yaji yaji da muradin sake kallonsa da wannan salo nasa kafin su kwonta

A nutse ya bude kofar, da waya a kange a kunnensa yana amsawa ya sauke dubansa a kan fuskarta

Dauke nata duban ta yi ta duka ta dauki kayan abincin ta dan raba shi ta shige ta nufi wajen ajiyewa ta ajiye sannan ta juyo dan komawa idannuwanta suka sauka a kan ky din hannunsa ya nufi wajen wrdrb din nan ya kuma ajiye shi a inda ta yi ta dage ta kasa daukowa hankali kwonce yana waya kan harkar kasuwancinsa

A wajen da take tsaye ta kasa motsawa ya waigo ya kalla, da hannunsa ya mata nuni da wajen zama, wato wajen kujerun nan da ta ajiye abincin

Jiki ba karfi ta karasa wajen ta zauna tana dan murza hannayenta tana sauraron muryarsa, irin yadda yake magana da turanci tamkar a harshensa aka fara jiyowa, cike da classs da kwarewar harshe

Kasa kasa take dan satar kallon afaffuwansa dake saman farin tiles din nan farare kar kar , a saman yatsutsan gashi ne kwonce lufluf haka kuma daga sama kadan kafin inda jalabiyar jikinsa ta rufe tana iya gannin duhun gashin dake kwonce lufluf a jikin kaffafuwansa, sai ta cire kai ta lumshe idannuwanta ita kadai tana tunanin rayuwa

Ya jima yana wayar nan , har sai da ta gyara yannayin zamanta sannan ya katse ya kai wayar ya ajiye bayan ya kasheta domin baya son takura, sannan ya taho a nutse ya zauna saman kujerar nan zama irin na hamshakai wanda yake zamansa tun bai kai a kira shi namiji ba

"Ina zaki tafi?" Ya fada a hankali yana dubanta

Dagowa ta yi kan dole ta dan dube shi, a hankali ta ce" Dakina"

"Kina da wani dakin ne sama da nan?"

'To ko ya manta mace biyu gare shi ne?' Rauda ke ayanawa a zuciyarta, a fili kuwa ta ce" Tun jiya na cika kwana ukun da ake yi fa"

Shiru ne ya wanzu a wajen, ita tana jiran jin umarninsa dan ta kula karfinta babu abinda zai kwatar mata, shi kuwa yana tunanin lalle y'ar gidan Mah tana tare da neman masifa walahi, in ba wannan ba so take yi sai ta bata masa yannayi ne? ok kwana ukun da ake yiwa wace ta taɓa aure take son fada masa ko?, shi yasa ya yi shiru har sai da ya cire abin a ransa sannan ya ce" Srv me"

Ajiyar zuciya ta sauke jin amon muryarsa dan har ta cire tsamani

A nutse ta fara zuba masa abincin ta dora a karamin teburin ta matsa gabansa, sannan ta dauki sauran kayan bukatan duka ta kai gaban nasa ta ajiye tana kokarin komawa wajenta ta zubawa hannayensa ido da ya saka ya zaunar da ita daga da shi sannan ya saka cokalin a nutse ya fara cin abincin hannunsa daya riƙe da nata yana shaƙar kanshin turaran da ta yi anfani da shi, har ya gama ya sha ruwa kadan sannan ya sha tea din da guminsa sosai hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya yana jin nutsuwa na sauka a cikin jikinsa, dan rabonsa da abincin kirki tun jiya, yau din basu rigaya sun karya ba ya fitar nan sai dawowar nan da ya yi

Dubansa ya maido kan RAUDA dake jira, a hankali ya ce" Cire hijabin mana ki sha iska"

RAUDA ta yi raurau tana kallonsa ta ce" Ni da zan tafi yayanmu?"

Murmushi ya yi ya mike tsaye , hannunta dake cikin nasa na cikin ya mikar da ita a hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta, kasa kasa ya ce" Da na yi part part a nan, saboda kar y'ayana su ga ina kwana a dakin ki,........ama in dai ina nan kuma kina gefena cen ne makwoncin ki....... Bismillah"

Jikinta karra mutuwa ya yi, a hankali ta dago dubanta ta sauke kan sagen fuskarsa da kanshin da jikinsa ke fitarwa, tana kallon nasa ya raba jikinsa da nata a hankali ya nufi bayi da nufin yin bruch

Idannuwa ta rintse tana jin tamkar ba ita ba, 'Ya Allah, ina son bawan nan naka, ka sasauta min yadda nake jinsa a raina dan bana so hakan ya zamo min ila'
Shine abinda ta yi ta ayanawa a ranta har ta ji motsin fitowa daga bayin, a hankali ta shiga tatare kayan abincin ta hade waje kuda a ranta tana ayana' Allah ya sa ba abinda zai ɓaci kafin safe'

A nutse ta je ta zauna wajen kujerar dake daf da sif tana kokarin kin hada ido da shi domin ya gama ya je bakin gadon ya zauna ita yake kallo, a sanyaye ta ce" Yayanmu, dangane da maganar kwanan ne nace wai tun jiya ne na gama"

"RAUDA zo mana, ko na zo ne?" Ya fada yana katse furucinta
Chapter 114 · 0% Book details