← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 117

Sashe 34

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aminu mai adaidaita ya ja numfashi ya ce" Walahi Hajia RAUDA har yanzu dai bamu samu labarinsa ba, ama baki ga yadda sojawa da polisawa ke kai kawo a anguwar ba, ai ki godewa Allah , Allah ya ga maraicinki ya bayyana maki mutanen nan a wannan lokacin, gashi yanzu ance wanda ya amshi abin a hannunsan nan kin ga mahaifin sarki ne, na tabata za'a ji abinda Malan Umar ke ciki bi izinillah "

RAUDA ta sake sada kanta, kasa kasa take maganar sosai, ama bai hanna Salima jin abinda take fada ba, hakan ya sa ta dan kalleta sai kuma ta cire dubanta dan ba zata so ta ga kamar ta takurata ba

A hankali RAUDA ta ce" Kana ji Aminu, dan Allah ka je gidan inna, ka ce da ita kar ta bari Abdul ya ji wannan abin, kuma kar a kai shi gidan nan, ka ga yanzun bana nan, idan aka kai shi na tabata Mama zata amshi shi ne ta galaza masa, ba zai iya jurewa ba, dan Allah ka min kokarin nan ka ji?"

Aminu ya tabatar mata zai je da an jima ya sanarwa inna, ta yi ta godiya har sai da ya ji kansa na dagawa dan shi abin samakal alkur'an, sannan suka yi salama

Tana mayar da bayanta jikin kujerar nan a hankali ta lumshe idannuwanta hadi da sauke numfashi a boye tana ji kirjinta na yi mata zafi, wani kiran ya sake shigowa

A raunane ta kalli numbar
Sunnan wanda ta gani ya sakata dan dagawa kadan ta daga ta kara cen ciki ta yi salama

A tausashe ya ce" tare da ke wifey, kin san wani abu? Yau na zo layin baban masalaci na nan maroco na ga wata yarinya marainiya, wifey ina so mu dauketa mu raineta, dan Allah ki ce min kina so kema? Idan kin amince na dauketa na fara gyara takardun ta, a saka mata sunnanki da nawa, yarinyar shekarunta duka duka daya da wata uku, Please ce min yeah kin amince "

Har ga Allah bata wani fahimtar yarensa, shiru ta yi masa har ya dasa aya, da kansa ya gane kamar bata tare da maganar da yake yi, shi kuwa ya yi kiranta da tarin zakuwa ne , dan Allah ya saka masa son y'aya, ama tun a yanzu an tabatar masa bashi da kwon baiwa wata macen bale ta haifo, shekarunsa Kusan hamsin yanzun, dan yan watanni suka rage ya cika hamsin, Allah ya jarabeshi da son RAUDA, shi Balarabe ne, ya san ba wai kyau ne ko fari ya ja shi ba, ya sani ne Allah ne ya dasa masa abin a zuciyarsa kuma yana fatan ta zamo mata a gare shi, shine damuwar ke damunsa idan ya tuna rashin haihuwa fa baban abu ne a duniyar mata, hakan na iya haɗasa masu rashin jituwa, shi din kansa ya san yana son y'aya, sai gashi yau ya ga yarinyar nan, an tabatar masa wai ana shirin mikata ne gidan marayu, dan kakarta dake rikonta ta rasu ta barta ita daya, mahaifiyarta wajen haihuwarta ta rasu, mahaifinta kuwa yana raye ama babu ruwansa da ita, jaririya ce fa, ama har ta zama kaya a hannun mutane, masu taimakon ta suke rike da ita ne suke shirin kaita yafe yana so zai je a kaita sai a mishi takardu ya zo da ita , dan ya shirya tsaf idan ya shigo Nijar auren Rauda shine abinda zai fara yi kafin komai a gabanan

A tausashe sosai ya shiga magana bayan ya kashe tv din dake dan bayani da harshen larabci, ya ce" Hey, Are You crying?"

RAUDA ta sake lumshe idannuwanta, a hankali hawayenta suka shiga bin gefe da gefen idannuwanta, haka kuma muryarta ta kasa fita, sai shasheka dake fita kasa kasa

Gabansa ne ya fadi, da sauri ya kashe ya shiga yi mata vidio call

Da kyar ta iya dagawa ta zuba masa matatun idannuwanta tana kallonsa kasa kasa

A hankali ya ce" Kuka kike yi? Me ya same ki? Kina ina ne?, me ya faru? Kin san inada matsalar zuciya ko? Kar ki saka na samu attack mana , tell me"

Da kyar ta bude bakinta, muryarta mai zaki da sanyi ta shiga fadin" Uncle dina, ba'a san inda yake ba, kana tune shine uwata, shine ubana, shine komai nawa........, an...an...an kawo kayansa da jini a jiki, bamu san yana raye ko ya mutu ba, ban san yaya zan yi........."
Sai kawai ta fashe da kuka tana ajiye wayar ta dora kanta saman cinyoyinta tana yi sosai

Ya Salam, ya Salam yake ta maimaitawa, kafin a hankali ya ce" Hey, RAUDA? Tashi ki ji"

Da kyar ta dago ta dauki wayar tana kallonsa

A tausashe ya ce" Ki daina kukan haka, in dai ina raye ba zaki yi kuka ba RAUDA, zan taho nan da sati Daya in sha Allah , na daina kaiwa wata biyun kin ji? Zan zo, ko a ina yake, ko nawa ake so a bada a sake shi zamu bada, mu yi ta addu'a in sha Allah, yana raye ok??????"

Kai kawai take gyada masa kamar wata yarinya karama, shi kuwa sai rarashinta yake yi, har ta daina kukan sannan ya mata salama dan ba damar jan firar duba da yannayinta

Gaba daya ta manta ba ita daya take falon nan ba, ita sanyin wajenma ya fara shiga kasusuwanta, a hankali ta karkata dan share hawayenta da hijabin jikinta ta ga fari kar din hannu na miko mata abin gogewa a hankali Salima ta ce" INNALAHA MA'ASABIRIN RAUDA"

RAUDA ta dago jajayen idannuwanta ta sauke saman fuskar Salima, ta kasa amsar abin goge hawayen, haka kuma ta kasa daina kallonta

Salima ta zauna daf da ita ta mika hannu a hankali zata share mata hawayen, RAUDA ta rintse idannuwanta, a birkice kuka ya kwace mata, a rikice ta......

🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹
Azl 20
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

A rikice Rauda ta mike da nufin tafia, da sauri Salima ta kamo hannunta tana mikewar itama tana kallonta ta ce" ki yi hakuri, kar ki ga ina takuraki, kuma ban tsaya dan na ji firarki ba, na tsaya ne dan bakuwar Mah kike , ita kuma tana wajen Bah, bana so na barki ke kadai kuma sai na ji wannan, RAUDA na ji sunnanki a wajen wannan da ya yi kiranki, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ban san girman dacin abinda kike ji ba, dan ban san dacin maraici ba, nakan kamanta a zuciyata ne, sai na ji dacin na nema ya zauta Ni, sai dai alhamdulilah kasantuwarmu musulmai Allah na saka mana hakuri da dangana komai girman rashin da zamu yi a rayuwa, ki yi hakuri, na saurari firarki kaf, in sha Allah uncle dinki ba zai rasu ba, ko a ina yake za'a samo shi, in sha Allah in dai kika samu gannin yayanmu ko? Walahi yana iya fitar maki da shi a kwana kusa, dan masu kawo rashin kirkin nan babu mai gigin kawo masa, ki yi ta addu'a, nima zan taya ki, ama ki daina kukan kin ji? Kowani tsanani yana tare da sauki Rauda, ki zauna ki ci abincin nan dan yiwa kanki horon yinwa ba zai anfaneki da komai ba sai azabtar da kanki da zaki yi, domin idan da yinwa ko ibada mutun zai yita ne wani iri, kin ji?"
A tausashe sosai take maganar, kuma ta tarewa Raudar hanya, a dole sai da Rauda ta saurareta har karshe sannan ta kasa yi mata tsayaya, dan ko ba komai Salima mai kaunar ta ce, mai son ta ga ta saku ta ware ta daina damuwa ce, dan haka ta dauki nasiharta da mahimmanci sosai har ta koma ta zauna ta yi hakuri suka ci gaba da zama da Salimar, danma ita Salimar takan je jifa jifa ta ga jikin iyayensu ta dawo, sai da aka kira sallar magarib ne suka shige ciki har dakin Salimar suka daura alwallah suka shiga gabatar da Sallah
Chapter 34 · 0% Book details