Sashe 100
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajia ya zuba masa ido, gaba daya gani take yi kamar baya ganewa, dan haka ta dan matso sosai kusa da kujerarsa tana kallonsa ta ce" Baka gane ba fa, ita Amnah itace y'ar wadinncen mutanen , ita kuma baby itace wace aka aura maka jiyan nan wannan y'ar karamar da bata cewa komai, yarinyar nan fa ya wajen Mamanka fa nake nufi, itace ai RAUDA ko?"
Tsakani da Allah sai da ya ji dariya ya kama masa zuciya, ya girgiza kai yana kallon tsohuwar nan da wani tsukaken bakinta irin na tsofi, to shi in ba garaje ba waye zai ce masa wance ce Rauda? ai sai dai ya gaya maka wace ita da sauransu
yana kallon ya ya ce"
😍😍😍😍😍😍😍
yana kallon Hajia ya ce" Ita dai jikar taki ce ta zane dayar"
Hajia ya yi shiru tana nazari, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ya juya ta je bakin falon inda Jakadiya ke tsugune tana jiran abinda za'a fadawa dogari da kuma wani sakon idan akoy
A nutse hajia ya ce" Ki ce a basu damar su shigo, sannan ki isar da sakon ina son gimbiya Amnah da gimbiya RAUDA su halarci falona"
Kai a kasa ta amsa da" An gama kakar saraki" Sannan ta mike ta wuce
Jiki sanyi Kalau Hajia ta koma ta zauna tana kallonsa irin yadda ya gyara zamansa yana cin tufa hankali kwonce, ta zatama zai yi tafiyarsa ne, sai ta ga ya zauna,, ba zata so a ringa irin shirmen nan a gabansa ba, dan kuwa ba zata so ya yanke wani hukuncin abinda ya shafi iyalinsa cikin fushi ba
Shi kuwa zaunen da ya yi, ba komai yake son ganni ba sai wayewar gari da idon da zata kalli mutane ita wancen da ake kira marainiyar Allah, yakan yi murmushi ya girgiza kai, duk irin ayyukan dake gabansa baya jin zai iya zuwa ya yi idan bai ga abinda yake son gani ba, bashi da niyar furta masu A a zaman nan, ama kuma ba za'a hannawa ido kalaci ba
Su suka fara shigowa bayan an bada damar su shigo baban falon Hajia
Abin mamaki yau dinma shi da abokinsa din nan da kuma matarsa, wato mahaifiyar Amnah
Tunda suka shigo Dogari ya nuna masu wajen zama saman baban cafet din dake tsakanin cafet din da ƙafafuwan YUSUF ke sama da kuma kujerar da Hajia ke sam,, suka zauna idannuwansu suka sauka a kan YUSUF kusan kowane ya karra kama kansa harma suka so manta abinda ya kawo su
Daga kofar shigowa dogari ya koma ya tsaya bayan sun gaishe da Yusuf da Hajia Dogari ya yi aikinsa ya nuna sun amsa, Bama kamar Yusuf da ya saka Tissu ya goge bakinsa sannan ya dan zuba masu ido kadan kafin ya dauke kansa yana murmushi, gasu dai cikin shiga mai kyau, sai dai a cikinsu kowane da abinda.ke.tafe da rayuwarsa mai hatsarin gaske wanda idan bawa ya ji sai ya firgita
Hajia kam abokin nan na Mahaifin Amnah ta zubawa ido, da wani kallon da ya saka shi sada kansa yana jin kirjinsa na sake dokawa, domin dama tunda suka shigo ya ga YUSUF ya ji hankalinsa na neman tashi
Kai Hajia ta dauke a zuciyarta tana cikin mamaki mai tsananin gaske na kamanin da wannan bawan Allah yake yi da Amnah, kamanin har sun bace sosai, sai ta sakawa ranta ta yiwu da akace abokinsa ne ko d'an uwansa ne na jinni kuma abota take da karfi a tsakaninsu?........., ita dai ta ture tana duban su da kula ta ce" Shin me yake faruwa haka ne? ance jiya wajen karfe biyu kun zo, gashi yau tun dazu kuke kofa, Allah ya sa lafiya?"
Kan mahaifin Amnah a kasa, yana jin abinda Hajiar ke fada ama tamkar wanda ya afka wata duniyar tunani daban, har sai da abokin ya sake tabo shi ya ce" ana magana baka ce komai ba Elhaji?"
Da wata irin murya, wace kana ji sai ka kalli mai ita duba da Muryar sama sama ce kamar baya cikin hayacinsa ya yi maganar , irin sama sama din nan ya ce" Eh, haka ne, dole zan zo da duk wani wanda ya isa da yata, dan ba zai yiwu a kashe min ita ba kamar yadda Hajia tace ko ba haka ba hajia?" Ya karashe yana kallon mahaifiyar Amnah da hannayensa bibiyu a hade kamar wanda ke rokonta wani abin, ita kuwa ta sake sada kanta yadda ka san irin manyan salihan matan nan da ko surutu da karfi basu iya ba bale ace zasu aikata mugun abu
Shigowar dogari da sauri yana fadin" Kai, ka sasauta muryarka a nan wajen ko ka fito mu iya da kai talaka!" Ya sa YUSUF dago dubansa ya masa alamun ya fita da hannayensa, da sauri ya juya ya fita din yana jin tamkar ya warto mahaifin Amnah ya koyo masa hankali, dan ba'a yi wanda zai yiwa MALEEK magana haka a gabansu ba tare da sun datse harshensa ba walahi! ya godewa Allah ba Taj bane a wajen dan kuwa shi bashi yake bi kuma sai an biya shi!
Sake gyara zamansa ya yi a lokacin da Mah ta shigo tana kallon iyayen Amnah da mamaki ta karasa ta duka ta gaisar da Hajia, sai dai Hajia bata samu damar amsa gaisuwar ba saboda ranta ya kai kololuwar ɓaci ta budi baki da fada ta fara fadin" Ohk, shine kuka kwaso jiki kai da d'an uwanka da matarka kuka zo ku shiga fadan tsakanin abokan zaman da fadan bai yi tsauri ba , dan ita Amnah itace mai gata ita kuwa RAUDA bata da kowa ko? To ai RAUDA ita keda gata, wanda bana tunanin Y'ARKU tana da shi, domin ga Mamanta nan, Ni kuwa nice kakarta, !"
Gira ya dan dage yana kallon Hajia kasa kasa ya furta" Ko?, to wa yace maki d'an uwansa ne? ba hadinsu fa"
kallonsa Hajia ta yi, domin idan ba ita dake daf da shi ba babu wanda zai iya jiyo abinda YUSUF yake fadi, da sauri ta kalli bakon , ta sake kallon YUSUF daidai lokacin da AMNAH ta fara shigowa da abaya a jikinta fara, tana gannin iyayenta ta je da gudu ta fada jikin mamanta tana fashewa da kuka, ita kuwa Hajia abinda ya fito daga bakinta tana kallon abokin mahaifin Amnah ta ce" A'a fa, d'an uwansa ne mana, bawan Allah kai ba d'an uwan mahaifin Amnah bane? haba wannan kama ai sai jinni, sai kace a tatsuniya ai ba za'a ce tsabar abotaka bace ta sa y'ar nan ke kama da kai ko?"
Da karfi mahaifiyar Amnah dake sune sune tana ba Amnah hakuri kasa kasa ta dago ta dubi Hajia, kuma wani ikon Allah a tare suka dubi Hajiar sannan suka kalli junna, da sauri ta budi baki tana fadin" Ke Amnah yi shiru mana, ya isa haka, ke ashe fada be kawai kuka yi ke da abokiyar zamanki, wannan ai ba wayo bane, ina mijinki yake da zaki wani kiraye mu? haba dan Allah Ni bana son ka zama mutun marar sirri, duba ki ga mahaifinki ko ido bai rintsa ba tunda kika kiraye shi kina kuka, na yi na yi ya yi hakuri ko menene ke da kike gaban magabata an yiwa abin tsawa kika kiya, haba Ni na ji kunya walahi kin sa mun zo gaban iyayenki da wannan maganar, Hajia dan Allah a yi hakuri a yafewa yarinta, kin san ita Amnah bata iya fada ba , sam bata san rikici ba, kunu huce in shaka sunnan Amnah fa, tsorota ta yi da y'ar uwar Tata shi yasa ta rikice, ama gabanan ai ko wani abin ne ga mijinsu sai ya yi masu shara'a ya sasanta su, in ba iya shege ba RAUDA kanwarta ce ai ba wani maganar kishi, Elhaji mu je haba ka huta bawan Allah gajiya ta ishe shi ita ta zo tana wani damun mutane, ku mu je" Ta mike tana mintsinin cinyar Amnah, wace ta dago tana kallonta da mamaki a bude fuskarta da kyau dan ta ga irin yadda jinni ya kwonta, har bata ga shigowar RAUDA da salamarta ba dan tsananin mamaki tana gannin yadda mahaifiyarta ke mata alamun su yi waya da irin yadda ta kada mahaifinta suka tafi komai ba'a yi ba, komai ba'a yiwa wancen mahaukaciyar sauvage din ba, duk irin abinda ta yi mata?
a rikice ta juyo bayan sun wuce , hakan ya sa dan kwalin abayarta faduwa daga kanta ya sauke daga rufewar da ta yiwa fuskarta
Ido Hajia ta zarro tana kallon fuskarta ta ce" Subahannalahi ke, meye wannan a fuskar ki kamar wace mota ta bi ta kai? kaikaikai rufe rufe wannan tsaba tsaba wajen kuncinki hala wani tautau ya zuba maki ruwansa a kanki? subahanallah...."
Mah ma dake murmushin inda RAUDA ta je ya zauna kanta a kasa tunda ta shigo da wani zumbulelen hijab tamkar zai makata a kas dan ya yi mata yawa sosai kuma kan nan a kasa ta ki dagowa ta kalli kowa ta dubi Amnah itama tana fadin" Subahanallah me ya samu fuskarki haka? ko wani abu kika shafa ya kumbura maki fuska?"
Amnah ta girgiza kai tana matse kwallah ta dubi RAUDA tana jin da ace za'a bata bindiga walahi tana iya harbe RAUDA har lahira, sai dai ba laifi wasan yanzu aka fara shi dan walahi sai ta rama, ta fashe da kuka tana fadin" Walahi babu abinda na shafa, jiya ne kawai na fito baban falo dan na yiwa honey sannu da zuwa wannan ta sandeni ta duka min karfe a wuyana ta shiga dukana da abubuwa, ba iya fuskata ba harda jikina du birdi ne, birdi ne wannan din ai na abin duka"