← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 117

Sashe 37

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Sunna cikin hada haɗar nan Mah ta fito dauke da kaskon turaren wutar da ta fito da shi daga ɓangaren YUSUF,

Itace ta ringa gaishe da matan Bah da girmamawa da kula, su kuwa sunna amsata kadaran kadahan harda wace ta shiga jiyan ta saki tsaki ta fito falon itama, kana gannin yannayinta ka san kamar wace aka yiwa dole, ga abin karin ruwa a hannunta

Mah ta ajiye kaskon dake dauke da tsumamen turaran wuta na Dolars a lungun kujeru ta zagayo ta zauna saman kujerar nan tana dan sauke numfashi, dan ta ci aiki harda na mamaki, domin tunda ta yi sallah ta kamawa YUSUF ya kimtsa mahaifinsa tas, ya dauke shi ya kai shi saman doguwar kujera suka cenzawa gadon dakin zama suka yi shinfida mai kyau, ta yi shara ta wanke bayi tas ta saka turare ko'ina suka kimtsa hatta labulaye sai da suka cenza, sannan ya maida mahaifinsa za kwontar wanda ke numfashi ama jikinsa da gumi, kuma yannayin kwonciyar da ake masa irin ta masu ciwon zuciya ne sannan ya tafi nasa dakin dan Hajia sai kira take yi tace kar ya amshi bakuncin kowa yau kuma kar ta saki ta yarda wani ya dafa masa abinci ya bashi ya ci ciki harda mutanen cikin gidan da sauransu sannan ta sanar Sarkin rawani zai zo da tufafinsa a masa rawani ita kuma zata kawo abincinsa, a haka dai suka yi salama da Hajiar Mah ta rarasheshi ya je ya yi kwonciyarsa domin a wannan lokacin da ake ta kai kawo din nan shi barcima yake yi a dakinsa, gashi har karfe tara ce zata yi

Da kula sosai Mah ta ce" Ku yi hakuri jiya na kwana dakin cen ban tsaya mun daidaita ba, na yi ta jira ko wata zata shigo har barci ya daukeni, yaya kuka tsara jinyar tasa ne Hajia?"

Hajia ta dago dubanta tana kallon Mah, ita abinda ya fi bata mamaki da ita kamar bata taɓa haihuwa ba caras da ita, ga shegen gayu, koda yake abin nata koda ba wanka ta dauka ba sutura na yi mata kyau ne wannan komai koshenka ba zaka kushe wannan ba

Kanta ta dauke ta ce" Ai kawai ki yi jinyar , idan kuwa da Maman su Khalifa zaku raba ba damuwa dan Ni ba lafiyar gareni ba nima"

Maman Khalifa ta juyo tana yiwa Hajia kallon lallema, ta dauke kai tana tabe baki dan walahi ita ba zata furta masu koda a ba a wannan shirmen, jinyarsa? A'a ita matar so ta je ta yi ama ba dai su ba!

Gannin haka ya sa Mah yin dan murmushi ta mike ta nufi kicin bata kuma furta masu komai ba, ba zasu gane bane, a da ta dauki wulakanci ama banda yanzu, su da kansu sun sani banda yanzu, ba wai dan YUSUF ya hau kujerar nan ba, a'a, tun kafin ya hau ta yi watsi da wulakancin su ta fuskanci rayuwarta tunda ta gane ba zaman mutunci ake yi da ita ba ta dangana da su!

Su Dukansu sun yi mamakin yadda bata basu hakurin a raba jinyar Honorable ba, sai kuma suka watsar dan sun san dama abinda take so kennan, maman Khalifa ce kawai ta kudiri a ranta ba zata bar mata mijin ba, zata hannata zaman lafiya da kai kawo tana watsa masu hannu da Bara masu kanshi kamar ita kadai ce matar BELLO ba!

Mah na nufar wajen Diner ta ja ta tsaya da mamakin yan matan dake tsaye kowace ta sha kwaliya su ukun nan tamkar wa'inda suka zo gidan biki bayan gidan rasuwa suka zo

Amsa gaisuwar da suke rige rigen yi mata ta yi a jimulce ta dauke dubanta ta ɗora saman RAUDA a tausashe ta ce" To nan babyn Mah"

RAUDA kunya ta ji ta kamata, sai kuma wani abu da ya sakata daga kafafuwanta ta karasa daf da Mah ta nemi dukawa dan gaisar da ita, wani abu mai kama da shauki da jin wani iri kamar idan wani mai daraja a duniyar ka ya nuna maka kulawar nan

A nutse Mah ta tareta ta dagota tana murmushin tsokanar da Salima ke yiwa RAUDA din, dan Salimar cewa ta yi" Iyeah, kin ga mamanki kin saku? Mah y'ar nan taki bata fira sai da ke kadai ama ko?"

Mah ta sakar masu murmushi zata basu amsa kunnayensu gaba daya suka ji ana salama da rakadi na sanarwar Hajia ke tafe

Har ga Allah sai da gaban Mah ya fadi, da sauri ta ware mayafin RAUDA da ta dan rankaya shi cen saman kanta ta yada mata shi sosai a saman kanta har ya rufe gashin kan nata sosai sannan ta masu alamar tana zuwa

Ta kamo hanya zata tafi falon ta ja ta tsaya saboda gannin kujerar Hajia na nufowa wajen table din tana bin kowa da kallo, bayanta kuwa tamkar jela matan Bah ne kowace yannayinta na nuni da kamewa da kula dan kar su aikata wani laifin

Ja ta yi ta tsaya ta shiga bin kowa da kallo, a lokacin ne Salima ta kamo hannun RAUDA suka fito sosai suka duka sunna gaishe da Hajia wace ke bin kowa da kallo ciki harda RAUDA

Hajia bata amsa ba, tana kallon kowa ne daya bayan daya sannan ta budi baki ta ce" Wadinnan fa? Ban sansu ba, da wannan"

Hajia mahaifiyar Salima ce ta ce" Bakin Andiya ne "

"Andiya?" Hajia baba ta maimaita tana kallonta da mamaki, ba komai ya sa ta jin mamaki ba sai gannin Hajia na fadin sunnan uwar Malik haka kai tsayen nan, ba maganar kishiyarta ko abokiyar gabarta, koda da cikinta ta haife ta an zo wajen da zata dan daidaita wasu abubuwan, ita bata ce su shirya ko su yiwa mahaifiyar YUSUF biyayya ba, No, abinda take so daya ne jal, a kiyaye girman sarautar kasarta, dan a kan wannan tana iya batawa da kowa a duniyar nan!

Mah ce ta budi baki a nutse ta ce" Eh bakina ne, su ukun nan ya'yan yan uwana ne, ita kuma wannan y'ata ce da nake riko"

Y'ata ce da nake riko ya saka daga Hajia baba har sauran zubawa Mah ido, ciki harda Rauda wace ta sake jin wani iri a kan Mah har ta ji wani abu ya tsirga mata zuciya mai kama da rauni da jin karfi irin na soyaya na son sukar maka zuciya

Abinda ke bakin Hajia ta hadiye bata yi ba a gaban mutanen, sai dai dayan bata hadiye ba, da kula sosai da kamewa ta ce" Ba damuwa, ama Wadinnan su ringa rufe jikinsu sosai, kuma su kiyaye kwaramniya idan Malik na nan, kafin a ware bangarensa daga naku!"

Tana gama fada ta juyar da kujerar tana dannata ta ci gaba da fadin" A irin wannan lokacin ko me kuke yi, daga ku har yayanku ya kamata Ku bar shi, ku yi jiran fitowarsa, idan ya fito gaisar da shi kadai zaku yi dan ba lokacin ya hadu da wani abin bacin rai daga gare ku bane, in ya tafi sai ku yi kai kawon ku kafin a gama ware masa nasa bangaren?"

Tana tafe a hankali ne da keken sunna biye da ita , Hajia na amsawa da in sha Allah, Mah ta yi shiru, da aunty amarya

Sai da suka nufo sashensa shi da mahaifinsa Hajia baba ta yi shiru ta dakata ta masu alamun a bude mata wajen Bah

Bude mata Hajia karama ta yi suka shiga ta karasa wajen da Bah ke kwonce

Ido ta zuba masa zuciyarta na neman tsinkewa
Da kyar ta danne abinda yake zuciyarta a kan danta ta yi masa addu'a sosai ta juyo da keken suka fito, dan ba zata tambayesu jikinsa ba domin dukkan abinda yake ciki ta sani a wajen likitansa da Mah

Da suka karaso kofar dakin YUSUF dakatawa ta yi ta dubi Mah ta ce" Ki shiga ki tashe shi, dan na san yana barci, dan Allah ki masa a hankali kar ki bata masa rai, ki rarashe shi ya yarda ya yi wanka sai mu shigo da Sarkin nadi a shirya shi"

Mah ta gyada kai a ranta tana ayana' Hajia da YUSUF kennan"

Har zata shiga Hajia ta sake jaddada mata ta bi shi a hankali, hakan ya sake riƙe wuyan matan Bah
Cen dama sun san soyayar da Hajia ke yiwa YUSUF daban ce da sauran duk wani jikanta, kuma sun sani sarai duk zafin Hajia tana shayin YUSUF , gashi yanzu ya zo wajen da duk iya shegen da ya shuka ba za'a zage shi ba ko a daga masa murya uwa uba a masa kallon banza? Ya Allah su kam haka zasu zo a banza su koma a banza kennan? Sunna ji sunna kallo yau matar da Hajia ta fi taana cikin ahali ce take yiwa magana da sanyin murya? Lalle akoy aiki ja gabansu

Mah na shiga da salama ta same shi kwonce saman gadonsa ya luluba da bargo , ac kuwa ya kure sanyinsa sai barci yake yi kamar ba shi aiki ke gabansa ba

Dakatawa ta yi daga nesa ta maimaita salamarta kamar sau biyu , ya yi shiru da nanauyan sauke numfashi zuwa saukakake alamun ya farka ama ya ki tashi

Mah ta ce" Ai sai ka tashi malam, kai YUSUF barci ka samu yi kennan? To tashi kakarka na kofa tsaye kuma gaba dayanmu ta tiso mu ka san ba zamu zauna ba sai ta ga ka fito ko?"
Chapter 37 · 0% Book details