← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 117

Sashe 70

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

RAUDA ta ja tsaki , zuciyarta na tafasa tana jin kai ita fa sarai tana iya murje komaima ta yi kamar bata taɓa Sanni ba a kan shirme, itama a dan zazafen ta ce" Sarki? sarki kika ce? ohk...., ya yi, ya je ya yiwa wasu sarautar ba Ni ba, ke kina so , so kike ki ce min, saboda tsabar balaki da wulakantar da kai, Ni mace nice zan hankalta da ana so na har na lalata auren wanda ke son nawa fisabililahi na zabe shi? Allah ya kiyaye, walahi ba zan taba yarda da wannan abin ba! ke bari ki ji, koda abinda kike tunanin haka ne wato yana so na, na ƙaryata, dan kuwa so din in har da gaske ya kama mutun shi yake salamawa ya sama ma kansa mafita ba wai Ni a yi tunanin Ni ce zan samawa kaina ba, i love Abdallah, Ni na san da ina son ABDALLAH, kuma zan iya rayuwar aure da shi har karshen rayuwata, ki Kadara wannan abin da kika karanta shirme ne kawai, kin gama bari ki gani....na goge, haka kuma na goge shi daga rayuwata, wace ya aura kuwa ya je ya zauna da abinsa shi ya gano!"
Daga nan ta yarda wayar a nan ta fice ta nufi bayin Mah dake cikin dakinta na barci ta bude ta shiga da sauri
tana rufe bayin ta saka hannayenta bibiyu ta rike kanta, bugawar da kirjinta ke yi na neman fin karfin ta
a hankali ta silale jikin kofar ta sake saka kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da wani irin kuka mai nishin nan, a ranta tana ta astagafari da ambaton sunnan Allah, ayanawa take yi' Allah kai ne Allah, Allah ka cire min abinda ke raina ya zamo kamar bai taba wanzuwa ba a ruhuni na, ya Ubangijin samai da kasai ka saka min soyayar mijina fiye da ta kowa a zuciyata ka bani ikon yi masa biyayya da dukkan lokacina a kansa, ya Allah ka ji kaina idan har ba zan iya manta abinda ke raina ba ka amshi raina na zo gareka tun kafin na kona kaina, ina tawasali da sunnayenka tsarkaka ka tsare Ni da fadawa halaka a kan makauniyar soyaya.....'

A falo kuwa, jiki tamkar an zarre mata laka ta zauna kasa tana sauke ajiyar zuciya, a bayane, sai dai muryarta kasa kasa sosai ta ce" RAUDANA, ta wani fannin zan fi farin cikin ace kin watsar din, domin matar da ake maimaita matarsa ce ba zan taba so wani abu ya hadaki da ita ba a rayuwa, dan kuwa kudin iyayenta sun bata dama sosai na daukan duniya a matabata, na ga status din matar ƴaƴanta tana dora yau ne daurin aurenta, buri ya cika yau ta auri sarki? eh lalle abubuwa zasu karu har su wuce da, sam halayarku ba iri daya bace, ita ko gaisawa bata yi da talaka, bata hulda da mace mai muni ko baka, domin ko mai aikinta fara ce kyakkyawa, yarinyar nan ban san a inda ya ganota ba, ama idan ana kiran mutun dan Adam da AZAL tabas itace, tana da raini fiye da tunanin mutun, kuma idan tana waje ta tsani ace wani dan Adam ya fita a wajen, sai ta yi yadda ta yi ya zamo itace sama da uban kowa....., uhum Ni kam ina tausaya masa dan ko Tata mahaifiyar ita ke yi mata biyayya bale uwar miji, da wahala ta girmama mahaifiyarsa....." ( kai, 🤔, Mah,? lalle da an yi kulli kulin kubura da yar mutane muna gefe muna shan lipton)

....................................................

"HEY" SHAHEED ya fada a karro na uku kennan, tunda suka juyo suka dawo falonsa suka zauna , yana zaune ne ama tamkar gunki, ga fira a bakin SHAHEED din a yau, ama kuma abokin yin kamar baya cikin duniyar masu rai

"Lafiyarka kuwa?" SHAHEED ya fada , fuskarsa na nuna alamun damuwa

Rawanin dake kansa ya shiga kuncewa, har ya warware shi ya sauke hular dake ciki hakan ya ba gashinsa damar bayana , ya cire agogon dake hannunsa hadi da kai hannayensa wajen goshinsa ya ringa murzawa, kirjinsa na yi masa wani irin zafi, kwakwaluwarsa na tafasa, hankalinsa gaba daya tamkar ba nasa ba, duniyar kaf ta yi masa kunci fiye da tunanin bawa

A hankali ya sake kallon SHAHEED, muryarsa cen ciki ya furta" Ta yarda ta aure shi, SHAHEED ta yarda ta aure shi.........."
Daga haka ya dauko wayarsa, kirar samsung wace ake ninkata ya bude sai ga hoton kunshi a hannun mace ya haska saman screen din, a hankali ya shiga wajen msg ya bude ya mikawa SHAHEED sannan ya mike tsaye ya saka hannayensa cikin aljihun wandonsa ya ringa kai kawo yana ta faman kiran sunnan Allah, dan ya sani shi kadai ya isa ya sanyayar masa da zuciya a irin halin da yake cikin nan

SHAHEED ya karanta ya kai sau goma, du idan ya karanta kuma sai ya dago ya dubi YUSUF, sai ya sake karantarwar

"ya Salam, Dama a gidan nan take? dama a kusa da kai take?" SHAHEED ya tambaya, hakan ya sa YUSUF dakatawa ya dago idannuwansa ya zuba masa, lebensa kuwa ya yi Jajajir ya tasa tsabar yadda yake dantse shi

"Na san me zaka ce......, ya yaya ina ji ina gani ko?" YUSUF ya fada yana kallonsa, dan ya sani sarai SHAHEED a kan magana irin wannan kulun fada masa yake yi ya daina kiran soyaya Azal, ya gwada ya gani babu abinda ya kai soyaya dadi a gidan duniya, ama sai ya yi murmushi yace baya cikin wannan gangancin

"Koda ta tare sai ya saketa, ina zuwa!" SHAHEED ya fada a zafafe ya mike da nufin fita

YUSUF ya yi gaggawar riko alkyabarsa ya dawo da shi yana dubansa a tausashe ya ce" A'a, Please"

SHAHEED rai bace yace" Ka san kuwa a wani irin hali kake kokarin saka kanka? ka san irin girman rikicin da kake kokarin nuna zaka iya yi? waye kake son birgewa da nuna wannan halin? mace ce fa, ina mai tabbatar maka koda mutuwa zata yi tana iya rike damuwarta a kanka, ya Salam,, a kan me zaka bari ta aure shi?"

"Dan tana son shi!" YUSUF ya fada da muryarsa da take nuna yana daf da gazawa

sakin alkyabar SHAHEED ya yi ya juya ya nufi cikin bedroom dinsa ya bude wajen ajiyar magungunnansa ya ciro na ciwon kai ya bude frij ya ciro karamin ruwa ya bale ya hadiyi maganin sannan ya juyo yana kallon SHAHEED da ya harde hannayensa yana kallonsa ya ce" Idan ka ji ana cewa macen da ba za'a iya aure ba, gaba daya itace, dan da ka ganta a nan a kan kudi ko? Sai ta shaki wuyanka, dambe kuwa babu kalar wanda bata yi ba na gani, wanda na yi niya ta ga na ga tana yi nake bari ta gani a lokacin da take yi ama in fada maka ko a kwalar rigarta, kai dai halaya sak na rashin jin magana....ama ban taba jin haushinta ba dan na san dalilin da yasa take cikin wannan halin, SHAHEED tana da yaro , hakan bai taba damuna ba, da ido take min tatas sai dai ka ji ina sauke ajiyar zuciya....., kamaninta yadda ka san flower........" ya karashe yana sauke dan murmushi hadi da tatare girar goshinsa
Sai kuma ya gimtse lokaci guda ya ce" Na zata, zata ture, dan kofa saura minti ɗaya a Daura mata shi zan katse, hakan ya sa wayar nan bata fita a hannuna ba sai yanzu da na baka...., ka ga shiru ba msg dinta ba kiranta, da ace bata sonsa koda kadan ne, da ta lalata wannan aure nasu..... shi yasa nace ba zan taba yafe mata ba, ta idasa sakani yarda cewa *SOYAYA ITACE AZAL DINA!*"

SHAHEED kasa furta komai ya yi, yana kallonsa ya cire rigar dake jikinsa ya nufi bed dinsa, a takaice ya ce" Please, ka hanna kowa zuwa inda nake, nd wace Hajia ta aura min ta sauka bangaren Mah idan na shirya raba bed dina ta zo!"

Daga nan ya rintse idannuwansa, ya ci gaba da juyawa a saman gadon nan
abu daya yake son ganni a gabansa a yanzu, itace, ya dubeta ido cikin ido yace nawa take so da har ta iya zabar kudaden cen a kansa? ta san me yake iya bata ko ya mallaka mata a duniya ne? ta san shi me ya mallaka a duniya ne?, yana so ace ya ganta ido cikin ido ta fada masa shi zata sake ba wani jikinta ba shi ba?, zata iya zuwa ta ga wani ba shi ba? ita ai ba yarinya bace, ba kuma makauniya bace, ya tabata a irin yadda ya karanceta ta jima da gane abinda yake ransa, yarda ne bata yi ba bayan shi ya yarda da wanda yake ganni a nata idannuwan? wayo Allah, ya Allah haka azabtar nan take? ashe zafi ne da ita mai karfin gaske? "RAUDA, BA ZAN TABA YAFE MAKI BA!" yake fada muryarsa a shake, jikinsa kuwa ya kama hautsinew da zafin zazabi!

SHAHEED , duk murnar da yake na auren abokinsa sai abin ya sare masa, shi da ace zai yarda, walahi a yanzu yanzu sai ta amsa sunnan matarsa, sai dai irin yadda ya kulaceta abin ya bashi tsoro ainun, kuma a yanzu ba zai taba yarda ace da shi laifinsa bane, Bama zai bada damar nan ba in dai YUSUF ne, ba zai yarda cewar shine ya dace ya kwato ta ta yadda ita da kanta ba zata ankara da ta shiga Wajen da fitarta zai yi wuya ba!, sai gashi wani ya riketa a lokacin da bai shirya rabuwa da ita ba

Hucin numfashi ya fitar da wayarsa ya yiwa Sarkin bulala texte

minti kadan sai gashi ya shigo ya duka kansa a kasa bayan ya kawo gaisuwa wajen aminin uban gidansa sannan ya yi shiru yana jiran sakon mai Damagaran

Sai da ya gama daidaita abinda zai isar ya ce"

39

Azl 40
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim
Chapter 70 · 0% Book details