← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 117

Sashe 58

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali Atu ta saka hijab dinta ta rufe fuskarta tana girgiza kanta dan kukan da take tarewa
da kyar ta iya sasautawa tana kallon RAUDA dake fadan ta daina wai meye na koke koken?
ATU ta ce" Shine kika ki zuwa inda nake? shine kika ki dauke Abdul ku zo wajena?, kin san ko baki zauna a gidana ba kina iya zama a wajen Hajia ko? kin san Hajia na son ki domin Allah ko? shine ko ko tuna Ni kika yi tafiyarki kin samu Mah da wancen kanwar HONORABLE din ko?"

RAUDA ta yi murmushi tana fadin" ke kam ba dai jaje ba, to wai ki yi hakuri mana, sai da na daina baki hakurin ku ji min mata!"

itama yar dariyar ta yi tana kallon Salima da ta shigo yana murmushi ta ce" An ce fa ki je ku wuce, tuni sun fita sauran sun tafi ma"

Atu ta mike tana fadin" Bari in fadawa dear ya BARNI na kwana a nan din nima ko ki zo mu tafi"

daga Salima har RAUDA ido suka zarro, da kyar suka rarasheta bayan ta amshi numbar Salimar tana fadin zata dawo ta kawo mata wata wayar kuma su tafi tare idan ta fadawa Mah

ita dai Rauda murmushi kawai take yi, suka rakata har wajen mota sannan suka dawo
sunna shigowa falo Salima ya amsa kiran mahaifiyarta, tana kallon RAUDA ta ce" bari ki ji, walahi wanke wanke na jiranki dan na kai maki su na tara maki, idan na fito daga dakin Mama daki zan wuce na yiwa Abdul lesson nima na yi karatu ehe!"

tana fada tana yin ciki da dan gudu ne, hakan ya saka RAUDA sakin murmushi tana girgiza kanta ta nufi kicin din hankali kwonce ta cire dan kwalin nan ta rataya ta daure gashinta a tsakiya sannan ta shiga gyara plate plate din wajen pampo ta dauko sabulu da sponge ta shiga wankawa zuciyarta fesss, ta samu duk wani nauyi ya ragu sai nishadi take ji a cen kasan zuciyar Tata, ko dan ta hadu da ATU ne? ko kuwa dan ta samu nutsuwa a fira da Abdallah ne? ita dai ta fi jin dadin a cen kasan zuciyarta idan ta waiga ta waigo ta ganta tsaye itama ana bata ba tare da an yi mata gori ba, ana ciyar da ita ba tare da ance ta kawo kasonta itama ba, ana yin fira da ita tamkar wata mai cikakken yanci, tana motsawa yadda ta so da tunanin kiran wata Mama har cikin ranta bayan Tata uwar ta kwonta dama, bata taba tunanin bayan gawarwakin da aka barta ta hanga daga nesa zata kuma jin ana yi mata fada dan ta gyara ba, dan a da ta yarda cewa tunda aka birne iyayenta shikenan an birne mai sakata kuma bai hannata, ashe a duniya akoy wa'inda ke daukan dan wani tamkar nasu har su yi masa fadan rayuwa? zata ci gaba da godewa Allah dan shine ya yasare mata har ta samu wannan daukaka

tana aikinta da bege ne a zuciyarta har ta juyo dan daukar abin goge kofunnan nan na kwalba dan ya rataye su a jikin karfen da ake rataye su idannuwanta suka sarku cikin nasa,

da sauri ta rintse idannuwanta kasa kasa ta dafe kirjinta da ya buga mata da mugun karfi ta furta" A'uzubilahi minna shaidani rajim"

kofar frij din dake hannunsa ya mayar a hankali ya rufe , yana rike da kwalbar lemun da ya dauko ya karasa saman kujerar dake kicin din mai dauke da dan table, domin irinsu sun kai hudu a kicin din ya zauna yana ajiye kwalbar sannan ya sake dago dubansa ya kuma zuba duban da ya yi mata a dazu wanda ya gama raya mata sak yana mata kallon wata fasika subahanallah

idannuwanta ta dauke, dan bata iya irin kallon nan ba, da wahala ta iya jurewa, ama kuma ta kasa jure kawar da kan nata da kuma kasa hakura da abinda ranta ke ayana mata har ta sake juyowa ta kalle shi zuciyarta na dokawa tana jin tamkar ta je inda yake zaunen nan ta fada masa walahi abinda ya gani ba abinda yake tunani bane a kanta, ama ta kasa dan haba daya yakan cike mata idannuwa da tunani ne har ta ji ta gaza katabus idan yana wajen

idannuwansa ya cire a kanta, yana jin dacin da ya rike masa makogwaro har yanzu bai fada ba, shi yasa ya fito daukan jus dan baya bukatar surutu da kowa sai gashi ya samu yar nan a kicin din tana aiki , shi dai bai san me ya zaunar da shi ba, ya dai zauna ne ya kasa tafiya

karasawa ta yi ta dauki abin bude juss din, sannan ta dauki kofin da ta wanke jiki a mace ta karaso wajen table din ta ajiye kofin hannunta na dan so ya mata rawa dan har sai da ta dan jimke shi kafin ta kama kwalbar da abin budewar nan ta bude sannan ta dan dago a hankali idannuwanta suka sake shiga cikin nasa

daburcewa ta yi , a sanyaye ta ce " walahi ba abinda kake tunani bane a kaina, Ni ba yar iska bace, kuma shima hakanan, barkwonci ne da tsokana take saka shi yin wasu ab....."
sai kuma ta yi shiru tana haki tamkar an biyota da gudu

kaifafun idannuwansa kawai ke kanta, ci kanki bai furta mata ba ya dauki jus din ya fice, inda ta ji wani shayinsa da tsoron yannayinsa a ranta, wanda bata taɓa ji ba, tunda Allah ya haliceta, bata firgita a kan laifin da ta san ta aikata bale wanda bata aikata ba , a birkice ta zauna saman kujerar tana yamutsa gashin kanta, tana jin tausayin kanta, kai abinda ta sani daya ne kar ya fadawa Mah wata maganar da Mah din zata ji haushinta, dan bata san me yake iya fasarata ba, dukda ya san da wahala ya wani kula da abinda ya gani, ama kuma idan da bashi da wani nauyi a kansa, yanzun yana da shi, dole ire iren abubuwan nan ya taka masu birki a masarautarsa

yana komawa dakin ya nemi waje ya zauna yana kama sunnansa a cikin zuciyarsa lokaci guda yana fadawa kansa magangannun da suka yi tasiri sosai wajen nesanta shi da AZAL!, ya fada tun kafin ya gane kansa, bayan ya gane kansa kuwa ya fada babu AZAL din da ta wuce ya *SOYAYA!* , kuma in sha Allah shine da kansa zai yi yaki da kankin kansa ɗan gannin bata shafe shi ba, ba zai taba yarda da wannan *AZAL* din ba, komai rikicinta kuwa zai ture ne, dan haka ya kafa kai ya shanye jus din ya dauko wayarsa ya fara shiga sakwannin da aka ajiye masa na karin binciken da yake yi da irin tsarin da *TASA SALON SARAUTARSA* yake so ta kasance

wannan suka dan dauke masa hankali daga abinda yake tunanin ba'a kyauta masa ba, har ya dawo ya ringa basarwa tamkar babu wani abinda ke iya Dada shi da kasssssss a wannan fannin, dan binciken da TAJ ya masa a kan matar nan da Mah ke fushi da ita ya sake dauke masa hankali, wai ya je ya samu an yi mata sata, kuma bata san inda y'arta ta shiga ba, hakan ya sa tana neman susucewa domin zancecekun da take yi sai ya dauki fansa, ko a kan wa take nufi bai gane ba shi dai, ama kuma baban abinda ya fi ganewa shine babu abinda ke girgizata irin maganar mijinta da ta y'arta,da wannan ya rufe bincike bincikensa bayan ya ji jikin Uncle Umar ya warware sosai likitan na saka ran sakinsa nan da yan kwanaki idan ya sake murmujewa ciwukansa suka yi sauki sosai.

"Ashe baki da wayo? ashe shashasha ce ke?, uban me kike yiwa rawar jikin da zai sa kulun kina gindinsu? kin kawo su dakinki sai wahala kike ɗorawa kanki? Tun ina kauda kai har kin sa na magantu ke baki da hankali ne? Salima bari ki ji Salima A ruwa akan dade ba a wuta ba, kuma duk abinda kike tsinta a wajensu na soke ba ke ba YUSUF bale tarkacen dake tare da duniyarsa!" mahaifiyar Salima ke yi mata fada tunda ta shigo ta duka a gabanta

rai bace ta dora da fadin" kina kallo, tunda suka zo uwarsa ta kange komai, da gidanmu ama Hajia ta zo ta shinshinfida mana dokoki dan an dora dan so a mulki, a yi mu gani in tusa zata hura wuta, in dai mashayin yake kuma mazinaci? Sai ya aikata a cikin gari ta yadda zamu fito mu jefe shi!, ke dai ina hanna ki shiga harkar su, ina maki hannunka mai sanda har kin saka na yi maki magana, ki guji ranar da raina zai bace walahi sai kin kasa gane Ni, dan ba zan taba sasauta Maki ba!"

Kan Salima na kasa ne, hawaye na bin fuskarta, a zuwanta dakin mari biyu ta sha kafin wannan tashin hankalin ya biyo baya....., ba marin ne ya fi daga mata hankali ba irin furucin bakin mahaifiyarta
shin me ya yi zafi ne? me yasa ake son kai abinda yake danko da danko gaban wuta dan a raba? jinni daya fa akace, a jinni dayanma uba ne shi, ya kyautatawa kowa da kowa ba wai iya su da suke kannensa ba

a raunane sosai ta ce" Mama dan Allah ki yi hakuri"
Chapter 58 · 0% Book details