← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 117

Sashe 74

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdallah ya sauke ajiyar zuciya a tausashe , murya a jinyace ya ce" Zan so ace, tun ina cikin hayacina na cika abinda nake son cikawa, domin ke da kanki kin san idan aka zo wannan gabar kuma sauran saura ne, dan Allah ku yi hakuri, ba aurar maku yarinya bayan na san abinda nake ciki, da ace bata yarda ba duk irin yadda nake da burin aurenta ba zan tirsasata ba, Ni dai na san ina sonta domin Allah, shi yasa tunda na san da wahala ta rigayeni barin duniya na yiwa kaina wannan alkawarin na dukiyata itace maganarsa, Ni bani da dangi, koda ina da su ban san inda suke ba, basu san ko akoy Ni a duniya ba, iyayena sun yi aure ne irin na yawon duniya, mahaifina ya auri mahaifiyata, kuma Allah ya yi basu jima da auren ba suka koma ga mahaliccin su, dukiyata ta halal ce, ba gadonta na yi ba, nema na yi da zufata har na kai inda na kai, tafiyar nan da na yi na tataro komai nawa da burin yin rayuwa mai dan tsayi da ita na dawo nan kuma na yi shige da ficeta da lauyana an min abinda nake so, sai dai kashhhh, tunda satin aurenmu ya kama na zama ganinan, a kulun baya lafiyata ke yi, ko yau daurin auren nan da kyar makotana suka kamani muka je,ana gama daurawa na samu na dawo dan ba zan so ace tana cikin taron nan an je mata da maganar na fadi"

"Ya Salam, Abdallah, ama ciwo ai ba mutuwa bace ko? dan Allah ka daina magangannun nan mu je asibiti, ke ku tashi ku fadawa direba ya zo ya kama mana shi mu je asibiti" Mah ta fada tana tare hijabinta tana tare kukan dake son kwace mata, dan yadda yake magana yana jan numfashi ta bakinsa ko baka da imani sai ka tausaya masa

bai hanna su fita ba, sai dai sunna fita ya dubi Mah a lokacin da mike jikinta na rawa ta sake shiga neman layin Hajia ya ce" Mah, ciwona ya zama Cancer fa, dan Allah ku bar Ni na mutu a saman gado........................"

A lokacin ne kuma Mah ta juyo da sauri tana kallonsa, ta ki cewa komai sai nunawa direba da ta yi ya dauko shi su je, dan walahi ba zata taba iya barinsa a haka ba

Hajia kuwa sunna gama waya da Mah ta saka baban hijabinta itama tana neman layin Bah ama bata shiga hakan ya sa kawai ta nufi Part din Malik da fatan Allah ya sa bai kwonta ba, tare da yan rakiyarta

sunna karasowa basu tsaya kiraye kiraye ba suka bude mata ta wuce ciki

a bakin kofar nan mai madubi ta tsaya ta buga sannan ta murda ta shiga

A kwonce da yake idannuwansa kawai ya dago ya sauke a kanta sannan ya lumshe yana godiya ga Allah da ta zo a daidai lokacin da yake da bukatarta

Karasawa Hajia ta yi, ta zauna a kujerar dake daf da shi a sanyaye ta furta" Yau ko a leka Ni? Malik wuni guda?"

Shiru ya mata dan ya san dama sai an masa yan jaje,

Idannuwansa ya dago jin ta ce" Yaya muka ji da wannan sabuwar masifar? yau Ni Hajia Azal ta fado mana gida, Malik ba zan so ka ga yarinyar nan ba, kade kaden nan fa da ka ringa juyowa su ne, Ni kam safiya na yi ka saketa ta je gidansu, ba matar jikana bace y'ar nan ido a tsakiyar kai!"

Murmushi ya yi ya sake dago da kansa yana kallonta, kasa kasa sosai ya furta" Ta fado maki dai, kuma ba inda zata je!"

"na'am? me kace?"Hajia ta fada tana dubansa, dan yadda ya yi murmushin kamar wanda zai datsa mata magana domin haka yake yi mata lokuta da dama

kai ya cire ya ki bata amsa, a nutse ya ce" Bani da lafiya fa, kuma ina jin kamar wanda zan mutu, kin ga jikina karra rikicewa yake yi fa!"

a tsorace ta kalle shi, da sauri ta mike gabanta na faduwa tana sake duban yadda ya ringesa, ta kai hannunta wajen wuyansa, ai kam da gumi jikin nasa sosai dan haka ta nemi rikicewa tana fadin" Na shiga uku, ka ga cen wai mijin RAUDA ne akace ba lafiya shine na zo sanar maka ka sa a kai Ni, kuma sai in ji wai kana min zaka mutu?"

Idannuwansa dake lumshe ya bude a kanta, sosai ya so yin magana, sai dai ya rasa me zai ce, ya so maida idannuwan nasa ya rufe wayar Hajiar ta sake daukan kuka

a tare suka kalli wayar, Hajiar ta duba da kyau tana kankance idannuwanta ta ce "AMEERA din ce, bari na ji?"

Hajia ta daga kiran ta saka a amsa kuwa, sai ta ji Muryar Salima tana dirzar kuka tana fadin......

😭😭😭😭😭😭😭😭

Salima na dirzar kuka take fadin" Hajia, walahi fa inaga ya rasu innalilahi mun shiga uku!"

Hajia na tsaye ne, sai gata a zaune ta zube, idannuwanta na wani iri muryarta na rawa ta ce" Ke kuwa wani irin kina ga, dan Allah bani ANDIYAR!"

YUSUF dake ringeshe ya yi niyar dagawa Hajia hankali ne sai ya mike zaune yana kallonta , jin ta ambaci Andiya, kuma maganar rasuwa

Hajia walahi ita Raudarma ta summa, kuma Mah gatanan tana kuka, shine na yi kiranki dan walahi walahi Mah ta rufe shi ama direba ya taho gidan yanzu "

Me Hajia zata yi banda kwasar kuka, hannayenta saman kai wiwi take fadin" Mun shiga uku mun lalace wayo jikata ta rasa miji, innalilahi yau na yi wani rashin, la'ila ha ilalahu Muhammadu RASULULAH Sallallahu alaihi Wa sallam "

"Wai meye haka wai?" ya fada da dan karfi dan yadda Hajia ke rizgar ihu a kan abinda ba'a wani tabatar ba kuma bayan ba kyau yiwa mamaci irin kukan nan ya saka shi katseta yana mikewa tsaye

hankali tashe Hajia tace" YUSUF wannan yaro balaraben nan da ya gaisheni, shine ya rasu,dan Allah ka sa a kai Ni ka ji?"

Gaba daya jikinsa sai da ya mutu, a hankali ya koma ya zauna yana daukan wayarsa ya yi kiran direbansa amintace
jim kaɗan ya daga da salama a ladafce ya ce" Allah ya taimakeka gani na shigo dan na iso da sako, Allah ya yiwa mijin Hajia karama rasuwa, na baro su Mah a cen dan na zo na ji abinda zaka fada"

Ya jima wayar a hannunsa, zuciyarsa na tsintsinkewa kafin a hankali ya furta" Allah ya masa rahama, ka wuce ciki a je da likitoci su duba shi da kyau, idan sun tabbatar a gyara shi a zo nan da shi , idan bai rasu ba maza a kawo shi in yanzu za'a fita da shi a min magana"

Daga nan ya kashe kiran yana kallon Hajia take ta margaya kai taba sharar hawaye
ajiyar zuciya ya sauke, sosai jikinsa ya mugun mutu, dukda a bincikensa ya san da ciwonsa da irin matakin da ya kai domin Taj sai da ya je har wajen likitansa, da likitan ya ki fadin sirrin abinda ke yawan kai Abdallah wajen nasa sai da aka sada shi da YUSUF din sannan ya fada tun a nan ya ba masu gadi damar duk lokacin da ya zo su bar shi ya shigo, sannan ya dauke kansa a kan duk wani shige da ficen su sai na ranar da ta shigo da dare nan ya ji haushin abin, shima a lokacin dan Hajia ta gama guma masa tashin hankali ne na wai ita zata zabar masa matar aure
A nutse ya ce" Ki yi hakuri, idan ya rasu baya bukatar koke koken nan, ki masa gatan da kike yiwa iyalinki a kwana ana nema masa gafara kin ji?"

Hajia ta sauke ajiyar zuciya a zaunen da take hannaye bibiyu a fuskarta, a raunane ta ce" Allah ya masa rahama, yarinyar nan ke bani tausayi, ina matukar tausaya mata, tana son mijinta, gashi yarinyar akoy tarbiyya da mutunci, ashe ba zasu rayu da mijin ba? rasuwar miji baban tashin hankali ne a rayuwa, Allah ya bata dangana da hakurin rashinsa "

Idannuwansa ya lumshe har Hajia ta gama ta mike tana sake tambayarsa jikinsa
Da hannunsa kawai ya mata alamun da sauki, ta so sakawa a kirawo likita ya nuna ya bar shi, hakan ya sa ta fice ta tafi ta shiga neman layin baban malamin fadar dan ta sanar masa, sosai take tsaye kan lamarin sai bugawa take tana fadin mijin jikarta ya rasu, nan da nan har an shiga kai kawon taya zama a cikin daren nan, abu da masu hannu da shuni

TABAS RAUDA ta yi rashi a karro na biyu, rashin dake girgiza duniyar wace ta rasa, rashin da koda babu soyaya sai an girgiza, ita din ta girgiza, domin a lokacin da aka iso da ita a motar asibitin fadar bata san inda kanta yake ba, a lokacin kuwa su Bah sun ji, uncle dinta kasa rike hawayensa ya yi, hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa danma yana tare da mutane ana ta dannarsa, ama haka ya kwana ya je cen inda RAUDA take, ya dawo inda aka shinfide ABDALLAH
RAI KENNAN, BAKON DUNIYA, MUNA SON KA SAI KA FITA A LOKACIN DA AKA DAUKAR MAKA, ALLAH LA BAMU KYAKKYAWAN KARSHE

Tun cikin dare ta farka, sai suka yi mata allurar barci saboda kukan da take yi, Mah kuwa tana wajenta tare da Salima, Atu kuwa tunda duku duku ta karaso itama tun cikin daren mijinta ya fada mata, kwana ta yi tana kuka idannuwanta sun yi luhu luhu, duk idan ka kalle su sai ka tausaya masu

Da sassafe ta kuma farkawa, wannan karron ba da kukan ba, ama kuma idannuwanta ko bude su bata iya yi

muryarta cen ciki ta furta" Mah, har an yi sutura?"

Mah ta girgiza kai

A raunane ta ce" Mah a kai Ni na masa addu'a kin ji?"
Chapter 74 · 0% Book details