← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 117

Sashe 13

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali RAUDA ta karasa bayi ta yi wanka da brush ta fito ta daura alwallah ta shige ciki dan gabatar da sallar da aka sakata yin lati dan dole, inda yar gidan Mama ta bita da kallo a lokacin da ta shige daure da zani daurin kirji cinyoyinta du a fili da cen wajen wuyanta da hannayenta dai da kuma gashin kanta
Baki ta tabe kasa kasa ta ce" Du kyanki sai na auri mijin da ya fi ki in ji Mama, aikin banza kyan banza!"

Bayan ta gama sallah carbinta ke hannunta tana ta istigfari, a hankali a hankali ta fashe da kuka tana hade bayanta da jikin bangon dakinsu mai dauke da dati, dan a gidan idan Akoy wajen ajiye kowani tarkace dakinsu ne, duk yadda ta kai da gyaran dakin a banza ne tunda datin cikinsa ya ishe shi

A hankali take kukanta mai gunji da ratsa zuciya

Shin ina zata saka ranta ne?

Ina ake so ta kai kanta ne?

Dan ta hadu da maraici shine ta yi laifi?

Me ta yi da zafi?
Tana bakin kokarinta dan gannin ta faranta ran Mama, ama ba zata taba cin arzikin mutuntawa ba bale arzikin a dauketa tamkar y'a?
Me Mama take tunani ? Dama ita bata sakawa ranta zata yi aure ba a duniya saboda ba zata taba yin aure ta haihu ta mutu ta bar abinda ta haifa ya ga irin izinar da take gani na rayuwa ba, haka kuma bata taɓa sakawa ranta zata yi arziki ba, sai dai nacin da Mama ke mata na yau da kullum kan natawa cewar a duniya babu matsiyaci irinta dangin tsiya dan iyayenta da yan uwanta sun rasu a halin talauci wanda Allah ne ya halicce su haka Shikenan sai ya zama abin zagi? Idan ta samu zama irin wannan takan ji kamar zuciyyarta zata tsaya
Ita a zuciyarta babu gurin farin ciki
Babu gurin tunanin samun jin kai a duniya
Mutun biyu ke sakata cenza tunani lokuta da dama BARA'ATU da ABDUL HAKIM, ita Bara'atu ta riga ta san lagonta har tana sakata daria da murna, shi kuwa Abdul Hakim yana da uwa da uba a duniya da dangi ama irin rayuwar da yake fuskanta mahaifinsa ya ki bada shi wa dangin mamansa ya sa ta dauka itace duniyarsa, itace uwarsa, ubansa danginsa

Da sauri ta shiga share hawaye tana cire hijabinta ganninsa ya shigo da salama hannunsa dauke da bakar ledar da ya siyo kayan karin nasu sai farin ciki yake yi ya nemi waje ya zauna yana fadin" aunty harda kifin babale mai ayaba yau na siyo mana"

A dole ta kakalo murmushi tana gyara zama ta ce"iyeah bari na wasa hakorana Sarkin cin dadi ya samo mana kayan dadi"

Shima farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa ya bude yana mika mata nata, da nasa sannan ya bata cenjinta

Murmushi ta yi ta rike cenjin a hannunta tana tunanin yau ko da isheta zuwa wannan gagarumar restaurant din mai sunna ABUSA? dan tana so ta yi sabon kamu ko ta samu masu nauyi, ama kuma ba zata yarda ta tsaya daga nan ba sai ta samu baki ko uku ne yau din dan ta dan samu kudin ta ba Mama ko a bar mata Abdul ya kwana cikin nutsuwar zuciya ba zagi bare hantara

Sunna gama cin abincin ta haɗa ledojin ta raka shi bakin bayi ta tsaya ya shiga wankan
Yana fitowa ta bashi brush dinsa ya wanke bakinsa sannan ta raka shi daki ta kuma tsaya ya saka kayansa na islamiyya domin yannayin kwakwaluwarsa kin daukansa suka yi a boko , dan yannayin na Abdul Hakim sama sama ne

Cikin nutsuwa suke Tahowa daga dakinsu zuwa falo tana rike da hannunsa yana magana kasa kasa

Murmushi ta yi kasa kasa ta ce"

Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA

🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*

*PAID BOOK*

_Bismillahir rahamanir-rahim._

*8*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
KARKU BARI A BAKU LABARI🥳

Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*

Murmushi ta yiwa maganar da ya yi, kasa kasa ta ce" Ba Abul bane bawa, Abdul ne, kuma kai bawan Allah ne ba na mutun ba boyboy"

Dan rabewa ya yi jikinta a lokacin da zasu fice sakamakon gannin Mama ta dosa falon
Itama dakatawa ta yi har maman ta shige sannan suka fita kusan sunna sauke ajiyar zuciya a tare

A Nutse suke tafiyar, tana rike da hannun Abdul har suka karaso kusan masalaci daidai inuwar su malam da su Liman

Kamar yadda ta saba gaishe su a mutunce ta duka ta gaishe su sannan suka yi gaba

Sun dan yi gaba kadan Muryar babansu ta saka su dakatawa suka juyo kusan a tare

Da dan mamaki saman fuskarta ganninsa sanye da farar jalabiya kuma yannayinsa na nunin wanka ya yi harda kanshin turare ta ce" Baba?"

Shima murmushi ya yi yana kawar da mamakinta, dan sarai ya karanci mamaki ne ya kamata ganninsa a Anguwa a irin wannan lokacin , a da idan suka yi fada da Mamansu ya koma gidan giya Kennan sai ya yi niya dan kansa ya huce zai dawo gidan

Da kula yace" Ina zaku je?"

Dan murmushi ta yi tana jin kamar kwallah na neman cika mata ido ta ce" Makaranta zan raka shi, daga nan na kai shi wajen inna ya masu kwana biyu in bai tada rigimar sai an kawo shi wajena ba"

Murmushi baban ya yi cike da jin tausayinsu dan ya san saboda sun yi rikicin ne zata matsa shi nesa da ita kar Mamansu ta dake shi, yana laluba aljihunsa ya ce" Bari na ga ko na alewa na baka ɗan gidan auntynsa"

A aljihunsa babu wani abun kirki ko kwondala babu dan bai yarda ya zauna da kudin da ya yi niyar yi mata siyayar kayan makarantarta a gudun kar matarsa ta sace kudin ,
Da yar kunya ya dubeta zai yi magana ta yi gagawar fadin" Baba munada cenji a nan fa, zan bashi ko Abdul din baba?"

Abdul ya gyada kai yana bangalar darkyar da ta wuce misali yana kallon baban nasa, shi dai ya san babansa ne ama ba wata shakuwa a tsakaninsu sai ta shinfidar fuska, to yaushema baban ya zauna bale har ya wani shaku da shi?

Umar sai ya ji wani iri a zuciyarsa, yarinyar nan ba aikin fari take yi ba ba baki ba, ama kuma a wajenta ake amsar kudi, ya Allah ka sa Rauda bata wasa da mutuncinta duk rintsi

Kasa cewa komai ya yi sai jadada mata da ya yi yana wajen su liman , hakan ya saka mata farin ciki sosai a zuciyyarta suka tafi ita da kanninta a kafa har makaranta

A lokacin da ya shiga ya zauna suka gaisa da malam yana ta faman yi mata annuri ta dawo karkashin shuka ta zauna dan sai an tayar da su ta kai shi wajen inna ta koma gida, ta zauna ta shiga contact dinta a hankali tana dubawa da son ganin wanda ya dace ta sakawa Hi, wanda yake nacin son ganninta kuma ta san idan ya zo baya tafiya bai yi mata ALKHAIRI ba

A gaskiya ta irga mutane da yawan gaske, har sai da ta saki murmushi mai ciwo tana kallon cikin makarantar su Abdul a ranta ta ayana' Sai kace mai zaman kanta? Wannan ko mai sana'ar amsa a hannun maza ta biya masu bukatu ai sai haka, babu kalar wanda bani da shi Ni RAUDA ' ,
Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta kore tunanin dan bata so ta dagawa kanta hankali a tunanin da ba zai fisheta ba
Chapter 13 · 0% Book details