← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 117

Sashe 75

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Atu ta sake sada kanta wani kukan na kwace mata, hakan ya sa ta fice a dakin, Mah kuwa ta yi jarumta sosai ita da Salima suka maida mata zumbulelen hijab dinta Mah ta sa aka kawo mota har cikin asibitin suka shiga su hudu aka nufi bangaren Hajia da su, inda gawar take

Sunna zuwa Mah ce kadai ta rike hannunta suka shiga wajen da gawar take
A lokacin ana idasa shirya shi, fuskar nan tasa luwai luwai sai sheki take yi , idannuwansa a lumshe suke kamar wanda yake barci

Tunda suka shigo YUSUF ya dago dubansa ya sauke a saman kansu ya ji wani irin tausayinta wanda bai taba ji ba
a nutse ya dauke yana jiran ya ji ta barke da kukan da ta saba, sai ya ji shiru har ta karasa gaban gadon da yake kwonce a hankali ta ɗora lebenta saman goshinsa ta mana masa kiss, fari farin furfurar gemunsa ta dan zubawa ido kafin a hankali ta furta" Allah ya maka rahama mijina"

Mah ta lumshe ido, hawaye suka biyo kumatunta, ta sake kama hannayen RAUDA ta juyota tana kallonta a hankali ta janyota jikinta ta rungumeta, sai ta ringa sauke wata irin ajiyar zuciya hawaye na bin kumatunta a cen ciki ta furta" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une"

Daga nan suka koma bangaren Mah, wanda ya fara daukan mutane domin tunda asubahi gidajen rediyo aka fara sanarwar rasuwar, da kuma wa'inda aka kiraya aka sanarwa, AMNAH kam dala a bangaren su Salima ta kwana, kuma bata cika tashi da sassafe ba, shi yasa bata san abinda ake yi ba har aka fice da gawar Abdallah aka kai shi makwoncinsa na gaskiya

Sai kusan karfe biyu na rana ta farka a barci ta sauko daga saman gadon maman su Salima ta nufi bayi ta yi wanka ta dauro tawul din Salima dake bayin rataye wanda ya jima nan rataye domin ko ita idan ta yi wanka a yanzu ba zata yi anfani da tawul din nan ba sai ta wanke shi, ama ita ta ratayo abinta ta fito tana jin yinwa na neman yi mata ila suka hade da Salima wace ta zo daukan wayar maman nata da ta sakata zuwa ta daukar mata domin sunna cen bangaren Mah gaba dayansu harda Hajia baba , dan tunda Hajia Baba ta je suma suka je babu wanda ya tashi tunda basu ga ta tashi ba

kallon kallo suka yiwa junna, Salima da bata santa ba ta ce " Bakuwa muka yi banda labari, sannu da zuwa"

AMNAH ta sake duban Salima sama saman nan ta ce" Yauwa, Please a kawo min abinci i'm hangry, ina Hajia ne ta shiga ko tana falo?"

irin yadda take magana tana wani kalkaltu ya saka Salima yin sororo tana kallonta, sai kuma ta ce" Ta tafi bangaren Mah wajen makokin mana baki sani ba? " Tana bata amsa ne dan ta ganta tsamo tsamo a dakin mahaifiyarta, ta tabata ko Wacece ta kusa ce dan haka kawai da wahala ka iya ratsa falo biyun nan ka iso nan kuma har da anfani da bayin dakin, lalle ta kusa da kusa ce

"Rasuwa? a ina aka yi rasuwar kuma? Yaushe?" Ta fada tana dakatawa daga niyar cire tawul din da ta yi zuciyarta na rawa dan bata son ta ji maganar mutuwa, ko kadan bata so, abinda ta ki jinni a rayuwarta kennan, idan ta ji maganar mutuwa sai ta tsani wanda ya mata maganar ta daina yi masa magana sam, dan bata son abinda zai taba mata farin cikinta ko menene

Da mamaki Salima ta sake kallonta, to wannan tun yaushe rabintada fit? ko tace anya mutun ce kuwa? to ko aljanna ce ai tana iya gane an yi rasuwa abinda yan wani gari ma suka ji suka zo? ikon Allah
Ajiyar ta sauke ta ce" To Ni kam ban gane ki ba, ki yi hakuri, ama rasuwar nan tun jiya aka yi ta fa, kuma mijin RAUDA ne ya rasu, kowa yana wajen Mah fa, kuma ace wani da yake cikin gidan nan bai sani ba?"

Baki ta tabe, tana yarfe hannunta , itama fa tana ba Salima amsa ne dan ko daga skin dinta ta san ba yaku bayi bace
A gafarance ta ce" Baki sanni ba? Ni ce matar HR EXCELENCY , I'M AMNAH!"

Sai da Salima ya sake kallonta da sauri, dan abin ya shige mata kunne kai tsaye ne
kai ta dauke, cike da mamakin wai da gaske ko a'a?, sai dai tunawa da ta yi y'ar Wacece, kawar mamanta sai ta yarda, ama abinda ya bata mamaki dama a nan aka dauketa? ai ita ta yi tunanin tana bangaren yayansu, kuma wannan abin da ya faru ba wanda ya tuna da ita,
ikon Allah sai ta kasa tafiya har ta bude yar akwatinta ta ciro wata riga irin masu bin jikin nan ba ruwanta ta tube a nan ta saka bayan ta saka breziya da pant

Salima ta dago kanta jin tana fesa turare, da kula ta ce" Aya, ban gane ki ba ai, inai maki oyoyo, ki saka hijabinki mu je wajen Mah din, a cen ne ake zaman rasuwar, mijin RAUDA ne ya rasu kanwar Malik ce!"

Har ga Allah idan aka kirayi sunnan Mah sai ta ji gabanta ya fadi, ko dan an gama fada mata Mah din nan tsaf take iya hannata zama da mijinta ne? mtssss ita dai sam bata son ko sunnan matar, ama kuma sai ta shiga neman hijabin da ta amsa na maman Salima ta dauka ta saka ta dauki tanfatsetsiyar wayarta tana kunna wa dan tun cikin dare da ta gaji da kallon Tiktok ta kashe ta yar barci ya yi awon gaba da ita sai tashin nan da ta yi, bata nemi sallah ba, ko bata yi ne? bata dai yin ba yanzun

Salima haka kawai take gannin kamar AMNAH din nan bata da kamun kai, kuma faratunan dake hannayenta hade da kunshi sun bata mamaki matuka, ama kuma akoy fari, farinta har wani yellow yake yi, kuma idan tana magana idannuwanta a tsaitsaye suke, hakama yannayin maganarta ita kam sai take gannin kamar irin mutanen nan yan duniya haka, ama kuma ba zata yanke mata hukunci haka ba, ta girmamata a matsayinta Na matar ƴaƴanta, ta yi mata jagora sun tafi a mutunce har bangaren Mah, a lokacin Hajia na tausar RAUDA kan maganar cin abinci, firr RAUDA ta ki ta ci komai, ga kuka, ga jikinta zafi, hakan na neman birkita lissafin Mah da duk wani mai kaunarta, domin tunda aka saka ta saka wani katon hijab aka bata carbi aka tabatar mata daga jiya ta dauki nadin amarci a kanta yau na takaba ya kamata, wata hudu cif da kwana goma a duniya, du sai ta sake rikicewa har suka shigo tare , Salimar ta kai wayar wajen Mamanta dake zaune tare da dayar abokiyar zamanta, sannan ta wuce ciki inda Hajia ta shige da RAUDA, wato dakin Mah, hakan ya sa mahaifiyarta rakata da harara a ranta tana jin in sha Allah wannan karron idan ta rike Salima sai ta yi mata tsinanan dukan da zai dawo da ita hayacinta, dan ta kula kyaleta da take yi ne take son fin karfin ta

Zaunar da RAUDA Hajia ta yi bakin gadon nan, ta amshi madara mai dumi da Mah ta kada mata tana kallonta ta ce" Maza sha kadan kadan, ba'a so idan ciki ba komai a ci abu da yawa kuma ba zai yiwu ki zauna da yinwa ba kin ji y'ar nan? yaya zamu yi? Allah ne fa ya amshi abinsa, idan kika yi haka ai baki godewa Allah ba, ki yi hakuri kin ji? mutuwar nan muma ita muke jira, Allah ya kyauta namu zuwan"

Mah ta amsa da amen , ta mikawa Atu kwanon abincin ta nufi wayar dake dakinta tana kukan neman agaji

wayar ta daga a nutse ta yi salama
YUSUF dake zaune a falonsa tare da baki a nutse ya ce" Barka da warhaka Mah, yaya hakuri"

Mah ta amsa a hankali sannan ta yi shiru tana sauraronsa

A nutse ya ce" Akoy daidaikun mutane dake zuwa da maganar bashi, na kansa da wanda yake bi"

Mah ta bude idannuwanta dake dan sade, a hankali ta furta" Aya, ka ga kuwa a jiya Allah bai bashi ikon yi min maganar nan ba, ga fa akwatin da ya bani ban sani ba, ko abinda ya yanke haka din ne, ita daya ce zata gaje shi ko yayane, ga dai takardu na dukiyoyi da kys din gidajen da na motoci da kuma harkar banki, bashin da ake binsa ai ko nawa ne kawai a fadi sai a biya ko?"

Dan shiru ya yi, sannan ya furta" Na biya , wa'inda aka kawo kuma gasu ajiye"

Mah ta ringa godiya, har sai da ya ji kamar yace ya isa ama ya san in ya fada din ma sai ta ga dama zata bari

"Salima yi maza jiko min tawul na goge mata jikin haka, barshi shan madarar ya isa haka" Muryar Hajia ta shiga kunnayensa

A hankali ya dan daga idannuwansa a lokacin da Mah ke fadin" Ina Amnah ne? "

Har ga Allah sai ya rasa wace Amnah, sai da ya ji Salima na fadin" Tana falo wajen su Mama " sannan ya dan yi shiru ya tuna ashe wannan mai kama da birin ce Amnah
Shi kam sai ya yiwa Mah salama ya ci gaba da hulɗar dake gabansa

A cen wajen Mah kuwa sunna samu Rauda ta dan daidaitu suka fito falon Mah karami, a nan Mah din ke sanarwa Hajia abinda ya faru a jiyan

sosai Hajia ta sha mamaki, Bama kamar maganar dukiyar nan, sai ta rasa abin fada, sai adu'ar da ta ringa binsa da ita ta saka Mah ta kai akwatin ta adana tace sai Malik ya nutsu a kai masa abinda ya yanke sai a yi
Mah dai ta adana ama ba Malik zata kaiwa ba gaskiya, Bah zata ba ya ga uncle dinta abinda suka yanke shikenan.
Chapter 75 · 0% Book details