← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 117

Sashe 97

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe Mah ta ce" kin ga a jiya, na ji tashin hankalin da ya so rikitani, da kyar na iya hawa salaya na fadawa Allah har na samu sassauci , a jiya ne Hajia ta bani umarni a matsayinta Na uwa a wajena kan a hada aurenki ke da YUSUF , ta nuna na isa da ke zan maki magana, na nuna idan kika ki fa? ta nuna na isa da ke, na fito na je part din Hajia dan na amshi wayar Salima na yi kiran ki dan a lokacin tawa a hannun Hajia sai kawai na tarda Amnah da mahaifiyarta da kawayen mahaifiyarta sunna furuci kamar haka..........."
Ta kwashe komai ta sanarwa RAUDA wace ta kwalolo ido kirjinta na zafi da jin lalle za'a ci uwar sabada ita da Amnah da uwarta dan walahi talahi furucin da suka yi a kan Mah sai ta rama, dan babu ɗan da aka haifa da jinni da zai zagar mata uwa ta kyale shi, hakan ya sa take dantse lebe tana matse hannu tana adu'ar a gama firar nan ta tarda Amnah su daku idan ya so a rufeta a kurkukun masarautar!

Mah ta yi shiru kirjinta na dokawa a hankali ta ce" Sai gani sanadiyar abinda na jiyo da kaina na nemi babanku aka je aka daura maku auren da ta yiwu zaki ji kin tsane Ni, dan na nuna son kai, na nuna karfin ikon kina min biyayya na kakaba Maki auren da ba lalle ki so ba domin kamar yadda kika sani YUSUF baya ji, Yusuf ya yi zaman bin mata, YUSUF mafadaci ne, baya jin magana a da, a yanzu Ban san ko har yanzu yana aiyukan nan mararsa kyau ba ko ya fasa? abu daya na sani ba kowa zai so aurensa ba, komin mulkinsa ,komai kudinsa ba kowa ne zai so kasancewa tare da shi ba, shi yasa na zaunar da ke dan na roke ki......."

A hankali Mah ya sada kanta, zuciyarta cike da tsoron amsar RAUDA, dan walahi ba zata so ta ji wani abinda zai rikita mata lissafi a kan hadin nan ba, ta ji ta karra tashi da kaunar hadin a ranta bayan doguwar adu'ar da ta yi a jiya, dan haka a tausashe a kuma raunane ta ce" Dan Allah......."

Ta sake yin shiru, a hankali ta saki hannayen RAUDA ta hade nata hannayen a hankali ta sake furta" Dan annabi,......Ki yi hakuri ki amince da hadin nan....koda na wata daya ne tak....koda na sati
daya ne tak ..............'''...

Da sauri RAUDA ta kai hannayenta ta riko na Mah a dan rikice ta ce" Mah"

Mah ta katseta tana fadin" Ki bari na roka, dan na san na taro maki rigima, ki bari na roka dan na san abu ne marar dadi, ki yi hakuri ki bari na roka dan a yau yau nake da muradin ki je gidan cen a matsayin matar gidan, YUSUF Sarki ne, sarauta Allah ke naɗa bawansa, tunda ya hau sarauta alhamdulilah yana iya yinsa a matsayinsa na sarki, yana kokarin kare dukkan abinda ya dace, sai dai sarki sai da sarauniya, tasa sarauniyar maimakun ta zamo uwar marayu sai ta zamo makiyiyar marayu, ta kori da yawa ta zagi da yawa, ta wulakantar da yawa..... RAUDA kin san yau da gobe, na san har yanzu bata samu damar da take bane, da tuni ta aikata abinda take da niya, sai dai Ni na san karfin ikon mace a kan namiji, duk macen da ta yi niyar rikita maka lissafi cikin hikima zata saka ka aikata mugwayan aiyuka ba tare da ka ankara ba , saima ta Barka a zuwan kai ne ke tsara komai dan ka isa, bayan ita ke tafe da ragamar rayuwarka, Ni na tabata idan ta samu dama sai ta dama tashin hankalin da garin Tsatsunburum zai hargitse da fitintinu na yau da gobe ......... Daughter..........i bg you, ki amince da............"

Da karfi RAUDA ta shige jikin Mah ta rukunkumeta, murya na fita da wani irin sauti cen cikin makogwaro ta furta" Mah, Please ki yi shiru........"

Idannuwanta ta lumshe itama ta rungumeta,
a hankali ta furta" Mah......., ina dalili zaki ringa wannan magiyar bayan kawai cewa zaki yi ke wance na miki miji ki je ki yi biyayya?"

wata irin ajiyar zuciya ta kwacewa Mah, a hankali RAUDA ta sake rungume Mah, a raunane ta ce" Koda mahaukaci ne, ko maye ne, ko marar asali ne in dai ke kika zaba min in sha Allah zan yi biyayya bale wanda kika haifa da cikin ki........, Mah rashin jin sa ya kai nawa ne? koda ya fi nawa nima ai ba jin nake yi ba...., ama a haka kika daukeni tun baki san usulina ba, kika rungumeni kike ciyar da Ni ba tare da jiran na biya ki ba, kike tufatar da Ni ba tare da zagina ba, kika bani muhalli ba tare da mun hada kudin haya ba, karshe kika bani uwa da uba da dangi nawa nima wa'inda nake rayuwa a cikinsu kai tsaye da yanci, shikenan dan ina butulu sai a zauna ana hadani da Allah dan an min miji?......Dan Allah ki daina min magiya kar wani ya ji bayan mu na ji kunya Mah........"

Hawayen Mah sai yanzu suka bale, Walahi ta yi tunanin RAUDA bori zata dora tace bata so, ta zata da kyar RAUDA zata amince da wannan magana, sai gashi cikin kudirar Ubangiji yarinyar ta yi mata ba zata har ta sa ta ji wani irin kwarin gwuiwar da ya sakata sakin dariya bayan ta dago ta hannata kukan

Mah na dariya tana kallonta ta ce" Allah ya miki albarka, kin ga kwonta huta ina zuwa"

Mah ta mike cike da farin ciki ta fice a dakin

Mah na fita RAUDA ta sauke ajiyar zuciya ta sada kanta zuciyarta cike da tunani

Yau Yau zata tare? ..........kwarai kamar yadda ta nunawa Mah ta karba har cikin ranta ta karba din, kuma maganar tarewar zata je din............sai dai abinda yake dan kai kawon mata a zuciya shine..................ba maganar wani abin bayan wannan! daga shi har matarsa sai ta saita masu zama ne!, domin shima haushinsa take ji sosai da sosai!

________________________________

Damagaran

Zaune suke a falonsa, Shaheed da matansa, wato NAJEEBA da Nadia

Tun dazu yake waya da YUSUF, su kuwa sunna fira a tsakaninsu, ama tunda ya furta maganar sabon ango NAJEEBA ta yi shiru tana jiran ya gama

sun jima sunna yi kamar yadda suka saba sannan ya kashe yana murmushi ya juyo inda suke zaune dan meeting aka hada na maganar fita, sunna so a karra masu yawan fita a wata shi kuwa yace bai san zancen ba

Murmushi NAJEEBA ta yi tana kallonsa ta ce" Mai girma bawan Allah, abokinka aure wata da watanni ama ba'a daina kiransa sabon ango ba? koda yake, kaima ai ango ne Yaushema aka baka mu?"

murmushin ya yi shima ya ce" Mai girma baiwar Allah jiya fa muka kara masa wata, ina wannan wace mijinta ya rasu? wace Mah ke riko? ita muka bashi jiya"

Dif ta yi tana zarro idannuwanta, a hankali ta ce" Aban MUHAMAD kana nufin RAUDA?"
Shima ido ya dan zuba mata dan jin ta kama sunnan cirat kafin ya gyada mata kai

Kai ta dauke tana murmushi hadi da dan kada kafarta a ranta ta ayana' Masha ALLAH, yanzu sakon Amnah take ko wa ya zo daidai lokacin da ya dace ya zo, fita kuwa yanzu zan yake ta oga dan idan da hali yauma ka barni na je na yi Allah sanya albarka a wannan aure, domin yanzu Sir YUSUF ya yi aure mai sunna aure?'

Da wannan suka ci gaba da tattaunawa tsakaninsu na tsayar da mafita.........

___________________________________

Tunda tashin busa da hayaniya ke tunkaro dakin Mah gabanta ya ringa dokawa a gudun da ya wuce ka'ida, shi yasa ta yi tsuru ta zubawa Kofar ido har aka bude Hajia ta fara shigowa da sandarta a hankali, sai matan da aka yiwa lakabi da matan daraja wa'inda suke na darajan domin sukan halarci taron daraja ne, hannayensu dauke da akwatuna masu ɗauke da alkyaba da tufafi da kuma takalmi da sarka na gidan sarauta

Daga bakin kofa masu busar suka tsaya, sai dai tamkar a dakin suke busawar dan ita tuni ta nemi rikicewa, bale da ta ga niyarsu bayi zasu kaita, da girman nan nata wani saka lalle ne zasu yi mata, ko sun manta shekaran jiya ta gama takabar wani mijin da ta aura ko menene?, ko kuwa tarin girmansa ake son karra jaddada mata aka yi hakan da ita?, ita dai ta san wata irin juwa da tashin tsigar jiki suka hannata gane inda za'a nufa da ita, kuma me ake nufi da ita, har aka yi mata rabi da rabin wanka domin kuwa sket dinta a jikinta da karamar riga firrr ta rike su kanta a sade, hakan ya sa matan suka kalli junna suka sakarwa junna murmushi harda Hajia wace wani irin farin ciki ya sake lulubeta ta mika hannu ta karra daukan wata takarda a gefenta ta kara a wace ke gabanta

wani irin turare mai sansanyan kanshi suka yi mata wanka da shi, sannan suka karbi bra da pant din da Mah ta miko masu suka bata, Rauda kuwa da ta karba sai da ta shige bayi ta saka dan kunyarsu ta fi komai damunta a yanzu..................

56

Bayan ta saka din ta labe a bayin har sai da aka fitar da ita tana ji tana ganni su suka shiryata sannan suka zaunar da ita a bakin gadon nan, daya daga cikinsu tana murmushi ta ce" Girma ne, daukaka ce, daraja ce daga Ubangiji kasantuwarki mata a wajen MALEEK, Allah ya karra maki lafiya da nisan kwana, ya sa muna da rabon gannin tsatson ku ke da MALEEK......."
Sai kawai ta ga iyayen matan nan sun kai zaune a wajen kawunnan su a kas
Chapter 97 · 0% Book details